36

167 4 0
                                    

Me Zan yi da ita?

36

Kiran da Alhaji Baba yayi masa ne yasa sh jiyowa, hakan yasa shi fasa shiga garden 'din. Alhaji Baba ya yafito shi da hannu alamar yazo. Hakan ya saka shi nufar kakannasa.

A parlourn sa ya zaunar dashi, yana dubansa zuciyarsa cike da begen jikannasa. "Ka shigo jiya bamu ha'du ba? Ko da yake ni na hana Hajiya taso ka, Na san baka samu isashsshen barci ba anyi tafiyar da ba shiri, ya iyalinna ka?"
"Suna lafiya" "Masha Allah" nan ya zaunar dashi suka karya, yana ta tambayarsa cigaban da ake samu a business 'dinsa.

Mommah da Hajiya Mama suka saki ajiyar zuciya a kusan tare, ganin Imran bai shiga ba. Mommah tace "Alhamdulillah, ke basirah maza kije kice ta koma sitroom da karatun nan." Basira ta mi'ke ta fita isar da sa'ko, ita kanta mamakin yarda taga Shatu da ciki take yi.

——————————

Cikin masifa Kawu Sa'idu ya kalli Hajja, sannan ya dubi Manga "Tunda ya sake ta ba mahalu'kin da ya isa yasa ya dawo da ita, ai ni tun farko ban san da wata manufa kika ha'dashi aure da zainabun ba da ba zan amince ba wallahi, kuma yafiya dole ki yafe masa matu'kar ba kina so nima na janye hannuna a kanki ba, ban ta'ba ganin shashanci da zubar da mutunci ba irin naki, amma an zo 'karshe tun da gashi iyayenta sun 'dauketa, to ina dalili yarinya da gatan ta da komai ku saka ta a gaba har ciwon zuciya na neman hallakata, magana ta ta 'karshe kenan tsakani na dake ki bar Manga da Iyalinsa su huta, kafin ubangiji ya nuna miki Ishara, kuma ya zama dole ki bi ni Abuja ki duba yarinyar nan ki kuma bawa iyayenta ha'kuri ke da marasa kunyar 'ya'yanki."
Hawaye ne ya 'balle mata jin yace sai taje Abuja ta basu ha'kuri, gaskiya abinda ba zata iya ba kenan, a dai sake wata mafitar. "Don Allah kawu ayi ha'kuri ba sai naje ba, na amince ba zan sake shiga hurumin gidan sa ba." A harzu'ke Kawu Sa'idu yace "Baki isa ba dole kije wallahi kuma 'kafa ta 'kafarki, dake da fitsararrun yaranki." Daga haka ya mi'ke ya fice.

Yana fita Anty Amarya ta sakawa Hajja kuka "Don girman Allah Hajja ki bawa Manga ha'kuri na koma 'daki na. Hajja hannu bibbiyu kawai ta zuba tagumi ta rasa ma mai yake mata da'di. Wai kamar ita ace zata je ta bada ha'kuri tayi 'kwafa a fili tace "Ai kuwa Dijah idona idonki Allah ya dawo dake lafiya, ke kuma Zainab ki sha kuruminki komawa 'dakinki kamar kin koma indai nice uwar da ta haifi Manga. Sai sannan hankalin Zainab ya kwanta, Hameedah kuwa ta cika ta tumbatsa jira kawai take ta fashe.

——————————
Kwanan Imran biyu yayi shirin komawa, Ammar Kuwa Dahda yace ya zauna ba sai yazo ba tunda yaga jikinnata da afuwa.

Ranar da zai tafin da sassafe ya shigo cikin gidan, direct kitchen ya nufa, dai-dai lokacin Shatu tana kitchen 'din Burger take 'ko'karin ha'dawa, don tana son ta birge Mommah. Basirah kuma na gefe tana hidimar ha'da Alkubus da miyar taushe. Ji suka yi kawai an turo 'kofar, da sauri Shatu ta juya ta kuma ja mayafi ta rufe fuskarta da shi. Tuni 'kamshin turarensa ya baje kitchen wanda hakan yasa bugun 'kirjin Shatu ya tsananta. Gaisuwar Basirah ya amsa yana bu'de fridge. Har ya juya zai fita sai kuma ya waigo yana Mallon Shatu ba tare da ya san wacece ba ya dai yi mamakin rashin gaisheshi da ba tayi ba. Ta'be baki yana mur'de murfin ruwan ya kai bakinsa, da sauri ya fice.

A parlour yayi wa su Mommah sallama ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Tana saurarar Hajiya Mama da take mi'ka masa takardu "Addu'oi ne na tsarin jiki ka dage da yinsu saboda rayuwar nan ta zama abin tsoro ba'a zama haka. Allah ya tsare ya kiyaye ka gaishe mana da iyalinnaka." A gaggauce ya amsa mata yana ficewa da sauri don gudun rasa flight.

