Me zan yi da ita?
Littafin
Nazeefah Nashe
Elegant Verified Online Writers......
08033748387
https://www.wattpad.com/user/Nazeefah381?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=Nazeefah381&wp_originator=GHG3oXDuy%2FyzvnGIdOQobZD6X5lwLSdr1D2fuHcQ2YaWzGdHWjyTkcuCrRetsuFuOhOOST8i92DU1zHjm6baftBk6FpQLITawz9m%2F5qBhp2oUpPmsvRwZiKU4cLCvC8Q
**********************************
Sun samu tarba a 'kauyen sosai duk da ba su san da wacce su Momman suka zo ba, sai da suka huta sannan Mommah cikin son tsoratar dasu Ta ce "Mu dangin Shatu ne wato 'yar wajen innaji maryamu ni d'in 'yaruwarta ce yayarta ciki d'aya mun samu labarin Shatu tana garinnan shine muka zo tafiya da ita.
Kaf wajen ba wanda zufa bata karyo masa ba, musamman ganin Ammar da Hisham da shigar suit ba'ka'ke sai kace 'yan sanda.
Nan take tsoffin suka shiga rantse-rantse rashin sanin inda Shatun take Sadau ya ce "Aradu kakarta tana rasuwa ta arce ta bar garin nan. Sai da Mommah taga sun razana sosai musamman da suka ji ance za'a kamasu sannan ta sanar dasu gaskiyar lamari ta kuma yi musu nasiha sosai musamman akan wula'kanta maraya bayan a al'kura'ani mai girma ubangiji ya tsoratar akan Hakan, ya kuma yi umarnin a kyautata musu jikinsu ya yi sanyi sosai musamman da ta kwatanta musu da rasuwar d'aya daga cikinsu ya bar yaransa shin zai so a wula'kanta su. Kaf is wajen ba wanda bai yi hawaye ba, suka dinga yiwa Mommah godiya da ta sanar da su abinda ba su sani ba ashe al'amarin maraya mai girma ne a wajen ubangiji, al'kawari suka d'auka sosai don gane kuskurensu, kuma zasu je har birnin suka Shatu su bata ha'kuri da izinin ubangiji. Mommah ta ji dad'i sosai ta ce "Haka ne ya kamata."
Kwanansu d'aya cur kashegari da safe suka d'unguma suka tafi har da sadau da Iroro don suje su ga waje idan sun tashi zuwa ba sai sun nemi d'an rakiya ba. Mommah ta zube musu alheri sosai da kud'ad'e ta raba musu jari take suka dinga murna suna fad'in "Ahe shatu alherinsu ce amma suka wula'kantata." To dama haka lamarin ubangiji shi yasa ba'a so a karan farko ka wula'kanta mutum alhali baka san tarin baiwar da khali'ku ya yi masa ba, ba mamaki wata rana shine zai taimakeka to da wani idon zaka kalleshi bayan tarin wula'kancin da kayi masa.
Shatu sosai ta ji dad'in had'uwa da tayi da dangin babanta, murnarta ta gaza 'boyuwa akan fuskarta, sai murmushi take saki ko bakomai dangin uba da su ake ado, Hajja ma da farin cikinta ta dinga gaisawa da su ba tare da ta nuna musu 'kyama ba ko kad'an.
———————————-
Kwana ukun da Mommah ta basu Na cika ta tattara su Shatu suka koma sashenta Imran kamar yayi kuka gwara ma Ammar ya dake bai nuna rashin kunyarsa ba. duk da dai shi tasa matar daman raguwa ce bata fiya jurar fitinarsa ba tunda ta samu ciki kuma sai ta 'kara langa'bewa.
Imran da kyar ya gama sallama da Shatu har da hawayensa sosai yake jin zafin rabuwa da Hayateey d'insa, a kunne ya rad'a mata "Please ki dinga satar hanya idan ba so kike na kusa zarewa ba, wallahi da gaske ba zan iya juriyar wannan abin ba, Gaskiya banda uwa uwa ce da na nuna mata ban amince ba."Ya fad'a yana saka idanunsa da suke she'kin 'kwalla cikin na Shatu, mamaki ya kamata da taga da gaske Imran hawayen yake. Hannunsa ta ja tana matsawa a hankali ita kanta ba wai tana son rabuwarsu bane amma bata son ta yiwa Mommah da take wa kallon mahaifiya tawaye. Matse hannunnasa tayi da 'karfi alamar ta rasa abin cewa, sai kuma can murya a cunkushe ta ce "Please kada kaci amanata, kada ka kai bu'katarka wajen kowa duk sanda kake son kusantata ka tura min text ni kuma zan biyo dare Nazo." Kyakykywar runguma ya kai mata ya ce "Na sani ke kanki zaki wahalar rashina kusa da ke saboda jikinmu ya zama tamkar d'aya, dole zamu ha'kura da abinda Mommah ta ce, amma hakan ba zai saka mu jefa kanmu a halaka ba, ki cire kunya please ki dinga zuwa muna gaisawa ko da sau d'aya a rana." Yatsa ta sa ta lakaci gefen hancinsa ta ce "Insha Allah." "Ban yarda ba promise?" Hannunsa ta kama ta dun'kule cikinnata a hankali ta d'aga Kai. Ya rugumeta tsam a jikinsa, sannan ya taya ta jan trolley zuwa sabon d'akin da Mommah ta basu ita da Mubeenah a 'bangarenta.