35

189 5 0
                                    

Me Zanyi Da ita?

35

Cikin 'bacin rai ta kamo hannunsa, idanunta cikin nasa kafin ta furta "Haba Habibi yanzu Nigeria zaka tafi? Ka bari na samu sau'ki mana sai mu tafi tare, wai shin mai ma ake yi a Nigerian?" Zame hannunsa yayi kafin yace "Zuwa ta Nigeria ba shi zai hanaki samun lafiya ba, Mommah ce ba lafiya kuma Dahda yayi min umarnin lallai na tafi. Ko da ma baiyi min ba ya zama tilas naje na ga jikin Mommah." Har ya kai 'kofa ya jiyo yace "zan sanar da grace tazo ta zauna dake."  Yana fita ta saki ajiyar zuciya, 'kirjinta yana matu'kar suya da saboda tsananin 'bacin rai. Da sauri ta lalibi numberr Anty Amarya ta shiga danna mata kira ba ji ba gani.

'Daga wayar ke da wuya, Shaheeeda ta sa mata kuka "Ki taimakeni Anty, wallahi kamar komai ya warware ina hango tsanata a idanun Imran, duk da bai furta ba ina jin tsoro Anty. Yanzu ma fa Nigeria zai taho wai Mommah ba lafiya." Anty ya ri'ke kanta, ga shi time 'din tana cikin dangin su, ana ta sha'anin biki ba damar tayi wani abin. "Kiyi ha'kuri, zan san abin yi, ba dai Nigeria zai zo ba Allah ya kawo shi lafiya." Shaheedah ta kashe wayar ranta a 'bace don ba haka Ta so ta ji ba, so tayi Antyn ta san yarda aka yi ta hanashi zuwa Nigerian gaba 'daya.

—————-
Bayan fitar Dahda daga hospital 'din direct Family House 'dinsu ya tafi ransa a 'bace matu'ka, dama rashin mai zama da Mommah ya hana shi zuwa yayi musu maganar.

Tun daga corridor 'din sashen Hajiya yake jiyo ihunsu da shewarsu, yana jiyo Anty Amarya tana cewa "Ai cewa yayi bata da lafiya, shi yasa bai zo ba tun jiya."
Hameedah tayi zumbur tace "Shegiya ina ma mutuwa tayi muka huta da gayyar tsiya." Hajja tace "Wallahi kuwa, wannan masifa har ina? Ni na rasa yarda zanyi na datse wannan auren, amma kam na tsani yarinyar nan." Zuciyarsa ce ta sake dugunzuma kamar mai? A zafafe ya danna 'kofar 'dakin da 'karfin gaske,da yasa su saurin 'dagowa suna kallonsa. Gaba 'daya suka firgita har Hajja, musamman ganin yarda idanunsa suka ka'da su kayi jazur, ya kalli Zainab sai kuma ya mayar da kallonsa kan 'yan uwansa mata, "Duk abinda kuke fa'da ina jinku, a yau kuma na sake tabbatar da al'amarin tsanarku da Dijah mai girma ne, ba tare da sanin wani laifin Dijah tayi muku ba, laifinta 'daya da ta aureni take tattalina da nuna min soyayya, ku kuma abinda ba kwa so kenan kun fi son ku ganni da macen da zata dinga 'daga min hankali, don haka ayau ba sai gobe ba zan tabbatar muku mahaifiyata kawai nake shakka, kuma ita ka'daice wacce ba zan iya rabuwa da ita ba, kun saka mata a gaba gata can a gadon asibiti zuciya ta cunkushe da 'bacin rai, ku ko kunyar yaranta ba kwa ji? To daga yau na yanke ala'kata daku matu'kar ba zaku zauna da matata 'kalau ba, ke kuma zainab kije na sakeki saki 'daya." Gaba 'daya wajen ihu aka saka da salati, Zainab kuwa cikin tashin hankali take kallon Hajja tace." Hajja please kice wani abu mana, kina ji yace ya sake ni." Cikin takaici Hajja tace "Ince mai Zainab? Ina da mutunci ne a idonsa? Kina jin irin maganganun da yake fa'da a gaba na saboda baya gani na da mutunci, zuciyar Manga gaba 'daya an canja ta, ni kuma yarda ya rabu da 'yan uwansa akan Dijah ya kuma sake ki, ina tabbatar masa nima na zare hannuna daga lamarinsa, yaje dangin Dijah su zame masa uwa da uba. Na sallama musu shi wallahi." Hawaye ne taf a Idonta, don lamarin Manga ya kere tunaninta. Cikin wata irin karayar zuciya Manga ya zube idanunsa cikin na Hajja ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta ihu, ba tare da yayi magana ba ya juya ya fice, da sauri tamkar tashin iska.


———————
A ranar aka sallami Mommah, cikin hukuncin ubangiji jikinnata da sau'ki sosai. Fargabar ta 'daya komawa Abuja da aka ce zata yi bata so ta koma saboda bata son a san Shatunta na da juna biyu.

A ranar kuwa suka bi Flight zuwa Abuja, bayan Hajja ta sanar da ita ba matsala, suna da c.c.t.v camera yanzu a gidan, suna ganin mai shiga da fita a gidan duk wanda yazo zata saka Shatun Ta shige bedroom. Hakanne ya kwantar da hankalin Mommah, ita ma kam wannan ciwon ya razana ta kuma yanzu tana bu'katar a kar'bar mata ha'kkinta bata son ta rasa rayuwarta a garin kawaicin ta na banza.


Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now