5

198 8 0
                                    

*🤍ME  ZAN YI DA ITA?*🤍

        NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387

ELEGANT ONLINE WRITERS......

-5....

Momma ta sake gyara murya cikin kwantar da kai ta furta " Don Allah mama ki bar min ita kinga ke kina da wasu y'an matan ga hafsa ga nahnah ni kuwa Allah bai bani haihuwar d'iya mace haihuwar ma daga  'ya'ya biyun ba saketa nayi ba."  Mama ta girgiza kai " Gaskiyar magana addarsu ba zan iya ba su wadancan da kike magana ina na gansu kun kwashe kun kai can uwa duniyar turkey karatu, yanzu kuwa ita zan dinga gani kamar maryama da na rasa ". Dada taja tsaki " kaji min wani zancen shirme Idan da wanda ya dace ya ri'ke wannan 'ya ai dijama ce yo fisabilillahi tana da wata uwar ne bayan ita a duniya ai itace take da iko da yarinyar nan ba ke ba daga kawai kin haifi uwarta, don haka na zartar da hukunci dijama ki tafi da ita ke kad'ai zaki iya da wannan bararojin mai ido a tsakar ka ko samarinki sa ladabtar da ita musamman wancan miskilin kafi mahaukaci ban haushi da idanunsa kad'ai sun isa hukunta 'yar banza idan ta'kamarta ido ai gidan ta tarar." Wani kallo shatu ta watsa mata a zuciyarta tace " sai nayi maganin wannan tsohuwar kafin ta sheka barzahu ". Liman da lamid'o murmushi kawai suke ganin yarda mama ta had'a rai alamar sam hukuncin dada baiyi mata ba sai dai ba yarda za tayi da ita. Momma kuwa sai murmushi take tana sake jan shatu a jikinta. Daga gefe kuwa imran ne yake ta watso mata harara kamar ya sha'keta ta mutu tabbas banda an kusa bikinsa zai bar 'kasar da amaryarsa 'yar abuja zubin london inji dada da barin'kasar zaiyi kafin a sake ganinsa kuwa sai an yara. Ya kalli agogo yana mi'kewa "Momma ya kamata muyi haramar komawa saboda akwai abinda dada ya sani a company ban kai ga hattamawa ba kuma kinga mota muka biyo " Duk wannan dogon zancen yayi shine saboda baya so dada tace kwana za suyi yamma tayi. Dada ta zabga masa harara da ficificin idonta na tsoffi " Ma'karyacin banza Ka dai ce ba zaka iya kwana anan ba saboda shegen gwalangwasonka kada kayi ubanka'karya salihin bawa dashi ko da yake shima ya zama d'an banza watansa nawa bai zo ya dubani ba ko don bani na haifo wanda ya haifi ubansa ba amma ko bakomai ai ubannasa aminin lamid'o ne, shikkenan dai Allah raka taki gona ban kuma ce Ka gaya masa ba bare kasa ya daina min aiken wata da ya saba ko bakomai ai d'an albarka ne tsiyarsa ta rashin zuriya ta bishi sahura dai taga takaici da jikanta baya son ziyara". Gaba d'aya gurin ba wanda baiyi dariya ba har shatu idan Ka d'auke imran da ya sake kicin-kicin da fuska ya d'aureta tamau ya mayar da kud'in da yayi niyyar bawa mutanenta da ita kanta aljihu, yasa kai ya fice bayan yayiwa liman da lamid'o sallama. Dadah ta gyad'a kai "jarababbe umma ta gaida aisa gayyar na ayya ke dai dijama kin haifi ala'ka'kai." Murmushi kawai tayi ta mi'ke tana ri'ke da hannun shatu ta furta "Allah dai ya shirya mana zuri'a bari mu wuce kada dare yayi don ma mugun gudu yake a motar ". " wani irin gudu ki gaya masa ya tafi a hankali bana son shashanci " lamid'o ya fada yana kallon babbar d'iyar tasa cike da kulawa ya san sosai take jin zafin rad'ad'in mutuwar nan " kuma ki cire damuwa a ranki kada kije kiyi tunani har ciwonki ya tashi maryama addua take bu'kata yanzu, ita ta dace ko bakomai tayi mutuwar shahada tsakaninmu da ita addu'a dafatan muma mu cika da imani " lamid'o ya sake fad'a yana kallon'yar tasa ba tare da dubi da hararar da dada take watsa masa ba " Ba shakka zamani wato lamid'o a gabana kake lallashin  'yarka ta fari kai Allah da ya tsinewa nasara da ya kawo boka har tayi sanadin rusa al'adarmu da dane ko inuwa d'aya ba zaka had'a da dan fari ba balle har zance ya shiga tsakaninku tur da wannan wayewa, ko da yake har gwara kai ba gani ba na tsaya ina magana da kai da iyayenan zasu dawo da sunyi tur da haihuwata kai ku tashi ku tafi kada wanda ya sake dawo min nan balle ku sake sakani rashin kunya wai da bakina nake kiran sunan lamid'o waliyazubillah duk da dai na uku ne kai amma wa ya san na farko da na biyun Allah na tuba tun kan ayi suna suka mutu ai dai kai ne dai na farkon...." gaba d'aya gurin dariya ake suka fice suna mata sallama Momma tace " Danger number one "


