*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-10Sosai Hajja ta sake razana ganin shatu tana nufota, fad'i take " Don Allah kada ku cutar dani ku fad'i mai kuke so nayi? Ni baiwar Allah ce ba ruwa na da kowa a duniya." Shatu ta 'kya'kyata wata mahaukaciyar dariya " so muke kada ki sake cutar da hadizatu idan kuma kin'ki zaki ga sakamakon taurin kai kina ji?." Da sauri hajja ta d'aga kai " Na bi Allah na biku insha Allah ba zan sake komai ba" shatu ta sake kecewa da dariya bayan jin abinda tace cikin daka tsawa tace " To rufe idonki kuma kada ki sake ki bud'e sai nayi nisa da tashi sama." Da sauri hajja ta rintse idonta gam, shatu da sauri ta fice daga d'akin ta shige d'akinta. Ai cikin azama hajja tana bud'e idonta tayi saurin mi'kewa ta fice daga d'akin jikinta har makyarkyata yake, A tsakiyar falon ta tsaya ta dinga kwalawa mutanen gidan kira. Yarda muryar tata ta karad'e gidanne yasa d'aukacin mutanen gidan fitowa, suka tarar da ita a dur'kushe hankali tashe suke dubanta. Dahda ne yayi'karfin halin cewa "lafiya hajja?" Hajja ta zuba masa wani irin kallo " ina kuwa lafiya ko da yake yanzu ba zan yi magana ba sai da safe kai ni falonka a can zan kwana kuma kana zaune daga gefe na Yau gamo nayi da aljannu a gidannan." Dariya ce taso kama Ammar ganin yarda ta ha'ki'kiance take'buya a bayan dahda. Momma kuwa baki ta ta'be ta juya ta koma ciki bayan tayi wa amaryar mijinta kallo d'aya. Ita kuwa amaryar bin bayan mijinta tayi tana tsinewa hajja a zuciyrta yarda zata'bata mata daren amarci duk da tanadin da ta shirya masa ga turarukan tsubbace tsubbace da ta ambula a jikinta banda wanda ta turara sai da ta kusa samo kan mai gidan sannan wannan tsohuwar zata rusa mata shirinta.
'Karfe bakwai nayi Hajja ta fito babban falon gidan bayan ta tasa 'keyar dahda a gaba " Muje ka had'o min kaf kan ahalin gidannan ina da magana dasu " cikin tausasa murya yace" Hajja da kin bari gari ya 'kara wayewa ...." " Na'ki Na bari garin ya waye ahmadu nace na'ki Na bari manga uba na, saboda ba kai kayi gamo da abinda Na gani ba ko." Tayi saurin tare shi da sababin fad'a. Shiru kawai yayi yabi bayanta zuciyarsa fal 'bacin rai don dai uwa uwa ce da ba wanda ya isa yazo gidansa ya aikata masa haka.
A tsaye suka tarar da momma tana sake gyara cushions d'in main parlour d'in tas ta gyara gidan sai'kamshin turaren wuta gidan yake. Dahda ya bita da kallo ganin yarda tayi kyau sosai cikin wani pink lace duk da fuskarta ba fara'a amma dai bata fasa gaisheshi ba, sannan ta'karasa gefen hajja da take zaune saman kujera 'kafa d'aya kan d'aya tana girgiza jiki fuska cike da masifa, muryar mommah a cunkushe itama tace " Hajja barka da safiya an tashi lafiya?" Sai da Ta 'kare mata kallo sama da 'kasa cikin masifa tace " 'kalau sumul na tashi duk da ba haka kika so ba, cikin kiyayewar ubangiji na tashi lafiya, saboda kin san tsaye nake akan 'kafafuna wajen ibada, wai ke deejah har tsubbun taki ta kai ki fara turawa mutum aljannu ? Saboda Na saka d'ana yayi aure, to albishirinki wannan auren mutu ka raba kuma idan kin tashi yau da daddare ki turo min sarkin rauhanai ma ba aljannu ba , Aljannun naki mai suka isa suyi min sunzo sun baki labarin yarda Na fatattakesu da ayar Allah." Shatu da sauri ta juya Ta shige kitchen saboda dariyar da Ta ciyota. Hajja Ta cigaba " kuma ni da gidan d'ana ba inda zani zama daram." Mommah shiru tayi tana al'ajabin hajja yau kuma gingimemen sharrin da za tayi mata kenan lallai tsanarta da hajja ta girmama. Hajja ta juya gun Dahda " kai kuma manga kana tsaye baka tambayeni ba'asi ba, yo ai dai kace hajja mai ya faru kike wannan fad'a da safiya haka tunda kai haka Allah yayi ka kamar d'an fari, to ko Mahmud da yake d'an farin baya abin da kake. Wato kana ji cikin dare matarka tayi min turen jinnu wai suna gargad'i na na rabu da hadizatu kaji fa wai dijah yanzu har tayi shaharar turo min Jinny?" Dahda ya girgiza kai saboda 'bacin rai ma kasa magana yayi ya zuba mata ido kawai. Ammar ne cikin d'aure fuska yace " ko dai mafarki kika yi hajja ina mommah taga aljannun da zata turo miki? Mu tunda muke gidannan ba wasu aljannu." Girgiza kai hajja tayi sai kuma tace " Ba shakka, 'karya nayi maka kenan? To manga ubanka da yake zaune shine ma'karyaci ba ni ba. Ra'ayal aini yarda nake ganinka haka naga aljannu ina tofa musu addu'a suna ihu da tumami suna fad'in deejah ce ta aiko su, haka Na 'konesu 'kurmus ba mamaki idan kuka je d'akin ma kuka ga haya'kin da tokarsu, yo ni za'a kawowa zancen banza aljannun me Allah na tuba". Ba wanda ya sake mata magana haka ta mi'ke ta koma d'akinta tana sake bambamin tijara. Shatu da take la'be a bayan 'kofar kitchen ta girgiza kai had'e da yin 'kwafa ta juya ta shige d'akinta .
