Hajja ae gidan kamsh
Turaren wuta
Turaren gashi
Turaren kaya
Turaren wanka
Kulaccan
Kurkur oil
Humran
Kabbasa
and more
Whatsapp number 09120958937In dai turare mai nagarta kuke nema to kun dace, ku nemeta domin ku kwashi gara'basa.
Me Zan Yi Da Ita?
Kai Alhamdulillah Masha Allah jiya sister ta ta sha addu'a am really appreciated wallahi. Jazakumullah bil jannatil Aaliyah.
ME ZAN YI DA ITA?40....
Da wata irin zabura ta mi'ke cikin matsanancin 'bacin rai tace "Wallahi Imran ka yi da 'yar halak you will pay for it." Daga haka ta shige 'dakin ta cikin tashin hankali, tabbas dole ta kira Antyn ta ta gaya mata kalar iskancin da Imran ya tsiro da shi. Alamar duk wani shiri na su ya ruguje ko yana daf da rugujewa.
Imran tsaki yayi yana kaolin Hisham da duk ransa ya 'baci, da abinda ya aikata. Zai yi magana Hisham ya dakatar dashi. "Am highly disappointed wallahi au Imran gaskiya ban ji da'din abinda ka aikata ba da alama yarinyar nan ba ta jin da'din zama da Kai, me yasa ka canja ne completely kamar ba Imran 'din da na sani ba?" Tsaki Imran yaja yana zama saman kujera kansa kawai ya dafe yana murza goshinsa, kafin ya 'dago idanunsa sun burkice sunyi jajur "Ba zaka gane ba Hisham gaba 'daya yarinyar nan ta fice min a Zuciya, ga takaici da dana sani da nake na sakin waccen Yarinyar." Da sauri Hisham ya ware ido "What! Tsaya wai wa kake nufi? Kada kace min Shatun Mommah?" Direct Imran ya amsa masa "Yes exactly ko ina da wacce na saka ne bayanta?" Wata dariya ce ta 'kwacewa Hisham "Ashe kuwa ka sha giyar wake in dai Shatu ce, kada ka manta Shatu fa Fulanin Daji da kace ko an 'daura maka ita a 'kafa sai ka kunce, yarinyar da Mommah ta za'ba maka ka saketa within three days da aure ita kake gaya min kana da na sanin sakinta? To me zaka yi da ita? Kada kace min dawo da ita zaka yi domin kuwa tayi maka nisa tuni ta yi aure ta haifi twins." Wata irin zabura Imran yayi hankalinsa a tashe ya mi'ke yana kallon Hisham, kafin ya ji wani jiri na 'dibansa "Kace min wasa kake Hisham? Please!" Hisham yayi tsaki akan me zan yi mk 'karya gaskiya na gaya maka."
Daga haka ya zauna yana kallonsa "Ba abinci ne a Gidannan? Naga tun da na shigo ko ruwa baka bani ba.." Imran bai ko kalleshi ba ya zauna dafe da kansa. Zuciyarsa take wani irin tu'ku'ki tamkar ya mutu, da gaske ne Shatu tayi aure? Shatun da yake da niyyar mayar da aurensu, Shatun da ta mamaye duk wani gurbi da tunani na zuciyarsa, Shatunsa da yake tuno da duk wasu ni'imominta da Allah ya bata a lokacin da ya tara da ita, itace wani banza can ya aureta har ya 'dan'dani ni'imarta yaji taushi da santsin fatarta, yaji za'kin ba'kinta ya 'dan'dani da'di da gar'dinta har da albarkar zuria a tsakaninsu. Da sauri ya hau yamutsa sumar kansa yana fa'din No No No! Da 'karfin sa. Hisham tsayawa yayi cak yana kallonsa tsananin mamakin lamarin yake yi. Kafin ya ja tsaki yace "Tunda baka yarda ba kaje Nigeria 'din ka gani. Ai gani ya kori ji, kuma idan babu Abinci a gidannan ni zan kama gaba na." Mi'kewa kawai Imran yayi hannayensa zube a aljihu ya hau struggling a parlourn kafin ya juyo cikin kyakykyawan kallo ya tsare Hisham da idanunsa cikin zafin rai yace "Wani mai gangancin ne ya aure min mata?" Tsaki Hisham ya ja kfin yace "Kayi Istigfari ka daina kiran matar wani da sunan matarka, mutumin da ya aureta har da albarkacin zuri'a tashi guda twins ta haifo masa alamar an sha soyayya kafin a haifo su don sosai yaron yayi kama da ubansa.." flower verse 'din dake gefensa yayi cilli da ita ji kake wani taratsatsa bai damu ba ya tashi ya bi ta cikin glasses 'din ya isa inda Hisham yake. Wuyansa ya da'kuma a wani irin yanayi ya furta "Don't tell me rubbish, ya ishe ni Hisham, ka gaya min sunansa nace kawai!" Hisham ya ta'be baki ha'de da mi'kewa yace "Sunansa Muhammad, malam zaka bani abinci ko na kama gabana na gaji da wa'dannan silly Questions 'din naka kana nufin don ka saketa sai a rasa mai aurenta duk da tsananin kyan ta?" Idanunsa akan jinin ya ke masa magana "Idan ban da hauka ji yarda ka jiwa kanka ciwuka tun ma ba kayi arba da yarda ta goge ta zama kyakykyawa ba, da kuma santala-santalan yaranta ina ji da sai zuciyarka ta buga don tsananin takaici, ga shi wanda ta aura 'din yana tsananin sonta ya kuma fi ka komai ku'di kyau uwa uba dukiya......" da 'karfi Imran yace "Hisham! I'm tired of you nonsense zo ka fice min a gida kuma bikin naku ma ba zan zo ba, sai me don tayi aure ina ce dai ba gwauro ka ganni ba da matata." Hisham yana dariya yace "Fankon? Ko ba kai da bakinka kace duk ciko bane yanzu ne zaka kirata mata? Gida kuma kar kazo amma ka sani ko yanzu ka mutu, da kyar rahmar ubangiji ta sameka saboda rashin biyayya ga iyaye, Na barka lafiya dama sada zumunci nazo muyi tunda kuwa kayi min korar kare sai nace saduwar alheri." Daga haka yayi saurin ficewa daga gidan saboda dariyar da take shirin fallasa shi. Sai da ya bar harabar gidan sannan ya shiga tuntsira dariya tamkar mahaukaci sabon Kamu.