52

234 8 0
                                    

Tsam ta mi'ke ta shige toilet, wanka ta yi sosai mai sunan wanka, sannan ta hau wanke duk wani lungu da sa'ko na ha'koranta, ta sake binsu ta kuskure da mouth wash.

Tana fitowa ta bud'e jakar kayan da Mommah ta had'o mata, murmushi ta saki ganin duk masu kyau ne, tana bud'esu kuwa zallar 'kamshin turaruka ne ya bad'e hancinta, take ta lumshe idonta tana sake jaddada 'kaunar Mommah a zuciyarta tabbas Mommah Uwace abar alfaharin 'ya'ya, kunta ta kamata kamar tana gaban Mommahn na abinda ta dinga aikatawa ashe Mommahn duk gwada su take.

Lace ta ciro peach colour mai tsananin kyau ga taushi an yi mata d'inkin doguwar riga da tayi mugun fito da duk wata sura ta jikinta, kasancewar lace d'in mai matu'kar tsada na Hkg company ne yasa bata wani ji nauyinsa a jikinta ba. ta taje tulin sumar kanta kafin ta kawa 'karamin band ta kalmasa gashin a ciki sai yayi mata kamar gammo tabbas Shatu akwai suma.

A cikin kayan dai ta gano wasu chewingum masu 'kamshin tsiya hakan yasa ta wurga a bakinta. Yau dai su Shatu har lip stick a kasa akan d'an mitsilin le'ben sai gashi ya fito ras dashi ya bada shape d'in heart, ba ta ja jagira ban sai dai ta taje gashin giran, ta kuma saka masacara a Zara-zaran gashin idonta. Ni kaina sai da
Na ware ido Na sake kallonta tamkar ba Shatu ba musamman da ta kalmasa d'ankwalinta ta yi d'aurin Zahra buhari ga gold ya ji a wuyanta da hannuta tsaf ta fito a zaratan Mata tamkar ba Shatun Mommah ba.

Zamanta ta yi a gefen gado da
Mayafinta a side jira take ta ji motsin shigowarsu ta yafe mayafin don tayi al'kawarin sai an mata siyan baki kamar yarda ake yiwa kowace amarya.

Tana jin motsin kuwa taja mayafin ta rufe kanta ruf, tana cigaba da danna waya, tuni d'akin ya baje da wani 'kamshin zallar turarikan Wuta da humra da aka had'o mata. Na Hajja A'i gidan 'kamshi duk mai son turarenta ya duba page 40 akwai numberrta ta iya turare sosai tabbas ba 'karya musamman na jiki da dorot.

Har wani part Na daban ya kai Ammar bayan sun dawo bedroom ne da parlour yana murmushi ya dubi Ammar d'in "Ka sha zamanka anan kada ka fito sai na zo da kaina na fito da Kai." Ammar ya zaro ido cikin mamakin furucin Imran d'in sai kuma ya yi murmushi ya ce "Allah sarki ni na baro tawa amaryar na zo inda za'a kulleni ace kada na fito ai shikkenan, da zan samu jirgi ma yau zan koma don hankalina yana kan Mubeenaty." Imran ya hau sosa 'keya kafin cikin dariya ya ce "Kai yaro ne bana son kaga abinda hankalinka ba zai iya d'auka ba ko na jefaka a wani hali gashi madam d'in taka bata kusa." Ammar ya sake ware ido ya ce "Lallai Bros nine ma yaro da Aurena fa?" "Ka san meye auren? Ai da ka tare da ita ina tabbatar maka ba zaka iya tahowa ka barta da tare zaku ta ho honey moon amma ka taho ka barta acan. Ka yi zamanka kawai ka saka a kawo maka ita ku gurji amarci wallahi zan kai ku guraren sha'katawa da yawa." Ammar ya grigiza kai "Ma dawo nan gaba, idan Mommah zata zo, saboda akwai tarin ayyuka da Na bari a Qatar." Imran ya fice yana cewa "Kai ka cika ni da surutu Na bar madam a can."

Ya dinga 'ko'karin kiran Mommah, amma bata d'agawa tun d'azu ya ke nemanta ya zabga mata uban godiya. Duk da dai ya samu Dahda amma Mommah fa? Da ita ya kamata yayi sharing duk happiness d'in nan don haka ya 'kudirce cewa 'karshen wata suma zasu tafi ya sake jaddada gidiyarsa garesu sannan shi da Shatu da su Akram su je wajen dangin Baban Shatun.

