*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-32Elegant Online Writers.....
Momma ta sake gyara zamanta, tana kallon Shatu "Kada ko da wasa ki gayawa kowa kina da ciki, idan nace kowa ina nufin kowa, yanzu tunda hutu kuke jibi insha Allah zan wuce dake Abuja a can zaki haihu, idan yaso a samo miki malamin addini da wanda zai dinga koya miki karatun boko, kafin ki haihu mu san mai za'a yi." Shatu ta d'aga kai cikin 'karfin hali jikinta duk a sanyaye yake, ta mi'ke ta fita bayan Mommahn tayi mata umarni.
Ko da ta isa d'aki tsayawa tayi cak a gaban mudubi, ta d'aga rigarta hannunta akan shafaffan cikin da ko alamar da nuna zaunuwar ciki bai yi ba.sai dai motsin da cikinnata yake yi ne ya tabbatar mata da akwai cikin, lokaci d'aya ta saki hawaye sai kuma murmushi kamar wata zautacciya, a fili ta furta oh ni Shatu nice zan zama Mama". Ta saka tsalle cikin tsananin murna saboda dama Allah ya sawa Shatu jarabar son yarinya. Tayi sak kuma cikin tsoro tana tunanin Innaji kada dai itama ta mutu kamar yarda Innaji ta mutu. Zama tayi gefen gadon hannu bibbiyu tayi tagumi tana tunanin Innajinta. Take hawaye ya gauraye idanunta cikin tsananin kewar Innajinta.
———————————-
Ammar tunda ya shiga d'akinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai struggling a d'akin zuciyarsa cike da tunanin abubuwan da yaji suna tattaunawa. Shatu da ciki? Kuma cikin Imran, hankalinsa kam ya tashi duk d'okinsa na Shatu ta gama idda ya sanar da ita abinda yake kwana yake tashi dashi, da gaske yake son Shatu, zai iya cewa tun ba yanzu ba ya fara sonta, tun kafin ayi bikinsu da Imran, lokacin da aka yi auren hankalinsa ya tashi sosai, sai dai da ya tuna Imran ba sonta yake ba hankalinsa ya kwanta, ya tabbatar ko mu dad'e ko mu jima zai rabu da ita a taurin kai irin na Imran ya san ba zai zauna da ita ba, sai dai kash burinsa bai cika ba ashe Imran ya gama da Shatu. Amma duk da hakan ba zai fasa ba, ba zai daina jumirin Jiran Shatu ba har zuwa sanda zata haife ta gama idda. Idan ya so tana haihuwar sai ya fitar da abinda yake cikin ransa a d'aura musu aure. Da wannan tunanin ya mi'ke ya nufi d'akin Mommah.A zaune ya samu Mommah da alama tayi zurfi a tunani, jin sallamarsa ne ya sata saurin d'agowa tana amsa masa sallamarsa bayan sakin gwauron ajiyar zuciya.
Ammar ya 'karasa ya zaune a gefenta, hannunta ya kama a hankali yace "Mommah kiyi ha'kuri kada ki dinga d'aga hankalinki akan Imran addu'a kawai zaki yi masa nima kuma zan taya ki, sannan cikin Shatu ba zai hana ni aurenta ba idan ta haihu." Da sauri Mommah ta d'ago tana kallonsa, kafin tace "ya aka yi kasan tana da ciki?" Murmushi Ammar yayi kafin yace "Duk naji hirarku d'azu, Na biyo ku da magungunanta da kuka manta a mota na samu kuna zancen." Mommah ta saki ajiyar zuciya kafin ta kalleshi tace "Ammar ina son wannan ya zama sirri tsakanina da kai pls, bana son kowa ya san da zaman cikin nan, hankalina ya fi kwanciya da hakan ina son na bawa mutane da dama mamaki, ka kuma kwantar da hankalinka Shatu tamkar ka aureta ka gama in dai ina raye, saboda na lura da abubuwa da dama tun farko da kai Shatu ta dace ba da Imran ba, saboda haka a ranar da ta haihu ranar suna za'a d'aura aurenku, saboda bana son yaron ko yarinyar suyi maraicin uba, sannan bana son su ri'ki Imran a matsayin Babansu." Ammar farin ciki ya cika zuciyarsa, burinsa zai cika a lokacin da ya cire tsammani da tabbatuwar hakan. Shatu burin ran sa zata zamo matarsa, ai ji yayi kamar Mommah ta tsundumashi a aljannah, ya shiga furta "Nagode Mommah ubangiji ya 'kara girma, amma kuma ya za'a yi da karatunta?" Mommah tace "Idan mu kaje Abuja zan samar mata fitattun malamai zan kuma basu ko nawa ne su dinga yi mata lesson a gida, tana haihuwa sai ta zana S.S.C.E, burina a yanzu bai wuce ayi auren ba, ko don na cusawa Imran ba'kin cikin da ya cusa min, Na san tabbas nan gaba sai yayi da na sani in dai dangin Abbanku ne." Ammar ya mi'ke farin ciki fal zuciyarsa tare da tunanin Shatu ta zama tasa confirmed.—————
Da daddare kuwa bayan Dahda ya dawo ya ci abinci ya gama duk wasu al'adu da yake yi kafin ya kwanta, Mommah ta kawo masa zancen son tafiyarta Abuja, sai dai ta 'boye masa musabbabin tafiyar tata ta dai sanar dashi tana son zuwa kai Shatu hutu. Bai kawo komai a ransa ba yace "Allah ya kaimu gobe zan saka Ammar yayi muku booking flight, hakan yayi kyau ko bakomai ai sunyi miki kara kuma na tabbata suna son ganin jikarsu." Murmushi kawai Mommah tayi alamar ta jin dad'in barinta da yayi.