*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-22Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shige masaukinta,tayi shirin barci ta kwanta sannan Ta samu Hajiya mama da zancen tariyar shatu kamar yarda su kawu sa'idu suka bu'kata "Hajiya mama kin ji bu'katar da suka zo da ita na son shatu ta tare nan da one week." Hajiya mama da sauri ta kalleta "wani irin zance ne wannan ina ce dake mu kayi zancen nan,kika tabbatar min baki saka nan da sahekara biyar ma zata tare ba,su waye suka zo da wannan batun nifa bana son mutane su ga muna tauyewa yarinyar nan ha'kkinta a fara zaton don marainiyace don haka ni ban amince ba na tabbata kuma Babanku ma ba zai amince ba." mommah tayi 'kasa da kai tace "wallahi Hajiya mama nima yanzu na fiki da na sanin aurennan ji nake kamar na warwareshi,ban da kawu sa'idu ne ma yazo da maganar da tuni na gama solving d'in problem d'in to shi mutum ne kaifi d'aya da baya canja magana, shi ya gayawa Dahda yace a gaya min a bisa umarninsa yarinya ta tare ko nan da one week ne ba na son yaga kamar na nuna masa bai isa da yarinyar ba." Hajiya mama ta girgiza kai kafin taja ajiyar numfashi tace "Tir'kashi!ana wata ga wata yanzu shatu mai zata je ta aiwatar a gidan auren shekara sha hud'u da watanni?ai an daina yayin wannan auren,wallahi dama da kinyi shawara dani tun a farkon fari ma ba za'a yi wannan auren ba yanzu mai gari ya waya? Kin san dai babu dalilin da zamu bad'awa wannan dattijon arzikin 'kasa a ido dole mu amince da abinda yace tunda dai kina gani ranar shi yazo ya siya miki 'yanci a gidannan,dole mu amince Allah yasa haka shi yafi zama alheri a gareta,ikon Allah kenan idan banda haka ga iyayenta nan su hafsa ko maganar aurar dasu ba'a fara ba sai ita jaririya a kansu,to Allah ne kad'ai ya san lamarin da ya 'boye a bayan hakan sai mu bita da fatan alheri,amma ko nan gaba idan zaki aiwatar da abu ki dinga neman shawara don aikin mai shawara baya 'baci,kuma ko bakomai ba za'a zo ana dana sani ba Allah ya shige musu gaba yasa ace gwara da aka yi." Murya can 'kasa mommah tace "ameen ai insha Allahu ma zan ja kunnensa kada ya sake ya d'ora mata nauyin auratayya har zuwa san da za ta gama ko da secondary ne" murmushi mama tayi a zuciyarta tace "kayya ban da yaran zamani duk da dai aure ne aka yi shi ba da son junansu ba." momma ta gyara zama tace"kuma da dada zan had'a ta su tare har zuwa san da
Zamu ga kamun ludayin zamannasu,Sannan ga babansu ya bada ten million yace a siya mata kayan d'aki suna cikin account d'ina." "Kash ai da bai wahalar da kansa ba addarsu,kuma tabbas Na san Babanku fad'a zaiyi,amma shikkenan kiyi masa godiya ai hannun ba zai 'ki dad'i ba,mu ma za muyi namu 'ko'karin don Babanku yace kallon shatu yake kamar maryam gatan da maryam ba ta samu ba shi zai mayar kan shatu, zan kira shi nima da safe nayi masa godiya gobe sai ku fara shiga kasuwa da 'yan uwanki ku siya mata kaya Na gani Na fad'a kayan da ko gidan waye za'a kai ba'a ji kunya ba zan wa Babanku waya anjima kad'an shima ya bada abin da zai bayar." Momma tayi godiya ta mi'ke ta tafi wajen dahda don shima bai je dinner ba yace ba zai iya wannan rashin kunyar ta 'ya'yan zamani ba. Hajiya mama kuwa d'an kwanciya tayi da niyyar cikin dare za ta tashi tayi nafiloli Ta sake ro'ka musu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba don ita macece mai ibada kuma kullum addu'arta akan zuri'arta take.Sai 'karfe d'ayan dare dinner ta tashi duk da ango ya gaji amma kasancewar amarya tana ta girgizar rawa yasa dole ba'a tashi ba.rawa ce ta rashin kunya take ta yinta kamar yarda amaren zamani suke yi abin har mamaki ya dinga bawa jama'a musamman ango da abokansa. Da ya gaji ne ma ya mi'ke ransa a 'bace ya fisgi Hannunta suka fice daga hall d'in dinnerr.zuciyarsa a cunkunshe da ba'kin ciki kasancewarsa mutum mai kishi, bai san ba abinda mutane suke kallo a jikinta ba.
Tun a mota kuwa ya dire mata kwandon masifa kamar zaici babu. Ita dai tayi shiru don ta san ta 'bata masa rai. Yana parking kuma kallonta bai yi ba,ya bud'e motar ya fita.jikinta a salu'be ita ma ta fito daga motar tana kallo ya shige part d'insu ta san ko ta bishi ba zai saurareta ba don haka ta wuce cikin gida da niyyar ta kira shi a waya ta bashi ha'kuri,tunda dai ta lura har lokacin aikin su bai kammalu ba.