Ta mudubin motar ya hango fitowarsu da sauri ya waro sexy eyes ganin da yarinyar aka fito mai hakan yake nufi wai wannan'yar dajin motarsa zata shiga kai ina impossible ai da sake.
Ya fito daga motar daidai lokacin'karasowarsu mommah tace "bud'e motar mana imran, yamma fa tayi " ya 'bata fuska sosai " Momma yamma fa tayi kuma gaskiya gudu zanyi sosai why not ku kwana anan idan yaso gobe nayi muku booking flight ku taho."  Momma  ta watsa masa wani kallo ta san sarai nufinsa Aysha ce baya son ta shiga motar bai kuwa isa ba zata nuna masa ita ta haifeshi " sannu ubana to yau d'in za mu tafi idan yaso'karewar gudu ka mayar da motar taka jirgi bud'e mana malam " fuska a d'aure tamau tayi maganar tana mamakin halayen imran da sam bata san inda ya kwaso su ba. Jiki a salu'be ya bud'e motar had'e da mi'kawa Ammar key d'in " kuje I will manage ko a hotel ne by morning insha Allah zan bi flight na taho and make sure kuna zuwa ka kira car wash su d'au motar nan every thing na cikinta ya zama clean." Ammar ya kar'bi key had'e da bud'e driver seat momma ta waro ido tace " yana ina shi " Ammar yaja numfashi don yasan fad'an momma shi kuma yana son d'an uwansa baya son'bacin ransa " Momma zai zo ya tuna akwai yana da abinda zaiyi a bauchi ". Gani yayi kawai momman ta fita ware ido tayi tana kallon imran jingine jikin bishiyar'kofar gidan kallo da take masa ne yasa shi rusinar da idanunsa baya jurewa sun saba tun suna yara da idon take hukunta su, hanya kawai ta
nuna masa ta shige. Ransa a 'bace ya bita tabbas ya san dai kafin ya isa gida wani ciwon sai ya kamashi.

Shima Ammar d'in kallo d'aya tayi masa ya fito ya koma d'aya seat d'in zuciyarsa fal da tausayin d'an uwansa don ya san kam yau sai ta Allah.

A salu'be ya tada motar bayan yayi adduar tafiya الحمدلله الذي سخر لنا... zuwa Karshe ya kuma ware a .c don ya kore masa warin jikinta da dum da motar tayi har da su fess turaruka. Momma tana kallonsa tana'bata rai cikin'kyamar banzar d'abi'arsa. Shatu kuwa kwafa tayi don sarai ta san ma'anarsa ta hakan wato kyamarta ma yake yi ai kuwa za tayi maganinsa kafin ta bar motar, ba mamaki ma bayan fitsari har kashi sai tayi a motar....😂😂.

Wani irin gudu yake shararawa duk a tsorace suke a motar ganin yarda yake mommah kuwa ta'ki magana sai addu'a da take a zuciyarta. Shatu kwance take luf a cinyar mommah wani barci ne yake fusgarta, cikin hukuncin ubangiji kuwa cikinta ya fara murd'awa ta daddage ta saki wata tusa da ta d'umame motar gaba d'aya Allah ne ya kiyaye saura'kiris ya saki sitiyarin motar yaja wani wawan burki, ammar ya dinga'kok'arin'kinshe dariyar da ke cikinsa amma ina sai da ta bayyana a guje ya fice tuni ya fara kwara amai, Ammar ya fito masa da ruwa yana aikin jera masa sannu. Momma kuwa duk da tausayinsa ya shigeta haka ta gintse. Shatu sai dariya take yi tana'karawa momma tace " wallahi shatu idan ya kamaki ba ruwana " " yo mommah ba k'yamata yake ba saura gudawa ma " Mommah ta waro ido " kada ki fara shatu idan ba so kike ya kashemu a titi ba kina ganin wawan burkin da ya sha Ba don Allah ya kiyaye Ba kowa a bayanmu ba da tuni mun mutu." Shatu ta zaro ido " momma mutuwa kuma a yanzun da zan fara jin dad'in rayuwa aradu ma ki daina wagga zance yo tunda nake ban ta'ba tunanin zan shiga wannan abin ba ban Ta' ba ganinsa ba sai yau amalanke muke shiga garinmu da zanzo nan kuwa motar kayan miya Na shigo aradu dana shiga nan na zata aljannah nake " mommah ta girgiza kai "To kada ki sake abinda zai zubar damu a titi motoci su take mu mutu." Ta d'aga kai. Ya huta sosai kafin yace " Ammar jeka Kai bud'e glasses d'in motar ventilation ya shiga ka fesa air freshners tabbas Ba mamaki mommah ta d'auko ajalina " Ammar ya d'an shafa bayansa " bros ba zaka mutu ba just because of her sai kwananka ya 'kare Ka dinga daurewa pls mommah bata jin dad'i the way she looked at you ka dinga controlling temper Dinka" hannu ya d'aga masa " jeka kayi abinda nace maka kawai ni Na san abinda zanyi muna zuwa gida I will pack everything nawa na tare " Ammar ya zaro ido " saura fa 4 months bikin ya zaka tare yanzu " Imran tsaki yayi idan ban tare ba so kake na mutu ko?" Ammar ya juya yana'kunshe dariyarsa ya gama duk abinda ya sashi sannan ya dawo yana kallon yarda yake mayar da numfashi alamar ya galabaita a aman " Bros mu tafi kada dare yayi " mikewa kawai yayi ya mi'ka masa key d'in " muje kayi driving I can't do it "

Ta mudubin motar yake watsa mata harara ta saki baki sai barci take har da munshari ya sauke duk glasses d'in iska Na shiga motar a zuciyarsa yace " Gwara a tafi haka " momma dake kallonsa ta ta'be baki " zan baka mamaki imran kada Ka shiga hankalinka ".

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now