4

197 9 0
                                    

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-4
ELEGANT ONLINE WRITERS****

Dada ta zuba mata idanun tsofaffinta , cikin gatse tace "inji ubanki muji da ya sace mana'ya ya gudu da ita" shatu ta girgiza kai had'e da mi'kewa a katifa tayi kwanciyarta. Ba a d'au dogon lokaci ba barci yayi awon gaba da ita. Dada ta bita da harara " wannan yarinyar daga gani 'yar daru ce bari kakannin naki suzo ni za'a barwa ke sai na koya miki hankali tukun, ke fure kira min su lamid'on kiji sun taho " furere ta amsa daya bayan d'aya suna ficewa daga d'akin. Koda furere ta kira wayar taji shiru ta tabbatar sun taho kenan tunda ta san ba sajin kud'in jirgi kullum a tafe suke.

Dada tana zaune tana lazimi ita kuwa shatu barci takeyi sosai abinta cikin kwanciyar hankali.

Liman na dawowa dada ta sake bashi labari, cikin farin ciki yake kallon shatu da ba abinda ta d'auko na uwarta da alama can dangin ubanta ta d'auko don ban ga kamanni ba " ya fada yana kallon dada, dada ta ta'be baki " yo kaima dai ka fad'a yarinya kamar bararo ko fulanin daji anyi magana tace inji ubanwa? Bari su su lamid'on suzo sa tantance idan jininsu ce ko Ba tasu ba sa san yarda zasuyi da ita, ni wallahi tulin sumar kanta ne ma da idanunta suke ban tsoro yarinya kamar d'iyar jinnu don kyau ". Malami dariyar su ta manya kawai yayi gani n shatu ta mi'ke ba tare da sanin dadar ba tana ta harararta " yo ki fito kice min kawai baki yarda dani ba mana Allah na tuba na me zan zauna ina muku'karya "

Sallamar su lamid'o ce yasa dada yin shiru bata tanka ta bata Allah ya sani tsoro yarinyar ke bata " maraba lale da iyayen maryama kuzo yau dai kuga jikarku d'iyar maryama " da sauri suka 'karasa d'akin suna watsa idonsa akanta ta kuwa 'kuri tana kallonsu.maman maryama tace "dada kada kice min wannan jinin maryama ce?" Dada ta ta'be baki "babu wai itace maryama ta haifo muku bararoji mai kama da ubanta. Ai mama bata'karasa jin abinda zata ceba ta 'karasa da sauri ta kamata ta rungume " Alhamdulillah ashe zan sake ganin maryama?" Shatu ta zame jikinta " ai kuwa ba zaki sake ganin maryama idan dai ba yau kema zaki bita yarda ta tafi ba ashe kuna sonta ku ka kasa bata burin ranta akan haka ta gudu ta bar gida ta bar gatanta ta gwammace rayuwa cikin daji ". Lamid'o zama yayi yana kallon yarinyar mai cike da tsiwa da surutu mama kuwa sake janta jikinta tayi " mun dade muna neman inda zamu ga maryama sai yau Allah ya nufa " cewar lamido dada ta girgiza kai " yau ai kaga dalilin da yasa ba zaku ga maryama ba tana can 'kungurmin dajin da ba wuta balle a samu tv ta ina zata ji cigiyarta da ake ba'kin cikina d'aya ne Allah ya dauke maryama ba tare da mun sake ganawa ba sai bararon 'yarta da ta bar mana" dada ta fad'a tana fashewa da kuka, mama ma zama tayi da'bas a kujera tana juya maganar dada lamid'on kuwa salati kawai yake ja , yanzu maryama ta mutu maryaman da ya dad'e yana nema ya nuna mata gata dama tuni ya yafe mata , mama kuka ta saka sosai tana rungume shatu a cinyarta cikin tsananin'kaunarta sam bata damu da daud'ar da take jikinta ba. Shatu taji zuciyarta ta karye da tausayin kakanninta mutuwar innaji ta dawo mata sabuwa kar itama ta rungume mama tana sake sakin kuka mai ratsa zuciya mama ta sake rungumeta tana shafa himilin gashinta.

