6

172 7 0
                                    

*🤍ME  ZAN YI DA ITA?*🤍

        NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
 

-6

ELEGANT ONLINE WRITERS ******


Ammar cikin nutsuwa yake driving har suka isa cikin garin kano'karfe 8:00 dai-dai, shatu lokacin har fitsari ta janga'ba a kujerar ba tare da sanin mommah ba.

A unguwar railway su kayi parking bakin wani tangamemen gida gari guda, da tafkeken gate, gani tayi kawai gate din ya zuge ba tare da tasan wanda ya zugeshi ba.Automatic gate ne. Ammar yayi packing a packing space. Momma ta bud'e  'kofar had'e da jan hannun shatu a hankali ta waro ido ganin gurin da lema murya  'kasa-k'asa tace " shatu fitsari kika yi?" Shatu ta d'an ta'be baki " To mommah fitsarin ne ai ya matseni kuma ina cewa zanyi zai fara masifa ". Momma tayi saurin rufe mata baki don kada imran da ya fice da sauri yaji "Muje kafin ya ankare " da sauri shatu ta fita daga motar ammar yayi dariya yana tunanin yarda za'ayi da cakwakiyar'yar mommah da yayansa, yasan dai kwarai za'a buga show.

Suna shiga tangamemen falon kamshi ya doki hancin shatu ga sanyin A.c ta lumshe ido had'e da runtse ido tana bud'ewa tabbas dai da a mafarki taga wannan gidan to tabbas zata ce aljanna tayi mafarki da ita. Momma ta ri'ke mata hannunta ta kaita'kofar wani sashe suna shiga ta kaita wani d'aki kusa da nata " daga yau ga d'akin Ayshata  muje in nuna miki komai a toilet kiyi wanka ko da yake wannan wankan na yau yafi 'karfinki da kaina zan miki da nace ma in kaiki saloon to bana so su fara ganin wannan daud'ar kannaki jira ni anan am coming." Da sauri ta fita daga d'akin shatu ta sake ware ido tana kallon gadon yanzu wannan d'akina ne gado na da sauri tayi tsalle a gadon tana tintsira dariya " ahe dai ina da gata muke zaune can a dajin Allah aradu innaji ta kwari kanta cabd'i"

Shigowar mommah yasa tayi shiru momma ta shige toilet ta zube kayan da yake hannunta duk mayukan wanke kaine da combs dama toilet din akwai dryer. Shatu ta fara'bata rai sam bata son a ta'ba mata kai da dai mommah zata gane da ta kyaleta. Momma ta zare du'kun'kunennan mayafin nata ta zaunar da ita bakin jaucuzi ta fara kunce tufkekken gashin kanta mommah tayi mamakin ganin tumulin gashin ta ji'kashi ta saka shampoo ta barshi for a minutes sannan ta fara had'a ruwan da zata dirje daud'ar Jikinta.
Sosai ta wanke kan sai sheki yake wajen wanka ne shatu Ta fara'boye-'boyen jiki mommah Ta harareta " zaki tsaya ko sai na 'bata miki rai ke da ko irgar dangi baki fara ba to koma kin fara ni ba uwarki bace ". Shatu Ta d'an sunkiyar da kai mommah Ta saki murmushi " Ashe kina da kunya." Tas shatu Ta fito duk da dai sai a hankali zata baje amma ko bakomai anfi baya.

Fitowarta ne yasa momma ta tsaya domin ba kayan da zata bata tasa tsaki tayi tace "zauna nan ina zuwa bari na aika ammar ya siyo miki ready made kafin da safe mu shiga kasuwa ".

