Me Zanyi Da Ita?
38
Tsawon awoyi takwas Shatu Ta 'dauka a kwance, kafin su shigo don 'daga ta ayi mata wanka.
Mommah da kanta tayi mata wankar bayan nurse 'din ta nuna mata yarda zata yi, sosai ta gasa mata jikinta da towel. Shatu ta fito da 'kwarinta, duk da tana jin iska kamar ta 'dauketa, ba mamaki saboda an cire abin da yake cikin.
Kafin a mayar mata da drip 'din, Doctor ta bu'kaci a bata yaran su 'dan zu'ki Maman saboda hakan yana da amfani a wajen jariri. Kunya ce gaba 'daya ta dabaibaye Shatu tana jin tamkar 'kasa ta dare ta shiga.
Mursisi tayi, tamkar bata fahimci abinda Momma ta ke gaya mata ba. sai da Mommah ta fahimci kunya take ji, sannan ta shiga lalla'bata "Haba Shatu, daure ki ba su kowa daga haka ya fara kuma kina ji aka ce hakan yana da matu'kar amfani ga lafiyar su, ko ba kya son su zamo masu kuzari?" Hawaye ne ya fara ambaliya a idanun Shatu, a zuciyarta ta raya yau fa ake yinta! Yanzu ta ya zata iya shayar da su? Wallahi kunya ba zata barta ba. musamman ga Ammar yana zaune ya tasa baby girl 'din da kallo, ji yake tamkar ya lasheta ko don ganin tana kama da Shatu ne. Mommah ta kalli sashen da take kallo, tace "Au Ammar dama kana nan maza to ka bamu waje." Yana murmushi ya fice a zuciyarsa yace "Kwana nawa ne zasu zama mallakina a daina yi min rowarsu."
Yana fita Momma ta zura hannu da kanta ta zaro Maman ta ri'ko Baby ta manna maman a Bakinsa, da sauri Shatu ta runtse ido na tsananin jin kunya. Duk da babu ruwa a ciki sosai haka ya dinga zu'ka tamkar zai cire kan, da alama nan gaba Good sucker za'a yi.Hajiya Mama dariya tayi ganin yarda Shatu take ta kawar da kai idanunta kuwa a rufe ta kasa bu'de su. "Addarsu da kin bar masa haka, kada ya kwankwa'de ita kuma ya barta, duk da ni zan fi son haka kada ta ture min gwamnati wajen Alhajina."
Mommah tana murmushi ta mi'kawa Hajiya Mama shi kafin tace "Tun yaushe kuma kina ganin yarinya Balarabiya. Bari Alhajin ya zo ki ji mai zai ce." Tana ri'ke da 'yar ta sake ciro 'daya maman ta manna mata a baki. Wani karan Kuka Shatu ta saka da ita kanta bata san dalilin kukan ba sai dai na fassara shi a na farin ciki.Sun dai sha abinda suka sha amma ba don sun 'koshi ba, hakan yasa da Ammar ya shigo Momma tace yaje ya tambayo Doctor ko za'a iya basu madara? Take Doctorn ya rubuta musu madarar da za'a iya basu mai kyau ta S.M.A ya siyo musu carton guda a pharmacy 'din asibitin, sai da aka dama musu suka sha sannan suka samu barci mai nauyi ya 'daukesu. Shatu kuwa tsananin yunwa take jin musamman jin cikinta yayi fa yau.
Sai dare Dahda ya koma gida. Da azama Zainab ta tare shi cikin kwalliya ta gani a yaba. Ga 'kamshin humra da ta sha surkulle kala-kala da ta ba'de jikinta da ita. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar da take masa, da
Azama kuma ta rungumeshi tsaf a 'ko'karinta na son ya sha'ki sihirtacciyar humrar.Abin mamaki Dahda janyeta yayi gefe, tabbacin sa'kon nata bai isa in da take so yaje ba. Fuskarsa a ha'de tamau ya shige 'daki.
Zainab ji tayi kamar ta 'dora hannu a kai tayi ta zunduma ihu, ta rasa wani irin mutum ne Dahda da duk 'karfin asiri baya cinsa, duk da ta sani abin a bayyane yake Dahda baya wasa da ibada musamman sallolin dare da azimin litinin da alhamis, sallahr walaha da azkar na safe da yamma duk basa wuce shi. Sannan duk sanda zai yi barci sai ya karanta suratul mulk da suratul kafirun bayan azkar 'din barci. Amma duk ta jingine hakan ta 'dora laifin akan Mommah Dijah baiwar Allah gani take sihirin da take masa ne yafi nata 'karfi.