Tsawon lokaci suna cikin jimami kafin lamid'o ya kalli shatu yace ya sunanki?" Murya a dashe tace " shatu " lamid'o ya jinjina kai " to ya akayi kika gane nan kika zo ina so naji labarinki da garin da kuka zauna da labarin rayuwar maryama a garin....... shatu ta gyara zama daidai lokacin da wani daddad'an'kamshi ya ziryaci hancinta tana d'aga ido ta hango mai sallamar da sauri ta mi'ke tana wara ido tana fad'in "innaji " mama ta kama hannunta " zauna aysha ba mamanki bace yayarta ce da take bi ana ce mata mammah " mammah da take tsaye ta waro ido tace " mama kada kice min y'ar maryama ce ina maryaman ina 'yar uwata alhamdulillah yau burina ya cika ". Mama hawaye ya ziraro mata don Ta san za'ayi haka Ta sani sarai deejah bata da buri irin taga maryama kullum zancenta kenan. Shigowar samarin yaran deejan yayi daidai da lokacin da mama tace " Addu'a 'yar uwarki take bu'kata yanzu Allah yayi mata rasuwa wannan y'arta ce Aysha da ta bari ". Gani su kayi mammah kawai ta zube numfashinta na 'kokarin d'aukewa da sauri y'ay'anta su kayi kanta suna jijjigata had'e da kiran sunanta amma shiru. Dada ce ta d'ebo ruwa ta watsa mata sai kuwa ta kawo ajiyar zuciya "mama don Allah kice min wasa kike ko mafarki nake ba maryama ta bace ta mutu " Lamid'o ya mi'kar da ita zaune Kafin yace " Allahn da ya fi mu son maryama ya amsheta addua tafi bu'kata yanzu sai kuma d'iyarta da ya bar mana mu dinga kallo muna jin dad'i Alhamdulillah da wannan hikima ta ubangjji ". Da sauri mammah taja shatu jikinta ba tare da 'kyankyaminta ta rungumta tana bata sumba a gefen kumatu cikin nuna mata tsananin 'kauna take share mata hawaye tana kallonta with so much caring , saurayin d'anta da yake gefe imran ya hau 'bata fuska cikin tsananin mamakin mammahn da bata'kyankyamin wannan yarinyar da Daud'a ta samu wajen zama a jikinta. Zuciyarsa har tashi ta fara yi saboda mutum ne shi mai tsananin'kyankyami da tsafta har da ta siyarwa. Runtse idonsa yayi kawai ba ya ma son sake kallon wannan kwamacalar. Ya bud'e kujerarsa wata karama da ya shigo da ita daga motarsa ya zauna. Sai a lokacin dada ta kula dashi duk da'kamshinsa ya sanar da duk ahalin gidan zuwansa'kamshin turarensa na amouage interlude 53 ya karad'e gidan sanye yake cikin black jeans da white long sleeve shirt ta Ralph lauren polo ya gyara glass dinsa da yayiwa idonsa kyau ba'a ganin 'kwayar idonsa gashin kansa a kwance luf, murya a dashe yake gaida lamid'o da dada. Dada cikin mamakin halinsa na ko da yaushe tace" jakadan turawa yaushe ka bayyana a 'kasar." Cije lips dinsa yayi bai bata amsa ba sai ammar kaninsa ne yace " yau kwanansa biyu " dada ta kyabe fuska " ai dama shi ba zaka ganshi ba Sai a dangin uwarsa saboda sun fimu farcen susa ammar kaine namu Allah yayi maka albarka yo wannan dama fuska kamar hadarin kaji wake maraba dashi ga shegen tsurfar tsaftar tsiya da 'kakale aikin banza ko mu har a gaya mana tsafta " . Ammar dariya kawai yake shi kuwa imran ya'kare tsuke fuska shi yasa sam baya son zuwa gurin tsohuwar nan mai shegiyar maganar tsiya. Lamid'o ya gyara murya kafin ya dubi Aysha " ina jinki ayshatu bamu labarin " ai kuwa ta sake gyara zama ta jingina kanta a jikin mommah ganinta take kamar innaji wallahi. Mommahn ta kara janta jikinta duk da warin da bakinta da jikinta yake bata'kayamaceta ba tana sauraran yarda take basu labari tiryan-tiryan.

Kafin ta gama bada labarin gaba d'aya gurin kowa kuka yake har ammar banda imran da ya d'auke kai gaba d'aya haushin yarinyar yake ji ga shegen surutu kamar kanya ba mamaki ma 'karya take ba jininsu bace idan banda haka mai ya had'a su da bararoji. Yanzu haka had'a baki a kayi da ita tazo ta cucesu mutanen duniya da basu da gaskiya musamman su d'in da an sansu a gari . " ya kamata ku bincika kafin ku tabbatar da gaskiyarta " hakan kawai yace yaja baki yayi shiru kamar bashi yayi magana. Momma ta d'ago a fusace zata yi magana lamid'o ya d'aga mata hannu ita kuwa shatu wata harara ta zuba masa da ya sashi ware ido yana kallonta cikin mamakin rainin da ta nuna masa sai kuma yayi Kwafa. Dada ta gyara zama " yo saboda Allah ai gaskiya bature ya fad'a nima fa mamaki nakeyi ace wannan bararojin jininmu ce to ka fad'a ace ina ka fito don dai mune masu kalan dangi sai kuma mu had'a jini da bararo " mommah idan ranta yayi dubu ya 'baci ta kalli dadan kafin taja'kafar shatu ta nunawa dadar " duk wanda ya san yar uwata maryama ya san wannan copyn kafarta ne da hannunta dada ki daina daka ta imran da shegen halinsa dinnan na bin kwakwkwafi a ina yasan maryama balle ya tantance jininta maryama da ta bar gida yana shekara guda duk'kaunar da maryama ta nuna maka ban mance da ita ba." Imran ya ta'be baki kawai ita kuwa shatu zaro hotuna tayi ta mikawa mommah da takardar da innaji ta bata tace ta basu. Mommah na gani ta mikawa lamid'o " Baba kalla kaga wallahi rubutun maryama ne wannan tabbas " lamid'o ya kar'ba ya kuma shaida tabbas rubutun d'iyarsa ne.

Sun ci sun sha akayiwa maryama addua sannan su lamid'o mazauna abuja suka fara haramar tafiya. Mama tace shatu tayi wanka ta canja kaya kafin su wuce shatu ta had'e rai sam bata san zancen wanka. Mommah ce tace" haba mama na zata zaki bar min ita mu koma kano tare musamman ganin bani da y'a mace ashe maryama ce zata haifa min" mama ta girgiza kai imran yana zaune a gefe yana adduar kada Allah yasa mama ta amine banda rigimar mommah ya zata kai musu bararo gida......😂😂😂😂 To fa!

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now