'Karfe biyu daidai ba'kin Abuja suka sauka. 'Kannen mommah ne hisham da hafsa sai nahnah. Kyawawa dasu farare tas kamar su innaji da mommah. Shatu tana zaune tana lesson driver ya dawo daga'daukosu d'aya bayan d'aya suke bin ta da kallo ita ma tana kallonsu, Hisham ne ya bud'e mata alamar ta taho ya dube ta kafin yace If I guessed It right you're shatu ?na canka shatu ce ko?" Da sauri ta d'aga kai hisham da su nahna suka rungumeta da ihu cikin tsananin farin ciki suna murnar ganinta hakanne Yasa Ammar da mommah da imran saurin fitowa suna murnar ganinsu , kasancewar sun dad'e basu zo hutu ba nahna da hafsa suna turkey, shi kuwa hisham mate d'in Ammar ne tare suka gama makaranta a egypt, Imran ne yayi oxford university england. Murna da hayaniyar da suke ce a main parlour ta fito da mutanen gidan har Hajja da ta fito tana dogara sandarta da yake tana da 'kiba ciwon'kafa ya sata a gaba.
'Daya bayan'daya take hurga musu kallo tana amsa gaisuwarsu a gatsine " Ba shakka dijah kin ci gida kin mallake manga kin mallake dukiyarsa ga 'yan uwanki ma sun zo sun taru a gida, kai Allah wadaran naka ya lalace su kuma wad'annan gand'an-gand'an 'yan matan daga ina?" Nahna fuska a d'aure za tayi magana mommah ta girgiza mata kai " Don't say any word here ku shiga part d'ina am coming." Kasancewar akwai tarbiyya hakan yasa basu shiga ba suka ja hannun shatu su kayi gaba su imran ma suka bi bayansu. Mommah ba tace da hajja komai ba ta mi'ke zata wuce. Cikin masifa Hajja tace " la shakka ga 'yar iska wato kin bawa banza ajiyata nayi tayi ko? To kinyi da gyatumarki mai kama da sadakar yallar nan kuma da ni kike zancen yau yau zasu juya su koma, kuma kaf jakunkunansu sai nazo Na caje don yanzu haka wani tsubbun suka kawo miki an ji anyi miki kishiya azo a koreta ko? Kuma idan zasu tafi ki tattara har bararojinnan su tafi da ita shaid'anun banza kawai." Momma wani abu Ta had'iya kawai ta juya ta shige part d'inta zuciyarta na tafarfasa, itama fa mutum ce ba dutse ba dole zuciyarta zata dinga zafi da irin cin kashin da hajja take mata amma ya zata yi dole ta girmamata tunda d'anta take aure. Sai da Ta share hawayen fuskarta sannan ta'ka'kalo fara'ar dole ta bud'e'kofar falonta.
A zazzaune ta samesu tuni sun watsar da lamarin hajja sun saka shatu a tsakiya, sai fito mata da tsarabar kayayyaki suke wanda suka siyo mata a turkey da wanda kakanninta suka bata, sai nuna mata tsananin soyayya suke, hakan yasa fara'ar fuskar shatu ta kasa 'boyuwa kowa nuna mata 'kauna yake ashe ba zata yi maraiciba bayan mutuwar innaji, ashe yanzu ne zata fara fuskantar farin ciki a rayuwa. Ta lura kowa sonta yake idan ka d'auke Imran da yake gefe yana harararta 'kasa-'kasa. Hisham ya dubi Mommah kafin yace " Hope dai by now an yi mata register a school ?" Momma ta girgiza kai " so muke brain d'inta ya da'n bud'e before taking her to school insha Allah" Imran ya ta'be baki cikin takaici yace " Allah wahala kawai kuke wannan yarinyar she will never be socialized kamar yarda kuke so , rayuwar daji fa tayi ai sai a slow kawai dama kun daina wahalar da kud'inku kawai don wasting time dinku zaku yi ji fa wasu tarkace a hannunta " ya fad'a yana nuna hannunnata, gaba d'aya gurin shiru kawai su kayi zuciyarsu kowa da mamakin imran. Hisham ne ya katse shirun yana dafa Imran yace " Amma son banyi expecting hakan daga wajenka ko bakomai she is your bloody sister da nake fatan mu nuna mata soyayya mu kuma bata jin dad'in da ta rasa." Tsaki yayi Hasfa ganin yarda mommah ta damu sai ta sako wasa cikin zancen " Rabu dashi Yaya hisham bayan ma bai san yarda rana zata fad'i ba " da sauri ya zaro ido " wa? God forbid wallahi insha Allah rana a gabas zata fad'i ko don ba kiga babban kamun da nayi ba classy baby ga good hygiene ga kyau ga ladabi." Tsakin da mommah ta zabga ne yasa yin shiru duk gurin kuma aka saka dariya ban da shatu da imran ya riga ya 'bata mata rai. Mi'kewa tayi zata shige ciki taji Nahna tana cewa " Mhmn Allah ya kaimu lokacin da zaka zo kana'yar murya " ya mi'ke yana fad'in " ai ko a 'kafa aka d'aura min wallahi sai na cire na yar " Mommah kwafa tayi tana nuna musu dinning " Hisham close the chapter kuyi taking shower ku ci abinci duk da dai tafiyar dad'i kuka yi tafiya a jirgi" Nahna tace " Yo wa zai zo kano from Abuja a mota."