Da sauri Hajja tayi 'ko'karin ri'keta, sai dai ina 'kwacewa ta yi kamar mai iskokai a kanta tayear fice a guje, duk wanda ya ganta a lokacin zai iya zargin hauka take sabon Kamu.
A wani parlour kuwa Allah ya taimaketa ta riski Shuwa ai kuwa direct ta sha'kar mata wuya. Shuwa da dama ta san za'a rina sam bata firgita ba, illa 'ko'karin Ta 'kwaci kanta cikin matu'kar jarumta ta fisge wuyanta sannan ta zabga mata mari, hakan ya tunzira Hameedah ta samu wani sanda ta rafka mata, Shuwa ta zube 'kasa da sauri Zainab ta yi kanta tana fad'in "Ke baki da hankaline? Kashe ta za Kiyi?" Wani kallon banza Hameedah ta watsa mata "Ri'kakkiyar munafuka ai na san duk wani 'kulli dake aka 'kulla shi, yarda kuka yiwa Dijah shine nima za kuyi min ku yaudare mijina kamar yarda kuka yaudari Yaya Manga to wallahi ni na fi 'karfinku daga ku har tarkacen asirinku, Hajja yau zan sanar da ke komai wallahi Zainab asiri ta ke makawa Yaya Manga da kebin kan ki shine dalilin da yasa idon ki ya rufe har kika aura mata Yaya Manga, munafuka kuma yanzu ma sun sake 'kulla wata tsiyar don kuwa farra'ku suka shirya yi miki da d'anki Allah ya toni asirinsu shi da Kansa Yaya Mangan ya ganta tana ha'ka rami zata birne, kuma ita Shuwan ita ta gaya min da bakinta, har haurawa muka so yi da ita da taje gidana akan me yasa za suyi miki haka suka ce so suke da zarar sun mallaki Manga sai su karya asirin lokacin burinsu ya cika an fitar da Dijah daga gidan Manga...." gaba d'aya parlourn salati aka saka cikin mamakin wannan abin aljabi, da takaici Hajja taa dubi Zainab ta ce "Yanzu Zainab abinda za kiyi min kenan duk da 'kaunar da nabin nuna miki amma ki rasa sakayyar da zakiyi min sai ki yi min farra'ku da d'ana?" Kuka sosai Hajja ta saka yayin da Zainab ta fara ranges-rantsen 'karya. Nan fa kallo ya koma sama 'yan biki suka had'u a wajen aka suka su Zainab a gaba ana jifan su da kalamai marasa dad'in ji.
Hargitsewar da gurin yayi nea dangin Mommah na neman tada wata fitinar don kuwa rantsewa suka yi sai sun illata su Zainab, hakan yasa Mommah kiran su Dahda ba shiri don gwara maza su shiga cikin lamarin tunda ana neman illata su.
Da kyar su Dahda, Kawu Sa'idu da Alhaji Baba suka samu shiga gurin, duk da korar da aka dinga yiwa mutane amma kowa fir ya'ki fita, kuma ana mi'kewa za'a fita dasu suke saka musu duka hakan yasa dole aka zauna anan ayi shari'ar.
Kawu Sa'idu ne ya kalli Hameedah yace "Ina jinki me ya Faru?" Nan cikin kuka ta shiga bashi labari turyan-turyan.
Tana gamawa Kawu Sa'idu ya saki Murmushi ya ce "Hukumullahi la ajabun ashe har anzo wajen madallah da sarkin sarakuna mai sakayya yanzu tun a duniya ba sai Anje 'kiyama ba. yanzu ke me kike so ayi? Abinda fa kuka yiwa Dijah ne ya juya ya dawo kanki, ko kunya ba kiji ba da bakin ki kike cewa an had'u da ke an yiwa jininki asiri shima Imrana ashe asiri kuka yi masa to ba jan magana nake nema ba ta faru ta 'kare sai kije ki rungumi ha'kuri kamar yarda Dijah ta ha'kura Allah ya ba ku zaman lafiya ke da kishiyarki, ita Shuwa ai gaba ta kaita shashashai kawai duk 'kawar da ba zata d'ora ka a turbar arziki ba ai kaa gujeta, Allah ya kyauta yanzu ai kun ga ishara da ku da duk mai hali irin naku."
Har zai mi'ke ya fita don shi ko ganinsu baya son yi. Dahda ya gyara zama ya ce "Kawu ina da magana, dama ina taso Allah ya kawo mu rana irin wannan, ranar da zasu toni asirin junansu da bakinsu, tuni na san da wannan zancen da kuma idona na kama Zainab zata birne laya cikin dare wanda sunana da na Hajja yake zane a jikin layar, kamar yarda shima Imran ya kamasu da matarsa da tulin kayan tsubbace-tsubbace a gabansu, shima ya nuna musu tamkar bai gane ba, sai dai dukkaninmu mun yanke hukunci d'aya domin kamar yarda Imrana ya saki matarsa hakanan nima na saki Zainab..." cece kuce ya tashi a wajen bayan Manga ya zaro waya ya kunna vedio ya yi connecting da T.v a parlourn sai ga kuwa Zainab tana birne birnenta. Gaba d'aya salati da salallami mutane suke a wajen. Cikin tashin hankali Hajja ta ke sake duban tv d'in da gasken dai Zainab ce ai kuwa sai ga Hajja tana kuka riris tana fad'in "Allah ya isa Zainab na bar ki da mai hudowar rana da fad'uwarta shine zai mana sakayya."
