31

182 5 0
                                    

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-31

Elegant Online Writers.....

Tsaki kawai ya ja, yayi keeping wayar a side, ba ya son duba sirrin mutum sam, hakan ba d'abiarsa bace. Yana zaune har ta gama shiryawa kafin ya mi'ke su tada jam'in sallar.

——————————-
Bayan wata uku..

Kafin nan abububuwa sun fara da dama, wasu masa dad'i wasu sa'banin hakan. Shatu ta koma school kuma sosai ta mayar da hankalinta akan karatunta, gayu kam iya gayu yanzu Shatu ta zama 'yar gayu bugawa a jarida. Momma ta mayar da ita classic baby, koman ta mai tsada ake siya mata kayan cosmetics da kayan sawa duka masu tsada sosai take using. Girki ma Mommah ta dage sosai waken koya mata, tana kuma dagewa sosai da yake ta saka abin a ranta. Tuni suka manta da Batun Imran, da tun bayan tafiyarsa ya kasa kiran Mommahn, sau tari yana son kiranta sai dai yana tsoron fad'anta. Hakan yasa sai dai yawan turo mata text messages akai-akai, ita kuma ko ta karanta bata bashi amsa.wani lokacin ma ba ta karantawa take barinsa.

A yanzu kam Imran suna yawan samun sa'bani da Shaheeda, don haka kawai wata rana sai yaji ya tsaneta baya ko san ganinta. Wata rana kuma sai yaji ba wacce zai iya so bayanta. Sau tari tunanin Shatu yana damun zuciyarsa, har yaji ya d'okantu da son ganinta, amma kuma sai yaji take ya 'kara tsanarta. Don haka Shaheedah suka 'kara dagewa duk da ba su samu wanda zai kai mata sa'kon ba, suna matu'kar 'ko'kari wajen kawar da hankalinsa, ko da na lokaci kad'an ne. Suka kuma kawar da hankalinsa daga tunanin zuwa Nigeria yaji sam ya tsani zuwa Nigerian sosai kuwa, lamarin dai sai addu'a.

Gefe d'aya Ammar yana ta dakon jiran lokacin da Shatu zata gama idda don ya bayyana mata abinda yake ransa, ya kuma kafa kansa a zuciyarta. Duk da Mommah tace ya bari ta gama karatu amma yarda soyayyarta tayi 'karfi a zuciyarta baya zaton zai iya hakan. Don haka duk san da yayi tafiya tsarabarta daban take daga kayan sawa har kayan makeup ya d'aukewa Mommah su shi yake yi mata, har waya ya siyo mata Iphone 13 ya kuma koya mata yarda ake amfani da ita. Zuwa lokacin yana ta lissafi ta gama iddar ya fayyace mata sirrin zuciyarsa.

Yauma da wuri ta dawo daga Islamiyya saboda ciwon mara da ya addabeta. Tana shigowa direct bedroom d'inta ta wuce ta cire uniform ta fad'a toilet. Kamar yarda tayi hasashe period d'inta ne yazo wanda daga shi ta gama idda. Bayan tayi wanka ta kintsa kan ta sannan ta fice parlour.

A kitchen Ta samu Mommah, sakwara take da mitar egusi, gefe d'aya baseerah mai aiki tana wanke kwanu kan daga aka 'bata. A sanyaye ta shiga kitchen d'in ta zauna a d'aya daga cikin kujerun da suke working space na kichen d'in. Mommah cikin kulawa ta kai kallonta kanta tana murmushi "Ya aka yi lazyn Mommah gajiya ko yunwa? Don na san yanzu kin zama acici." Mommah ta fad'a tana murmushi. Basirah tayi dariya tace "Wallahi kuwa Mommah har cikin dare fa tashi take cin abinci." Mommah tace "Mhmn basira rabu da ita ai gashi nan sai uwar 'kiba take ta bud'e ko ta ina girmanta ya wuce shekarunta, yanzu fa idan tace shekarunta sha takwas ba sha biyar ba ba wanda ba zai yarda ba, yarinya ta zama uwar mata, wallahi ki rage cin nan, duk halittunki sun bud'e." Shatu ta turo baki kamar za tayi kuka, ta hau buga 'kafa tana kallon Basirah da take mata dariya. Cikin muryar shagwa'ba tace "Mommah wallahi kiyi mata magana ba ta fini 'kiba bama ni fa ba 'kiba nake ba cinyoyina ne suke 'kara girma don duk wanduna na sun yi min kad'an, sai kuma riguna na daga 'kirji wallahi duk sun matse ni." Mommah tayi dariya tace "Ai dama ba 'kiba kike ba bud'ewarce take bani mamaki, sai dai na godewa Allah da ya bani yarinya mai cikakken diri son kowa 'kin wanda ya rasa masha Allah." Shatu tana murmushi tace "Amma to me yasa Ya Imran ba ya so na?" Tuni annurin fuskar Mommah ya 'bace 'bat, sai kuma ta kalli Shatu tace "Ya period ya zo kuwa don a lissafina yau ko gobe ne." Shatu ta d'aga kai "Wallahi yazo shine abinda yasa ma na gudo gida da wuri, wannan zuwan ma sai da na samu pain." Mommah tace "Allah yasa kin gama a sa'a ubangiji ya tsare min mutuncinki 'yar albarka." Shatu tace "Ameen" jikinta a sanyaye.

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now