37

405 5 0
                                    

Me Zanyi da ita?

37

Nimcyluv ubangiji ya baki lafiya, Allah yasa kaffara. Ku saka marubuciyar Zain abeed a addu'a da bakunanku masu albarka.

Alhamdulillah nagode sosai da wa'danda suka kira ni ko text messages domin yi min fatan samun lafiya, nagode 'kwarai da ba zarku nake taka rawa, Alhamdulillah ala kulli halin, wa astagfirullah min kulli zanbin.


Tsawon lokaci suka 'dauka a cikin theatre Room 'din. Kafin lokacin fitowar tasu su Mommah addu'oi kawai suke zubawa domin samun nasara.

Da sauri wata nurse ta iso wajensu, idanunta cikin na Hajiya Mama tace "Alhamdulillah, an yi aiki successfully, an ciro Baby Boy yanzu za'a fito da ita." Gaba 'daya wajen suka ha'da bakin fa'din "Masha Allah." Hajiya Mama ta bu'de jakarta ta ciro ku'din da bata san adadinsu ba ta dam'kawa matar. Ita kuma ta juya da sauri ta koma dama tukwuicin take yiwa.

Juyawarta kenan, suka ga ta dawo da sauri tace "Hajjaju ashe biyu ne, tukwuicina yafi haka duk da yanzu kishiya aka zanka'do miki." Wani tarin farin ciki ne ya wanzu a zuciyarsu, wannan karan Ammar ne ya zura hannu a aljihunsa ya ciro dalolin Amurka guda uka ya dam'kawa matar. Mommah kuwa burinta taga Shatu domin ta gama biyanta a duniyar nan ta khali'ku.

Bayan mintuna Goma aka fito da yaran, Tubarakallah shine abinda su Mommah suke cewa kawai yayin da su kayi arba da zanka'da-zanka'dan yaran tamkar 'diyoyin larabawa. Hannu bibbiyu Mommah ta saka ta rungumesu tama manta da wata kunya balle ta tuna Hajiya Mama a wajen, zallar farin ciki ya sata shatatar hawaye cikin wani rin shau'ki take bawa yaran sumbata a kumatukan su, tana jin tsananin 'kaunarsu na ratsa dukka sassan jikinta, fiye da lokacin da ta haifi Imran da Ammar, tabbas ta yarda da maganar malam bahaushe da yace Abin cikin 'kwai yafi 'kwan da'di.

Hajiya Mama kuwa sai kallon Mommah take fuskarta cike da murmushi a zuciyarta tace "Dijah dole ne kiyi farinciki ni kaina da aka haifi Imran nayi fin haka balle ke da aka yiwa biyu lokaci 'daya, kuma tuwo na maina don kuwa Shatu 'yar Mommah ce halak malak.

Dai-dai lokacin aka fito da Shatu a wheel bed idanunta a lumshe hawaye yana zirara ta cikin su, hannu ta mi'kawa Mommah, da sauri kuwa Mommah ta mi'kawa Ammar Babies 'din ta nufi 'yarta. Da ita aka tura ta har zuwa Amenity1 'dakin da zata huta.

Ammar farin ciki ne ya baibaye zuciyarsa, yana ayyana ko yanzu kallon Shatu take kamar ta zama tasa domin dai kuwa yau ta gama idda. Babu shamakin da zai katange shi da furta mata zahirin abinda yake zuciyarsa, da zarar sun isa gida an sallamesu, tunda Mommah ce tayi masa al'kawarin ko ranar suna za'a iya yi musu aure.

Idanunta a lumshe alamar barci yana son 'daukarta, Mommah ta haska mata fuskokin yaran tana cewa "Shatu na bu'de idonki kiga 'kurrati ainun. Shatu ta ware idonta tar tana kallonsu tare da girmama hikimar ubangiji ta yarda yaron yayi kama da Imran kwabo da Kwabo, ita kuma jaririyar tayi kama da ita sak kamar tayi kaki ta zubar. Cikin zuciyarta tace tabbas 'kudirar ubangiji girma gareta ubangiji yayi muku albarka, ko a tunani ban ta'ba tunanin haihuwar biyu ba. Sai ta lumshe ido sai kuwa ga hawaye ya sake zubo mata na tsantsar farinciki da godiya da ni'imar Azza wa Jallah.

Bayan sun nutsu Hajiya Mama ta kalli Mommah "Ai sai a fara sanar da dangi haihuwar." Mommah ta girgiza kai "Wallahi Hajiya bana son kowa ya san da haihuwar nan..." "Ai kuwa gan-gan kenan zancen banza zancen wofi a na wani dalilin zaki ce ba za'a sanar dasu ba, shikkenan sai a 'boye ciki haihuwar ma a 'boye, sai kace an haifi shegu to ba dani za'a yi wannan iya shegen ba. Ki 'dau waya ki kira mijinki ki fa'da masa, sannan a gayawa duk wanda ya dace." Cikin takaici Mommah ta shiga bin umarni Hajiya Mama don taga ta hau da yawa.

Dahda ta fara kira ta sanar dashi, kasa'ke yayi da wayar ba tare da ya iya furta komai ba. Ransa ya kai 'kololuwar 'baci. Jin yayi shiru yasa Mommah fa'din hello!hello! Mamaki ya kamata jin ya saki ajiyar zuciya alamar yana jinta.

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now