63

345 12 3
                                    

https://www.wattpad.com/user/Nazeefah381?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=Nazeefah381&wp_originator=GHG3oXDuy%2FyzvnGIdOQobZD6X5lwLSdr1D2fuHcQ2YaWzGdHWjyTkcuCrRetsuFuOhOOST8i92DU1zHjm6baftBk6FpQLITawz9m%2F5qBhp2oUpPmsvRwZiKU4cLCvC8Q

Me zan yi da ita.....

Gida kam yayi kyau sosai tamkar a 'kasar turawa parlour komai anyi shi bisa tsari. Shatu ta dinga zagaye gidan cikin tsananin murmushi da murnar cikar burinta, tabbas rayuwa tazo mata da d'imbun nasarori wanda ba ta Ta'ba mafarkin kasancewarta a cikinsu, Gida mai kyau Miji Nagari ga arzikin haihuwa da Allah yayi mata musamman twins da ta haifa, tabbas Allah ya cika mata ni'imominta na duniya, abinda ya rage mata kawai yau ta ganta ta zama cikakkiyar lawyer. Shikkenan ita kam sai tace tazo duniya a sa'a. Addu'arta kullum Allah yaji 'kan Innaji da Babaji har da Gwaggoji da Moddibo. Hawaye ya zubo mata, da ta tuna dasu sune kad'ai basu mori arzikin nata ba, Ta so ace suna raye sun ga yarda Shatu mai idon ta a loko ta koma. Imran ne da sauri yasa hannayensa yana wiping tears d'in da take fitarwa. Da murmushi a fuskarsa ya ce "Me ya saka a wannan hawayen zubowa?" Itama murmushin tayi a hankali ta furta "Na tuna iyaye na, shine dalilin zubar hawaye na, Innaji da gatanta ashe ta bar mu mu kayi rayuwar jeji a can Niger, insha Allah kuwa zan kai musu ziyara, zan sa a gina musu makarantar Boko da ta Islamiyya har da masallachi duka sada'katul jariya ga iyaye Na, in dai Na zama lawyer Na fara tara ku'din salary na." Murmushi Imran ya saki yana jan hancinta ya ce "Ba sai kin zama lawyer ba, Hayateey dole na cika miki burinki Insha Allah." Tsananin murna yasa ta doka tsalle ta rungumeshi tana furta "Thankyou so much 'kalbeey." Dariyar ta bashi ganin har yanzu ta'barar Shatu tana nan da yarintarta. A zuciyarsa ya furta auren irinku Shatu rahma ne da Allah yake bawa  'kayyadaddun bayinsa, ciki da waje kinyi min ba gi'bi.

Bayan wata biyu kusan ince gaba d'aya familyn d'in suka tafi umara Iyayen Mommah da su Nahna Hisham da matarsa har da hafsa da ta haihu kwana Arba'in da suka wuce, Hajja da Ammar da Matarsa Mommah da Dahda Imran da Shatu, Akram da Ikram, masha Allah haka suka d'unguma umara cikin tsananin farin ciki da walwala.

Hameedah ma ta so zuwa sai dai laulayin da take yasa mijinta ya hanata zuwa, don tun bayar nadamarta da addu'oin da aka yi tayi ya fito ya sanar da ita gaskiya dama duk shiri suka had'a da Imran ba wani asirin Shuwa da ya cishi sun dai yine don su ganar da ita sharrin dake cikin tarayya da irin su Shuwa. Tuni Ayda da Amna sun 'kara girma kamanninsu sun 'kara fitowa sosai zahiran da Mommah suke kama. 

Sati uku cif suka d'auka a saudiya suna ibada sannan suka dawo zuciyarsu cike da ya'kinin ubangiji ya amsa musu duka addu'oinsu.

Shatu dai suna dawowa ta koma makaranta gadan-gadan ta kama karatu, Mommah take kaiwa Aidah da masu aikinta guda biyu, idan ta dawo sai ta biya ta 'daukosu. Don ta iya driving sosai.

Imran ya tattara ya dawo Nigeria don ba zai iya nisa da Shatu ba, ya dai 'dora duk d'awainiyar ayyukansa Na can akan wani d'an turkiya da ya tabbatar yana da ri'kon Amana. Shi kuma ya bud'e wani companyn anan kano, zai iya cewa Auren Shatu ya zamo masa da alhairai masu tarin yawa don ta ko ina bud'i yake samu.

Ba kuma ruwansa da kowacce mace don tabbas Shatu kullum sai ta d'auke masa sha'awar kowace mace, yana da ya'kinin ko kyauta aka bashi mace zai ce ya yafe don ya san Shatu number one ce a fagen kishi. Shi yasa ma yaji a zuciyarsa sam ba shi da muradin 'kara aure.

—————-

'Bangaren su Zainab kuwa tuni suka yi baran-baran da Shuwa kowa ya kama gabansa, Shaheeda kuwa da kyar ta samu wani 'karamin ma'aikacin gwamnati ta aura don ya fi mata zama ba auren don sam ba zata iya kame kanta ba. Duk da rashin mutuncin mijin haka ta ha'kura ta aureshi tayi matu'kar da na sanin biyewa Sharrin zuciya da turbar da suka 'dorata akai. Haka dai dama abin yake duk burin Zainab yabi ruwa, 'karshe dai ba arzikin ba mallakar mazajen wad'anda basa so su zauna gidan mijinsu kuwa gasu nan suna zaune abinsu lafiya, cikin kiyayewar ubangiji su kuma sai Allah ya barsu da iyawarsu, da malamansu da bokayensu.


Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now