Me Zan Yi Da Ita?
41
"Eeh tayi aure..." Yasirah ta zuba mata ido da sauri kafin ta mayar da kallonta akan Imran da ya runtse idonsa gam yana furta "Oh shit!" Yana buga hannunsa a table, sai kuma ya mi'ke hannunsa saye cikin aljihu ya bu'de ainahin 'dakin Shatu, fes dashi 'dakin ga wani 'kamshi da ya kamashi ram na ainahin turaren da take amfani dashi. Idanunsa ya sauka akan wangamemen pic 'din twins suna babies, zuciyarsa na dukan Tara-tara ya 'karasa gurin pic 'din... cikin takaici yake shafa hoton kishi ya cika zuciyarsa fal. Ya shiga tunanin da tuni zuri'arsa ce wannan 'din. Ji yayi har jiri na neman kada shi hakan yasa ya kwanta flat a saman gadon Shatun, tunaninta ya dinga bijiro masa a yanayin da ba zai fasaltu ba. Da sauri ya dinga jan istigfari tunawa da yayi a yanzu Shatun matar wani ce. Jikinsa a sanyaye ya bar bedroom 'din nata bayan yaji a yanzu ba abinda yake bu'kata irin yara.
Ko da ya fito Anty Amarya ba yarda ba tayi dashi ba ya tsaya ya ci abinci amma ya girgiza kai "Alhamdulillah nagode" ya yi furucin yana ficewa da sauri. Motar Mommah ya hau ya bar gidan.
Takaici ya cika zuciyar Anty Amarya da Shaheedah da suke jin tamkar su saka kuka.———————————
'Karfe 9:00 dai-dai suka isa garin katagum. Gidan a cike yake dan'kam nan ido gaba 'daya ya koma kan Shaheedah kowa mamakin ramarta yake yi. Wai don ma a haka Hijabi ta sako har 'kafa.
Lokacin Mommah da Shatu basu iso ba suna gidan su Mommahn, Hajiya Mama ce kawai ta taho amma har su Hafsa da Nahna suna can Gidan ba su taho ba, haka nan Hisham da Ammar.
Dalilin hakan bayan ya gaida jama'ar da suke dam'kar a gidan ya fice da sauri burinsa yaga Mommah. Ita kuwa Shaheedah Hajiya Mama da farinciki ta tare ta, ta sa aka kawo mata kayan breakfast.Drivern Alhaji Baban yana parking Imran ya fito, cikin takunsa na ginshira, kayan sun amsheshi sun masa kyau sosai ba'kin yard ne a jikinsa 'dinkinsa na kullum gajeriyar riga da gajeran hannu, wannan karan dai anyi abin arziki ya saka hula a kansa, kuma hular ta amsheshi sosai da sai 'kamshin turare yake yi.
Ya da'de yana Knocking kafin Shatu da take kitchen tayi saurin fitowa kanta ko 'dankwali babu, Gashinta gaba 'daya ya zuba har gadon bayanta. Doguwar riga ce a jikinta mai jikin robber da tabi ta kwanta a jikinta ta kuma lafe ta fidda duk surar jikinta. Fitowar Hisham da Ammar ce ya sata jin wata matsananciyar kunya tayi saurin bu'de 'kofar kafin ta juya ta shige kitchen ya danno kai cikin parlourn ha'de da 'kamshin turarensa da ya baibaiye parlourn, wani shock da bugawar zuciya ne ya samu Shatu a lokaci guda, haka nan Imran da Ammar da yake gefe. Da sauri ta juya ta shiga kitchen ba tare da tayi masa second look ba.
Ko a kitchen 'din ma tsayawa tayi hannayenta dafe da 'kirjinta tana saurarar yarda bugawar zuciyarta ke 'karuwa, idanunta na sake hango mata fuskar Ammar da ya sake 'kawata ta da kyakkyawan saje, yayi fresh sosai alamar Naira ta zauna masa. Wani danshi taji a saman fuskarta, da hakan ya sata saka hannayenta ta ji ko menene mamaki ya kamata da taji wai ashe hawaye ne yake zuba daga idaniyarta ta, hawayen da za ta kira na takaicin ganinsa, ba ta so ganinsa ba a lokacin da komai ya 'kure. Mutumin da take kwana take tashi dashi, zuciyarta kullum bata fasa tunanoshi ba, in dai za tayi sallah sai ta Ro'ki ubangiji ya zare mata son shi daga zuciyarta, amma abin al'ajabi kullum soyayyar nan ninkuwa take, musamman idan tana ganin Akram da yake tsananin kama da shi. Idan tace bata son Imran ta yiwa kanta 'karya shine first love 'dinta da kuma shi ta so tayi rayuwar aure na dindindin, rayuwar da babu tasgaro a cikinta, sai dai tuni 'kaddara ta riga fata a yanzu dai kam ba zata ta'ba iya kallon idon Ammar tace bata sonsa ba, ko ba zata iya aurensa ba ya riga yayi mata halarcin da bai kamata ta bar shi ba a cikin ko wane hali. Sai kuma ta tuna da jan kunnenta da Hisham yayi akan ko da Imran yazo ta gaya masa tayi aure 'ya'yan bana sa bane, haka ma ya ro'ki Mommah, hakan ya sa ta sakin murmushi a zuciyarta tace "Za'a buga drammer domin a jikinta ta ji kallon da Imran yake jifanta dashi, ta shafa kanta da ko head tie babu, idanunta akan 'kirjinta da hips 'dinta da suka cika fam a cikin rigarta, wata kunya ta kamata ta san dole ko ba so duk namijin da ya ganta a wannan shigar ya baibayeta da kallo, wanda ba zai kasance na komai ba sai na zallar sha'awa. A hankali tace "Astagfirullah! Don kuwa sarai ta san ba muharramanta bane Hisham ne kawai muharrimanta. Ba tayi aune ba ta fara jiyo 'kauri, da sauri ta kai dubanta ga naman da take tafasawa za tayi shawarma, tuni ta waro ido ganin naman yana shirin 'konewa saboda tunanin da ya aureta na ba gaira ba dalili, tunda dai bata san da wacce Imran yazo ba. Duk da Uncle Hisham ya fara bata labari.