Hawayen idonta ta 'dauke tana tunanin Shikkenan ita kuma ta tabbata mara nasara a rayuwa, Dijah ce kullum take rinjaye a kanta. Abin ba'kin ciki haihuwar da Shatu tayi yau na 'yan biyu, ita tata 'yar bata jin ko 'batan wata ta ta'ba yi.Kamar an zungureta ta zaro wayarta ta shiga dannan kiran Shaheedah, ji take idan bata sauke duk wani takaicin ta akan ta ba yau ba zata samu salama a zuciyarta ba.
Shaheedah da ta ji kiran daga sama, a zabure Ta 'dau wayar gabanta yana sake duka, don tun da aka sanar da ita haihuwar ta rasa sukunin zuciya. Ganin Antynta ce ta 'daga a sanyaye. Kawai kuka ta saka mata. Zainab tayi tsaki "Ke da halla saurara min ki ji tambayar da zan miki, kina da ciki ko baki da shi?" A shagwa'be tace "Haba Anty Allah ya tsareni da haihuwa yanzu, ban shirya kwararra'bewa ba." Wani zagi Zainab ta 'kunduma mata kafin tace "Fahimtar dani ban gane mai kike nufi ba? Zuwa kika yi kika yi tsarin iyali ko me?" "Ni wallahi kwanaki ma na samu cikin ni nace masa bana so muka je muka cire shi." Zainab ta zabga salati "Shikkenan Shaheedah kin kashe ni amma kuwa ke dai nayi jakar yarinya da babu tunani ko ka'dan a zuciyarki, don ubanki to ga Shatu nan ta haifa masa twins, kin ga ko yanzu ta ci gida, ke sai ki zauna kiyi ta adana jikinki shashashar banza."
Cikin takaici ta ajiye wayar tana sake tsaki da la'antar shashashancin Shaheedah.Ita kuwa Shaheedah ta'be baki Tayi, cikin ranta ta ce "To ni ina ruwa na ta haifi duniya ma, ko da na 'boyewa Imran haihuwar ba don komai bane sai don kada yace lallai sai ya tafi Nigeria yanzu, idan ban da haka ni bana ba'kin cikin ta haifi 'dari ma.
Zainab kuwa da takaicin ya gama cinta, wanka Ta 'karawa she'kawa ta sake ambula sihirtacciyar humra, tayi shigarta cikin wata shara-sharan rigar barci ita a dole sai ta ja hankalin Dahda a wannan Daren. Ta fice bayan ta cilla chewingum a bakinta.
Taci sa'a kuwa ta samu 'kofar a bu'de, cikin farin ciki ta danna kai bedroom muryarta cike da kwainane tayi Sallama. Kamar wata zararriya ta saki zani da hijabin da ta shigo dasu tana jifan Manga da wani shu'umin murmushi, idanununta cikin nasa. Shi kuwa sak yayi yana yi mata kallon mamaki da tunanin ko ta fara samun motsuwar kwanya. Farinciki ya cika zuciyarta a tunaninta kallon tsananin bu'kata yake jifanta da shi. Ganin bai ta'ba tsayawa yayi mata wannan kallon.
Takaici ya gume Dahda, da sauri ya mi'ke idanunta zube Cikin shamulallen 'kirjinta da kyautatuwa yayi a 'boyesu saboda rashin kyan ganinsu, ba a bayyana ba. ko Mommah da nata suke cas gwanin sha'awa bata tayyara su haka a fili.Tsaki ya zabga ganin tana tunkaro shi yayi saurin dakatar da ita da hannunsa fuska a ha'de yace "Saurara am not in the mood, kuma Abuja zan tafi da sassafe na san ai kina da labarin kinyi Jikoki ko?" Ranta ya 'baci da salon wula'kancinsa, tunda aka yi aurensu bai ta'ba bu'katar ta ba kullum ita take kawo kanta idan bu'katar hakan ta ciyota, murya a sha'ke tace "Tabbas naji labari, amma ina tantama idan jikokin namu ne, kwananta uku da tarewa fa ya saketa, yaushe har ya sadu da ita ta samu ciki....." "Ke! Dakata bana son sakarcin banza kada ki sake ki sheganta min jikoki, ko kwana 'daya tayi ya saketa,
Hakan ba yana nufin ba zai kasa tarawa da ita ba, kuma 'ya'ya na sane don haka kada na sake jin wannan banzar maganar mara kan gado." Daga haka ya ja duvet ya rufe jikinsa idanunsa a lumshe yace "Idan kin tashi fita pls off the light asuba ta gari." Tsananin takaici ne ya rufe Zainab bata san sanda ta kai kanta bakin 'kofa tana takaicin asarar ku'din humra da tayi. (Haka lamarin yake wanda bai ji bari ba zai ji hoho!)—————
Takwas na safe a cikin asibitin tayi wa Dahda, tuni y kira Ammar ya tambayi 'dakin da suke, don fushi yake da Mommah ba zai iya kiranta ba, duk da tun jiya yake ganin kiran ta amma yayi burus ya 'ki 'Dauka, so yake ya nuna mata abin da tayi 'din zahiran bai ji da'di ba kuma bata kyauta ba.
