Me Zan yi da ita?
44
Da sauri Ammar ya 'dauke idon sa 'kirjinsa yana dukan uku-uku, tabbas ya yi mummunan gani da kuma ace ya san hakan zai ganin da bai shigo kitchen 'din ba. Ya runtse idon sa yana jin tamkar zuciyarsa za ta buga.
Shatu kuwa a zafafe ta kalli Imran "Burin ka ya cika, ya ganni tare da kai, wanda direct zai iya zargin wani abu wallahi ban yafe 'batawa masoyi na rai da kayi ba."
Shi 'dinma wannan karan takaici ya gume shi da sauri yace "Na ji da'di da ya gani, wa ya aike shi shiga gonar da ba tasa ba, ko an gaya masa bakin rijiya wajen wasan makaho ne, ai wallahi ka'dan ma ya gani matu'kar bai janyeba wata rana sai yaga abinda zai saka idon sa makancewa. Kuma wallahi duk ran da kika sake kiransa masoyinki ko mijinki a gabana sai na kusa cinye bakinki saboda sumbata, shine purnishment 'din ki." Daga haka ya juya da sassarfa ya bar kitchen 'din, saboda matu'kar zai cigaba da ganinta a hakan zai iya wuce gona da iri. Wani irin feeling yake ji na tashin hankali, wanda ya da'de bai samu kansa a wannan yanayin ba.
Shatu ta bi bayansa da kallo, ita kanta gaba 'daya jikinta a mace yake, rungumar da ya kai mata a bazata ta haifar mata da kasala, ta tayar mata da duk wata kwantacciyar sha'awarta, ta runtse ido tana sake sha'kar 'kamshin turarensa da ya gauraye jikinta gaba 'daya.
Ammar da Ta tuna ya sata fita da sauri, da nufin taje ta fahimtar dashi kada ya 'dora zuciyarsa a bigiren zargi.
Ta da'de tana knocking a 'kofar bedroom 'din kafin ya amsa murya can 'kasa "Yes come in, a bu'de take. Ya fa'da yana mi'kewa da 'kyar daga kwanciyar da yake, idanunsa sun ka'da sun yi jazur.
Jikinta a sanyaye ta shiga cikin 'dakin, idanunta a 'kasa tana wasa da fingers 'din ta. Ammar kuwa idanunsa a kanta yana tuno a yanayin da ya ganta a jikin Imran, ga 'kamshin turarensa nan ya baibaye jikinta don daga shigowarta bedroom 'din ya na'de 'kamshin turarensa, duk da zuciyarsa a zafafe take cike take da kishi, hakan bai hana shi sakar mata murmushi ba, yana yi yana kawar da 'bacin ran da yake fuskarsa. "Welcome Amarya ta, shigo mana ki zauna." Ya nuna mata kujera. Babu kuzari sam ta zauna har a lokacin idanunta a 'kasa. Kula da ya yi ta kasa sakewa ya sa shi cewa "Ko baki zo ba dama ina da niyyar kiran ki, maganar lefe ki ba ni sizes 'din ki idan kuma kin fi son ki siyo da kanki then sai na baki ku'din under wears 'din ku siyo da su Hafsa, tunda na ji sun ce kanon za su bi mu." Da sauri ta girgiza kai "Ka siyo kawai, zan turo maka sizes 'din ta whatsapp, amma don Allah kayi ha'kuri da abinda ka gani ba wani abu muke ba...." Da sauri ya dakatar da ita "Ban shirya jin komai ba, na fahimci abin da yake nufi shi yasa ma zan fara shirin bikin gadan-gadan, don ya fahimci da gaske nake ba gudu ba ja da baya, idan ma tunaninsa zan ha'kura na bar masa ke, ba zai yiwu ba."
Shatu kasa cewa komai tayi illa cigaba da jan zaren mayafinta da Tayi, har a zuciyarta ba haka ta so ba so tayi Ammar ya janye ya ha'kura. Amma ba yarda ta iya dole ta mi'ke ta fita daga bedroom 'din Ammar ya bita da kallo yana sakin ajiyar zuciya.
——————-
A ranar Imran ya juya zuwa kano so yake ya je ya think tsiye Shaheedah ya gano gaskiyar lamari, idan kuwa ya tabbatar ita ce ta ha'da kitimurmurar nan tabbas zai gwada mata zahirinsa. Ta jirgi yabi kuma tare da Akram da ya ma'kale masa ya tafi, ita kuwa Ikram ko kallonsa ba ta yi.
Ba tare da ya sanar mata zai dawo ba, zuwan da ake kira zuwan ba zata. Suna zaune ba je da kayayyakin da Shuwa ta kar'bo musu wajen yawon bin malamansu, ya tura 'kofar side 'din Anty Amaryar ya shiga. Ganin yarda suka razana ne daga ganinsa ya tabbatar masa akwai wani abu da basa so ya gani. Yana shigowa idanunsa ya sauka akan wata laya da aka gar'kamawa kwa'do (padlock). Gabansa ya fa'di, yayi excusing 'din su bai kuma fasa shiga ba.