Wannan karan ya sameta, da wani irin farin ciki da karsashi ya ce My heart. Sunane da ya ke Kiranta dashi rabonta da ta ji sunan a bakinsa har ta mance. Murmushi ta saki tace "Burinka ya cika ko? Yanzun ka daina fushi Dani? Kuma zaka yi min al'kawarin Imran d'ina Na da ya dawo mai jin maganata."
Ji ya yi kawai hawaye ya fara zubo masa. Bana komai ba sai Na zallar farinciki da takaicin ba'kantawa Mommah da ya dinga yi, ba tare da ya san dalili ba, cikin muryar kuka ya ce "Please My heart ki yafe min, na yi nadama." Ya fad'a yana danne gefen lips d'insa tamkar ya ciresu sosai yake jin zafin zuciya. Mommah ajiyar zuciya ta saki ta ce "Na yafe maka Imran dama can ban ri'ke ka da komai ba Na san ba yin kanka bane ina Shatu sun sauka Lafiya? Ka yi 'kokari ka had'a mata layin nan 'kasar don a dinga samunta a waya, ka kuma bi da ita a hankali she is still young." Daga haka ya ji ta katse wayar. Murmushi ya saki a zuciyarsa ya ce "Haba Mommah ai ba wannan maganar don tsahon lokacin da kuka tsaya kuna jan raina yau sai na fanshe a jikin Shatu, yarinyar da tunda na kusanceta ban sake barci mai dad'i ba yau dole duk mafarkan da  nakeyi su tabbatar zahiran Na d'and'anesu a zahiri.

Wanka ya shiga, tsaf ya fito yana zabga 'kamshin sabulan wanka na makari, Wando ya saka three Quater black da white armless riga ya gyara kwantacciyar sumarsa da sajen da yake gefen fuskarsa ba 'karamin kyau ya yi ba. sannan ya d'au ledojin take away d'in da yayi musu.

Kitchen ya shiga ya yi warming abincin ya kuma dafa madara fresh mai d'umi ya zuba a flask, ya yayyanka mata fruits duk 'ko'kari yake Na son faranta mata.

A dinning ya jere komai sannan yasa kai ya shiga bedroom d'in da take. Yana bud'e 'kofa daddad'an 'kamshin da ya cakud'e da sanyin a.c ya dakar masa fuska take wata kasala ta lullu'beshi.

Ya kai dubansa a saman bed d'in inda ta takure kanta murmushi ya saki yana taku zuwa wajenta. A gefe ya zauna ya ra'ba jikinsa da nata ya yi mata kyakykywar runguma ta gefenta yana sakin ajiyar zuciya ya yi nufin unveiling d'inta da sauri ta ri'ke hannunsa, da ya saka shi lumshe ido sabida taushin hannunsa, murya a sar'ke ta ce "Siyan Baki?" Imran ya shige jikinta sosai yana shinshinar 'kamshinta ya ce "Akwai siyan bakin da ya fice wannan ni cinye bakin ma zan yi, please Shatu ki bud'e min fuskarki I wanna kiss your lips." Cikin muryar 'bacin rai kamar gaske ta ce "Bakin da yake warin? Har ka daina 'kyamarsa?" Kunya ce gaba d'aya ta dabaibayeshi a kunne ya rad'a mata ban da tuna da ta shi muje ki ci abinci tunda rowar fuskar za kiyi min zan nemo abin siyan bakin." Ya fad'a cikin wata voice da ta toni asirin halin da ya ke ciki. Tana mi'kewa tsaye ta ji ya kai mata wata kyakykyawar runguma ya kuma cire mayafin da sauri ta bud'e ido tana kallonsa ranta a 'bace ta ce "Wallahi sai ka ba ni kud'in siyan baki na, kuma million biyar na ke so cif, sannan kada ka saka ran nan kusa zan amince ka kusanceni sai nan da shekara guda, sai na yarda da gaske ba sha'awa ta ka ke ba soyayyar zahiri ka ke min, sai ka kuma sanar da
Abokanka yarda ka ke tsananin so na domin sai an yi Walima ko anan ko a Nigeria ka fad'awa mutane yarda ka ke tsananin so na, sai ka yi min lefe sannan zan amince ka kusanceni shima after one year.

Da sauri Imran ya dinga jifanta da wani irin kallo ganin da gaske ta ke maganar da take, surarta kawai ya ke kallo da le'benta da ya ke fisgar hankalinsa. Ya ja gwauron ajiyar zuciya kafin cikin wata irin murya ya ce "One year fa kika ce?" Cikin sake tabbatar masa da furuncinta ta ce "Tabbas!"

Ayi manage da wannan zaman makoki muke don ma kada kujini shiru ne nagode

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now