Masu tambayar Wattpad user name d'ina ga shi nan
@Nazeefah381
Jikinta na 'bari ta ke kallonsa tana nuna masa d'akin da bakinta, kamar bai san komai ba ya ri'kota jikinsa yana fad'in "Lafiya?" A rud'en ta dinga gaya masa miciji miciji ne a bedroom. Ya gintse dariyar da take shirin tona asirinsa tare da ware ido ya ce "What? Miciji kuma? Yau mun shiga uku don micizan garinnnan ba su da mutunci tsaf suke hallaka mutum har lahira." Tuni ta sake 'kan'kameshi tamkar zata koma cikinsa. Ya zaunar da su kan kujera don ya ji 'kafafunsa na son gaza d'aukarsa saboda shaking da suka fara. Da gaske ta rud'e sosai a razane ta ke. "Please 'kalbeey ka fitar min da shi?" Da sauri ya dafe 'kirjinsa "Wa? Ni? Ta ina zan iya fita da shi Ai sai dai da safe a kira masu fita dashi, ni yanzu tsoro nama kar ya fito parlour d'innan, Cikin sauri ta mi'ke bai iske ta ko ina ba sai a bakin bedroom d'insa ya danne dariyarsa ya bi bayanta zuciyarsa fal farin ciki.A gefen gado ya tarar da ita a takure ta kalleshi har zata kwanta ta 'kudunduna sai kuma ta tuna ba tayi sallah ba da sauri ta mi'ke ta hau dube-dube.
Yana cute smilling alamar kinzo hannu ya ce "Me ki ke nema?" A 'kuntace ta ce "Ban yi sallah ba kuma ba kayan sallah ta anan." Yana so ya ce mata akwai kayan Shaheedah a d'akin tunda ba tazo ta kwasa ba bari ya d'auko mata Hijab d'in yana tsoron ba'kin kishinta. Ya ja ajiyar zuciya "Bari na lalla'ba na d'auko miki a ina suke?" "Suna nan saman resting chair"
Da sauri ya fice har da d'an tsallensa a bakin corridor a zuciyarsa ya ce "Yaro man kaza!"Yana dawowa ya ganta ta mi'ke tsaye wai ta ji motsi a toilet d'in, ya dudduba bai ga komai ba sannan ta yarda ta shiga shima don yana tsaye bakin 'kofar ta yi brush da alwala ta fito, har zata tayar ya ce ta jira shi shima bai yi sallahr ba.
Tare suka yi sallahr ya jasu nafila sannan kuma suka yi shafa'i da wutiri ya d'an dafa kanta ta ji yana kwararo addu'oi bud'e idonta tayi tana tuhumarsa addu'ar menene ya sakar mata murmushi ya ce "Ta neman zaman lafiya ai tunda aka kawo ki ba muyi ba ko?" Ta d'aga kanta "oya tashi kije ki kwanta." "Kai a ina zaka kwana na ga ma bedroom d'in naka ba kujera." Murmushi ya saki ya ce "Kada ki damu dani ni ina iya kwana a zaune ma banda ina tsoron micijin da sai Na koma parlour ma." Tausayinsa ta d'an ji ta ce "Ai kuma da sanyi ka dai kwanta daga gefen bed d'in ni kuma sai na kwanta a can side d'in." Yana murmushi ya ce shikkenan ma."
Har zata kwanta ya mi'ka mata fresh milk mai sanyi da ya riga ya had'ata da desire tablet, ba ta kawo komai a ranta ba ta kwankwad'e sannan ta zame ta kwanta.
Imran hankalinsa kwance ya shiga wankansa har da 'yar wa'karsa cikin tsananin farinciki ya tabbatar a irin halittar shatu mai saurin amsa kira da ko kiss aka yi mata sai idonta ya canja, da zarar maganin nan ya fara aiki da kanta zata kawo 'kafarta. Ya dad'e yana wanka da kayan wankansa masu matu'kar 'kamshi na companyn makari, ya fito d'aure da towel a jikinsa sai 'karami a hannunsa yana goge sumar kansa yana sane ya 'ki sako bathrobe so ya ke Shatu ta ganshi a haka ya sake cilla mata wani assignment d'in.
Shatu ta ware ido daga kwancen tana kallon Imran ashe dai da gaske ingarman namiji ta ke aure jikinsa a murje ya ke da alama yana shan training. Wata kunya ce ta kamata kasancewar bata ta'ba ganin namiji a haka, take kuma wasu irin abubuwa suka fara mintsilin jikinta da alama maganin ya fara aikinsa. Ta runtse ido tana kiran sunan Allah "Ya rabb kada ka bani kunya." Imran kuwa ya cigaba da shafa mai a gashinsa da cinyoyinsa sannan ya zira gajeran wando ya nufi gadon bayan ya rage hasken d'akin da sauri Shatu ta mi'ke tana kallonsa daga shi sai gajeran wandon da ko gwiwa baizo masa ba a fisge ta furta "A haka za ka kwanta ba ka jin kunya?" Ya dubi jikinsa menene? Ni dama can bana iya barci da riga damuna suke wai ma ba wannan ba naga kema rigar jikinki da ita da babu duk d'aya." Cikin tashin hankali Shatu ta juya a zuciyarta ta ce "Na shiga uku wallahi Imran mugu ne yana sane ya ke jefa ni a wannan halin." Ita kad'ai ta san mai ta gani ta fad'i hakan. Imran gani bata kallonsa murmushi ya saki sosai ya kwanta abinsa yana sake ware air condition d'in d'akin duk da sanyin da ake tsilalawa a waje. Shatu sassan jikinta ya sake d'aukan 'bari ta rutse hannunta a cinyoyinta dafatan Allah yasa ta samu sau'kin lamarin da take ji. Imran ya kwanta yana sakin ajiyar zuciya ya kunna wa'kar westlife a wayarsa kasancewar sa masoyin westlife d'in tun lokutan baya.