Su Zainab dai ba bakin magana gaba d'aya kunyar kanta ta isheta. Shaheedah kuwa kuka ta ke
Na fitar hankali tabbas ta san rayuwarta ta tawaya tunda ta rasa Imran, ta yi dana sanin bin zugar mahaifiyarta, ta tuna yarda suka cusa masa sonta ta kar'bi da yaji da asiri da rubuce-rubuce, gashi yau rana d'aya ubangiji ya toni asirinsu. Jiki a salu'be suka mi'ke aka basu hanya Hajja fad'i ta ke "Gayyar tsiya ku basu hanya su wuce zan kuma da uwarki in ji ko ita ta saka ki a turbar halaka."
Ta kuma cigaba da kukanta tana kallon jama'ar da ke wajen fad'i ta ke "ku kuma iyalen saka ido ai sai ayi gaba ko? An samu na kai rahoto idan banda haka abu na gida me ya kawo idonku wajen? Ni bana son munafunci."Sum-Sum kuwa suka fice daga wajen, Hajja ta kalli su Mommah kafin ta ce "Dijah don girman zatin ubangiji ki yi ha'kuri ki yafe min, duk da na san girman laifina a gareki wallahi kullum na yi nufin fara 'kaunarki da yabon kyawawan d'abiunki sai na ji zuciyata ta gaza hakan na tabbata ba haka suka bar ni ba, ni ba kiyi min komai ba wallahi kullum a cikin kyautata min kike?" Alhaji Baba ya ce "Alhamdulillah, hakan da kika yi shine ya dace ke kuma Dijah ki yi ha'kuri ki yafe mata ko bakomai ki saka ta a mizanin uwa don uwar miji uwace matar da ta haifa maka miji ai ba abar wula'kantawa bace macece da ya kamata ka bata daraja ta hudu bayan uwa uba miji ni ana wa hangen sai uwar sa tunda ta yi miki komai da ta haifa miki d'an har kike tin'kaho da shi a matsayin mijin ki. Ke kuma uwar miji duk matar da ta auri d'anki ta gama yi miki komai domin ta so d'anki ta na kuma kula dashi bai kamata ta zama abar tozartawa ko abar gaba da kishi a wajenki ba, kowa ya ri'ke mutuncinsa ya kuma tsaya a matsayarsa ubangiji yasa 'karshen lamarin kenan, ya sake dawwamar da zaman lafiya a tsakaninmu."
Kawu Sa'idu ya ce "Ka gama magana Alhaji Allah ya sa mu dace sai batun Imrana ina ga tunda komai ya bayyana ai sai ayi ha'kuri a mayar masa da matarsa."
Da sauri Dahda ya ce "Ayi min afuwa Kawu, tunda dai Imran ya ha'kura ya tafi akan zai auri 'yar gidan aminina har naje musu da maganar yarinyar ta amince musamman da taga hotonsa, to bai kamata a canja d'in ba a barshi a hakan ubangiji yasa hakan ya zame musu alheri."
Parlourn ya yi tsit saboda duk ba haka suka so ba musamman Hajja da take ganin duk laifinta ne ta share gumin fuskarta ta ce "Manga kayi ha'kuri a mayarwa da Imrana matarsa." Dahda ya girgiza kai kafin ya ce "Hajja don Allah a bar maganar kada a mayar da hannun agogo baya, ubangiji yasa hakan shine ya fi musu alheri ba mu san abinda Allah ya 'boye ba." Kan dole suka amince da abinda Mangan ya ce. Ita kuwa Hameedah a kanta komai ya 'kare domin dai Kawu Sa'idu ya ce ba ruwansa ba zai yiwa mijinta magana ba dole ta amince ta zauna da Shuwa a matsayin kishiya, hakan ne ya tashi hankalinta ta shiga wani irin kuka na tashin hankali 'karshe Mommah ce ta shiga lallashinta, ba kunya kuwa Hameedah ta kwanta lamo a cinyar Dijah tana saurarar nasihar da ta ke mata.
————————————
Duk wasu shagulgula da za'a gudanar a bikin sun tafi yarda ya kamata, amare sun sha bidiri don kuwa abin su a nutse su ke yinsa cikin kwanciyar hankali ba harigidon hauka ba, ba wani abu da suka yishi a cakud'e da maza illa dinner itama 'bangaren maza daban na mata daban, kuma babu rawa balle ace an had'u an cakud'a maza da mata sai dai muce Allah ya sanya alheri.
Kashegari ne d'aurin aure don haka gaba d'aya gidan bikin a safiyar ranar a cakud'e yake,
Duk inda ka juya mutanene dam'kam, duk da ba a gidan za'a d'aura auren ba a babban masallacin Abuja za'a d'aura.Amare sun sha ado cikin kayan Alfarma, gaba d'ayansu black lace suka saka da adon golden a jiki, hakan yasa suka yi amfani da mayafi da sar'ka duka golden, zo kaga yarda haskensu da kyansu ya 'kara fitowa musamman Shatu da idan kakin ganta ba zaka ce itace ta dire Ikram da Akram ba. sai dai sam ba ta da walwala, tun safe 'kirjinta yake dukan uku-uku ga wata fad'uwar gaba da ta riskarta akai-akai ta tabbatar yau zata zama matar Ammar, da ba ta yi masa ko d'igon so illa son 'yan uwan taka.
Angwayen na shigowa ta ji an rangad'a gud'a "Masha Allah Nahna amaryar Salees, Hafsa ta angwance da angonta Saleem Dukan da 'kirjinta ya cigaba lokacin da ta jithe ance "Ayshatu ta angwance da mijinta......."
Tashin hankalin da naga taa shiga ne yasa wayata ta su'bale ta fad'i.
Saduwar alheri