Tana fitowa babban falo ba taga ammar ba sai imran da yake zaune yayi wanka da fara jallabiya tas a jikinta mai gajeran hannu a jikinsa yayi kyau sosai kana ganinsa kaga mutum mai mutu'kar tsafta. Sai baza'kamshin turare yake yunwa ce take cinsa ya aika ammar yayi musu take away don baiga alamar masu aikin sunyi girki ba, may be basu zata zasu dawo ba." ina Ammar?" Momma Ta fad'a tana tsatstsare sa da ido , Imran murya can'kasa yace " Na aike shi eatery samo abinci." " sai ka tashi kai na aikeka samowa Aysha kayan sawa ba tazo da kaya ba " ta fad'a tana juyawa ba tare da Ta lura da waro idon da yayi ba yana ji kamar ya rusa ihu ganin zata shige yace " kud'in fa?" Ba tare da Ta juyo ba tace " ka siya da naka " dunkule hannu yayi ya daki d'aya cikin d'aya kamar ya tashi sama kuma ya juya da sauri ya fice daga cikin gida.

Da yaje ma rasa mai zai d'auka yayi ya d'auko mata riga da wando Na maza kawai bayan ya kintata tsahonta yaga ba zata zarta hakan ba. yunwa yake ji sosai amma mommah Ta sashi zuwa siyawa wannan bararojin kaya.

A falo ya ajiye kayan ya nunawa Ammar " mikawa mommah " ya zauna a dinning ya fara cin abincin" mintuna kad'an mommah da 'yarta suka fito Ta saka riga da wando duk da Na maza ne sai sukayi mata kyau, mommah Ta gyara mata kai an tsaga an raba biyu, jelar gashin Ta sauka har dantsen hannunta gashi mai yawa masha Allah sai 'kamshi take kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai ya cigaba da cin abincinsa momma taja kujera tace "zauna " Ta zauna tana hararar naman da yake ci tsoronta Allah kada ya cinye naman hakan yasa ta shiga tunanin yarda zata koreshi daga wajen ta kuwa daddage ta saki attishawa sai kuwa ga majina ta biyo hancinta da sauri ya furzo abincin dake bakinsa ya mi'ke da sauri ya bar wajen. Zuciyarsa na tunzirashi yayi mata dan banzan duka kawai. Ita kuwa dariya Ta fara babbakawa " Nagode Allah yo mommah da fa cinye naman zaiyi kaf da banyi haka ba " mommah duk da dariyar da take cinta ta gintse tace " baki kyauta ba kings yanzu kin hanashi cin abincin Ba kyau kada ki sake Ammar bishi da abincin d'aki". Ammar ya mi'ke yana murmushi sosai yarinyar take burgeshi shi kam sam bata damuwa sha'aninta take zubawa.

A parlornsu ya ganshi a zaune ya dafe kansa sosai tausayinsa ya kamashi ya 'karasa da abincin yana dafa bayansa Bros sorry don Allah ga abincin momma tace a kawo maka " zubawa plate din ido yayi yana saurin ja baya gani yake zai hango majinar a cikin abincin murya can 'kasa yace " 'dauki Ka tafi dashi ba zan ci ba ta had'a Ta cinye kana tunanin yau zan iya cin wani abin ko mai na kai bakina sai na tuna 'kazamar yarinyar nan bitch " ya mi'ke ya shige bed room direct toilet ya shige ya sakarwa kansa shower.so yake yaji zuciyarsa Ta daina'kuna.

Yana dawo da abincin mommah Ta kalleshi " baya ci ne?" Ammar a sanyaye ya d'aga kai yaja kunnen shatu dake zaune " if you try it again Allah sai Na zaneki mommah kija mata kunne ". Narai narai tayi da idonta " To ni ina ruwa na kawai atishawace fa tazo ya zanyi da ita to " " Excusing kanki za kiyi ki fita kiyi haka ake yi wai ke baki da manner ne?" Kuka Ta saka " Ni ka daina min wannan maganar ban iyata ba idan bakwa san zama na kuma kawai kuce na tafi. Ya bud'e baki zai yi magana mommah tace " Ammar ya isa ai da gaskiyarta to ya zatayi da atishawa fisabilillahi ni fa kada wanda ya 'kara takura mata duk wanda Ba zai iya zama ba shi ya bar gidan. Ammar ya bud'e ido "Mommah......" "kada kace komai " ita kuwa shatu plates d'in imran taja ta fara cin naman cewa takeyi " Yo ai yayiwa kansa ni kuwa gaba Ta kaini......" Ammar murmushi yayi ya wuce yana furta " Allah ya shirya ".

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now