Wa'ko'kin ba abinda suke 'kara mata idan banda wutar soyayyarsa da wata irin sha'awa da sam bata san ta kai mizanin haka ba a fannin.
Murya a dashe kamar zata yi masa kuka ta ce "Please Ya Imran ka kashe ba fa kyau jin wa'ka da daddare." Ya juyo yana mata wani irin kallo "Nima ba na ji da daddaren yau ne dai nace bari na kunna tunda ga ni ga hayateey ta a cikin duvet d'aya sanyi ma na ke ji please ki amince mu samu body contact yau dai d'aya ko ma rage jin sanyin." Ta runtse idonta saboda yarda ya ke mata magana da wani salo bata jin ko bai fad'a ba ita da kanta ba zata kai kanta garesa ba, saboda ta samu sau'kin abinda ta ke ji. Matsawa yayi sosai jikinta su ka samu body contact wanda dukkaninsu sai da suka saki ajiyar zuciya a haka kuma labarin ya sauya salo.
Lamarin da yazo musu a wani irin yanayi kowa burinsa ya nunawa d'anuwansa yarda ya ke matu'kar 'kaunarsa, Shatu tuni ta manta da wani batun shekara guda ta mi'ka kai Imran ya yi yarda ya ke so da ita, ta sha tsananin azaba fiye da darenta na farko sosai zata iya cewa budurwa ta koma sabida azabar da ta sha, Yau Mommah ta sha kira kai har da su Innaji da Babaji Ikram da Akram kuwa an kira su yafi shurin masa'ki.
————-
Da Asuba da kyar ya bud'e idanunsa ya mi'ke bayan ya zameta a jikinsa da kyar, ya zuba mata ido tana barcinta peacefully beauty face d'inta ta sake fitowa, wani farinciki yake ji yana ratsa shi fiye da farincikin da yaji a first Night d'insu. Da gaske yana tsananin son Shatu Son da shi kansa ba zai iya misalta shi ba, ya sha zumarta da madarar 'kaunarta wanda Allah yayi mata baiwa da su tabbas su Shatu ne maza suke kiran su da suna matan baiwa. Don kuwa dai komai da komai ta had'a har fiye ma da tsammanin yarda ya zaceta. Rungumar da ya yi mata ne ya farkar da ita cikin tsananin ciwon jiki ta turo baki ta ce "Haka muka yi da kai me yasa ka yi breaking promise d'inmu?" Wata dariya ce ta kufce masa a fili ya ce "Shatu Danger! Da amincewarki fa aka yi komai.. in tuna miki abinda kika ce da shau'ki ya d'ebeki?" Bai yi auneba ya ganta a bakin toilet t shige ta gar'kame.
Wanka take a cikin bathtub amma murmushi ta ke saki ita kad'ai tana tunano da sunayen da ya dinga sumbatu yana kiranta da su amma shine shi zai tsokaneta don tace "'kalbeey please banda kishiya ba zan iya sharing d'inka da wata banza can ba." Ta runtse ido tana sake tuno wasu al'amura masu girma da suka waka na a tsakaninsu, murmushi ya su'buce mata tabbas ta yi dace da samun ingattacen namiji mai cikakkiyar lafiya wanda indai ya cigaba da abinda ya ke mata tabbas zai mulketa son ransa don sai abinda ya ke so zata aikata.
Akan Sallaya ta sameshi idanunta ya sauka akan kayan da ya ajiye mata da ya d'auko a bedroom tana cono baki ta ce "Wai baka ji tsoro ba don Allah ka sake shiga d'akinnan?" Yana murmushi ya d'aga mata kai "kuma micijin yana nan?" Ta sake jifansa da tambaya shima murmushin ya yi ya d'aga mata kai Shatu ta fara tunanin ko dai dama wayo ya yi mata amma kuwa In dai micijin wasa ne ta tabbatar da hakan, sai ta rama ita ma. Da sauri ta zura rigarta suka tada sallah ganin lokaci zai 'kure musu. Tare suka yi azkar bayan sun karanta matayyassar minal 'kur'an Shatu ta dubeshi "Ina kwana?" Janyota yayi jikinsa ya ce "Sai kace wani a 'kauye wannan ce gaisuwar da nake so every morning." Ya fad'a yana kaiwa bakinta sumba ta. Lumshe ido ta yi a zuciyarsa ya ce ka Shatu akwai kar'bar sa'ko hakan yana nuna ita d'in lafiyayyiyar mace ce.
Ta mi'ke tsaye bayan zame jikinta da tayi, shima mi'kewar yayi yana fad'in ina zaki? Murya a dake ta ce "Zan je na tabbatar da micijinnan na gaske ne ko na 'karya ne? Idan na tabbatar na 'karya ne kana sane ka sani na yi breaking promise d'ina ina tabbatar maka sai na rama." Dariyarsa ya guntse hakan Yasa Shatu fita a hanzarce don son ganewa idonta. Imran ya ri'ke kansa ya ce "Shatu Danger! Ko wannan karan kuma da me zata rama oho ni dai ba na kwashi ganima ba." Ya furta a fili yana bin ta a baya........
08033748387