——————

Tunda ya tafi gaba 'daya walwalar Shatu ta tafi gaba 'daya, tunaninsa ya sake bun'kasa a zuciyarta, a le'kensa da tayi tana hango tsananin kyau da ya 'kara alamar ba abinda yake damunsa sai zallar nutsuwa da kwanciyar hankali. 'Kamshinsa yana nan ya kama gidan ra'dam tamkar lokacin ya bar gidan. Ita kanta ta amince Soyayyar Imran a jininta yake, idan ban da haka ya za'a yi ta kasa manta shi duk da butulcin da yayi mata, amma ina madadin raguwar lamarin kullum sabunta abin yake musamman yau da taji turarensa gaba 'daya ta sake tunowa da first Night 'dinsu, duk da soyayyar tasa bata jin zata sake komawa gidansa ko da ya bu'kaci hakan, gwara ta tsira da mutuncinta bakin da ya furta 'ki baya ta'ba dawowa ya furta so.

———
Kashegarin ranar su Hajja da Kawu Sa'idu suka zo, Hajiya Mama tayi musu tarba ta mutunci da girmamawa, fuskarta fal da fara'a tasa aka jere musu abinci iri-iri, amma haka suka dubi abincin a wula'kance ba tare da sun ci ba, duk da kajin da suke ta zaginsu. Hajiya Mama tana fita Kawu Sa'idu yasa musu fa'dan da dole suka 'debi abincin suka fara ci, sai dai suna ta jan addu'oi a zuciyarsu wai kar Asiri ya kama su. Kawu Sa'idu yace "Aikin banza ai shi mai yin abu shi yake tunanin wani ma irin abinsa yake. Ku dai daga ganin gidannan kun san sun fi 'karfin su tsaya yi muku Asiri shashashai kawai da babu Allah a ranku, wani yayi min abin rashin kyautawa a gidannan yaga yarda zan yaga mutuncinsa, kun samu mutane masu mutunci da karamci ma wallahi idan banda haka da wasu ne ya za'a yi su kalleku da ko ruwan sha balle su ha'da muku wannan daular." Tsit suka yi baka jin sautin komai sai na cokula sai kuma gashi sun cinye abinci tas ragowar shinkafa kawai suka bari. Kawu Sa'idu yace "Aikin banza kuna so kuna kaiwa kasuwa."

Bayan gama cin abincinnasu Alhaji Baba da 'kannensa biyu suka shigo, sannan Hajiya Mama da Mommah suka shigo. Har 'kasa kuma Mommah ta dur'kusa ta gaida Hajja ba tare da ko canjin fuska ba balle fitsara. Jikin Hajja yayi sanyi a karo na farko ta ji kunyar Mommah ita kanta ta shaida Mommah mai ha'kuri ce, don koda wasa bata ta'ba nuna mata ba'kin hali ba, kullum a cikin yi musu uzuri take. Ba yabo ba fallasa ta shiga amsa gaisuwar tare da tambayarta jikinta. Fa'da sosai Kawu Sa'idu yayi, ya kuma bada ha'kuri tare da cewa insha Allah anyi na farko an yi na 'karshe." Ya saka su Hameedah ma da 'yanuwanta suka bada ha'kuri, haka dole suka bayar ba da son ransu ba.
Sannan ya koma da yi musu nasiha sai dai gaba 'daya ba jin nasihar suke ba, musamman Hameedah da take gani kamar an zubar mata da ajinta. Alhaji Baba yace "Ni kuma tunda ka gama ina da magana, kayi ha'kuri yaronnan ya mayar da matarsa Zainab alfarma na nema. Kawu Sa'idu yace "Sun ci albarkacinka dattijon arziki na amince masa ya mayar da ita, amma a bisa shara'di ko kallon banza ban yarda ta sake jifan Dijah dashiba balle zagi, don iya shege saboda ta Samu 'daurin gindin uwar miji." Alhaji Baba yace "Godiya nake, Allah ya basu zaman lafiya ya ka'de duk fitina." Ameen suka amsa wasu a fili wasu a zuci. Taro ya watse, wasu sun kar'bi nasiha irinsu Fanna da Falmata wasu kuwa anan suka zubar tare da 'daura 'damarar sabon shiri.

A ranar suka juya maiduguri a jirgi. Su Mommah kuwa kashe gari ta bi Dahda suka koma. Wannan karan ma da kuka Shatu ta rabu da Mommah.

——————-
Bayan Wata biyu, lokacin cikin Shatu ya isa haihuwa, a asibiti kuma suka bada shawarar ayi mata c.s duk da dai zata iya haihuwa amma suna gudun faruwar matsala, saboda cikin yayi girma sosai ita kuma ga 'kan'kantar shekaru.

Ana saura kwana biyu ayi mata aiki Ammar ya samu labari don haka yayi shirin tahowa daga Qatar yafi so ayi a gabansa, ji yake tamkar Shatu shi zata haifawa babyn. Siyayyar da ya jibgo kuwa har da ta banza, kaya ne akwatina kusan biyar duka unisex na haihuwar.

Cikin murna Shatu ta tare shi, da abinci kala-kala tana girmama Ammar sosai tana ganin mutuncinsa musamman ganin yarda yake 'dawainiya da ita da aljihunsa da jikinsa.

A ranar ma Mommah ta iso tare da Basirah, bayan tayi wa Dahda 'karyar Shatu ce ba lafiya. Ammar ne ya saka hannu a madadin uban 'da aka shiga da Shatu theatre....
Shatu sai muce a fito lafiya..

Kuyi hakuri ba yawa yau ciwon kai nake, wallahi.

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now