Bayan Knocking na minti 'daya ya tura 'kofar bakinsa 'dauke da sallama ya shiga. Momma cikin farinciki ta amsa masa, ya 'dauke kai kamar bai ganta ba direct 'bangaren da Hajiya Mama ya isa har 'kasa ya dur'kusa ya gaisheta. Cikin kunyar surukuta take amsawa tare da yi masa murnar haihuwar da aka yi masa. Ya amsa shima 'din idanunsa a 'kasa, yana wasa da hannunsa, ya dubi Shatu da take 'ko'karin mi'kewa zaune yace "A'a Shatu yi kwanciyarki ke da baki da lafiya." A kwancen ta saki murmushin kunya ta gaida shi, ya amsa fuskarsa 'dauke da tausayinta yarinya 'karama 'yar shekara sha shidda da haihuwar 'yan biyu, gani yake kamar lamarin yayi mata girma. A hankali yace "Ya jikin naki?" "Da sau'ki Dahda" ta fa'da murya a sanyaye. Yace Masha Allah" yana kar'bar baby boy 'din da Mommah take mi'ka masa tana gaisheshi. Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Mamaki ya kama shi ganin yaron a hannunsa yana tuno sanda aka haifi Imran haka yake kwabo da kwabo kamar yayi kaki. "Masha Allah ubangiji ya raya ka. Amma ba kai ya kamata na fara 'dauka ba amaryata ya kamata na fara 'dauka." Ya fa'da yana ajiye shi a makwancinsa, ya 'dauki Baby Girl 'din yana bin Hajiya Mama da kallo da ta kama Shatu "Mi'ke maza muje ki tattaka, sun ce ki dinga tattakawa kada wajen yayi tsami." Daga haka ta kama ta tana takawa a hankali suka fita. Dahda yayi murmushi don ya san hakan wata dabara ce ta dattijan mutane masu nagarta irin dai surukarsa Hajiya Mama. Suna fita Mommah ta kama shi suka zauna, kanta ta 'dora a kafa'darsa suna kallon babies 'din tare. Muryarta ta kwantar sosai kafin tace "Yalla'bai am very sorry please naga fushi kake dani sosai, Don Allah ka yafe min, wallahi jiya ko kyakykyawan barci ban yi ba tunda nayi ta kiran wayarka ka'ki 'dagawa hankalina ya tashi please ka yafe min!" Cikin sauyin muryar da ta san tana narkar da zuciyarsa ta fa'da, tuni kuwa ya lumshe idonsa cikin sake godiya ga rabbi da ya azurta shi da mata ta gari mai amsa laifinta, ba kuma ta girman kai wajen bashi ha'kuri. Cikin wasa ya shafa kumatunta "Na yafe miki Deejah na, da kam nayi fushi sosai tunanina ba ki mayar dani wata tsiya ba, amma yanzu da naga zanka'de'diyar amarya ta duk wani 'bacin rai ya tafi. An gayawa Imran ni na kira wayarsa bana samun sa I don't know why?" Mommah wani murmushin takaici tayi kafin tace na gaya masa ga kuma amsar da ya bayar." Ta mi'ka masa wayar bayan ta bu'de text 'din da Imran 'din ya turo. Dahda cikin 'bacin rai ya ke mi'ka mata wayar cikin fushi yace Allah ya kyauta amma kuwa zai sha mamaki na a lokacin da yazo zaiyi iko da 'ya'yan nan." Mommah ta kama hannunsa tana matsawa a hankali tace "Ai ni na riga na yanke hukunci, hukuncin da na tabbata sai ya kusa buga zuciyarsa daga Shatu har 'ya'yan na mallakawa Ammar rana ita yau za'a 'daura musu aure......"