"Ya naga kamar baka yi farin cikin ganinmu ba? Cewa nayi bari muzo mu kwashi gaisuwa gurin Babban Yaya kafin mu wuce." Kicin-kicin Imran yayi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi masa don cin fuska ya aure masa mata sannan ya zo da ita gidansa wai sun zo sa albarka, ya juya tamkar ya datse gidansa sai dai ya fasa.
Jikin Shatu a sanyaye ta bi bayan Ammar tana Mamakin rashin mutuncinsa, idan banda neman magana mai ya aikeshi aikata hakan.
Zama suka yi a parlourn kowa fuskarsa babu annuri idan ka d'auke Ammar da ya ke ta sakin murmushi akai-akai. "Bros doguwar tafiya fa muka sha, ba wani d'an abinda za'a bamu mu sha? Ga amarya na tabbatar yunwa ta ke ji."
Ji Yayi kamar ya tashi ya rufeshi da duka amma sai ya matse ya ce "Ba'kon da ya sanar da zuwansa shi ake tarba da kayan motsa baki, ba wanda ya fad'o bagatatan ba musamman wanda ba gayyatar sa aka yi ba." Ammar murmushi ya saki kafin ya ce "Idan kuma amarya na kawo fa? Kasan dai akwai tukuicin siyan baki? Don haka ga Amaryarka nan na kawo maka sai ka bani kud'in siyan baki."
Daga Imran har Shatu wata iriyar zabura suka yi, suna kallon Ammar da ya ke ta sakar musu murmushi ya ce "Zahirin magana kenan, Ayshatu matarka ce da kai aka d'aura mata aure a karo na biyu ba dani ba. Ina fatan ubangiji ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali mai d'orewa."
Cikin wani irin shock Imran ya mi'ke ya isa wajensa ji kawai ya yi ya rungumeshi yana fad'in "Ba na son wasa Ammar har waya na yiwa su khalil wajen d'aurin auren suka tabbatar min da kai aka d'aura, kuma na ga iv d'in auren." Murmushi Ammar ya yi "Ba da taka Ayshatun aka d'aura min aure ba da tawa Ayshatun aka d'aura min aure."
Shatu cikin tsananin mamaki ta ke dubansa tare da wata irin kunyarsa da nadama akan rashin mutuncin da ta aikata akan ance shi ta aura ashe ba shi bane yanzu da wani ido zata dubeshi.
"How comes? Komai ya juye haka don Allah bani labari ya aka yi Mommah ta janye furucinta. Ta kuma ha'kura ta yafe min?" Imran ya fad'a hannayensa cikin na Ammar, da ya gyara zama yana kallonsa ya ce labarin da tsawo amma dole in gaya maka ko ka barni na huta jibi na ke son juyawa in d'auke amaryata zuwa Qatar nima.
——————————————————
Tun bayan da ka saki Shatu hankalina ya tashi musamman da naga Mommah a cikin wani yanayi, hakan ya sa dole na amince da shawarar da zuciyata ta ke bani na son sharewa Mommah hawaye daga takaicin da ka cusa mata, direct na furta mata ina son auren Shatu idan ta gama idda, duk da ina da tawa Ayshan da na ke masifar so ba kuma wata bace illa wannan Ayshan da na aura wato Mubeena. Na amince a raina zan had'asu su biyu na aura lokaci guda. Duk da dai ban ta'ba son Shatu soyayyar aure ba.
Na lura hakan yasa Mommah cikin farinciki sosai da har ta gaza 'boyewa sai da ta bayyana.
Kwatsam muna shirin Shatu ta gama idda a fara shirin aure, sai ga Shatu da ciki, hakan yasa direct lokaci guda na sanar da Mommah na janye maganar auran Shatu don ba zan iya auren uwar yaranka ba alhali kana raye mai zan ce da yaranka idan suka girma suka tuhumemu da wannan kwamacalar? Mommah ta amince da uzurina don ita da kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bace kuma tana tsoron haddasa gaba a tsakaninmu. Tun a lokacin muka fara neman hanyar da zamu daidaita ku koma, sai dai mun fahimci matsala ta wajenka saboda baka zo ba, sannan da ta haihu ma ka 'ki zuwa, ni na ro'ki Mommah kada ta yi fushi da kai ta saka a Addu'a nima kuma zan dage da yi maka addu'a don tabbas na lura lamarinka da saka hannu.
Lokacin da ka dawo na hango soyayyar Shatu sosai a ranka a take na ro'ki Mommah ta amince a mayar muku da aurenku.
Mommah ta ce Ammar ban 'ki ta taka ba amma ba yanzu zan mayar da aurensu ba har sai Imran ya shiga taitayinsa ka cigaba kuma da nunawa kana sonta kada ka bari kowa ya fahimci ba soyayya kuke ba. A take na amince da shawarar Mommah, ban gayawa kowa ba har sai lokacin da naga Dahda ya birkice akan lallai sai an mayar da aurenku, sannan na gaya masa na kuma tsara masa plan d'in yace zai nema maka auren 'yar abokinsa wacce ba kowa bace illa Ayshatu na. To kaji abinda ya faru, duk da na ta'kaita maka, yanzu dai a bani abinci don kuwa yunwa na ke ji."Imran da hawayen farin ciki ya gauraye fuskarsa tuni ya sake rungumw Ammar yana sakin kuka, kukan cikar burinsa a lokacin da gwiwarsa ta karye ya d'ebe haso da samuwar rabin rayuwarsa wato Shatu, yaji tamkar ya mi'ke ya rungumeta tsam a jikinsa amma ba Zai iya ba a gaban idon Ammar sai dai tabbas yau shi kad'ai ya san kalar soyayyar da zai nuna mata.
Da sauri ya mi'ke yana kallon Ammar "Ta shi muje eatery ka ci abinci sai muyiwa madam take away."
Ya fad'a yana jifan Shatu da wani sihirtaccen kallo da murmushi a bakinsa. Kunya ce ta kamata ta yi saurin sunkuyar da kai. Hakan da ta yi shi yasa ya ji ba zai iya tafiya ba ba tare da ya sata a jikinsa bugun zuciyarsu ya had'u waje d'aya don haka ya kalli Ammar da ya mi'ke ya ce "Please ina zuwa bari na raka ta d'akinta tukun ta samu ko wanka ta yi kafin mu dawo naga kamar she looks so tired" Ammar dai murmushi ya saki yana d'aga kansa.Shatu ta mi'ke ta bi bayan Imran wani farinciki yana huda duka sassan jikinta, da zuciyarta kai har ma da 'bargo.
Suna shiga d'akin ya juyo yana kallonta idanunsa na lullumshewa na zallar fitina hakan da ta gani ya tuna mata first night d'insu da sauri ta sunkuyar da kai, shi kuwa saurin jawota ya yi ya had'e jikinsu yana sakin wata ajiyar zuciya da ta tafiyar masa da duk wani 'bacin rai da ya taru ya dun'kule masa a ma'koshi, ashe da gaske ne ba'kin ciki na taruwa a zuciya.
Ita kanta Shatu sakin ajiyar zuciyar take ya d'ago idanunta yana 'karewa cikin 'kwayar idanunta kallo da wani kyakykyawan smile da ni kaina ban ta'ba ganin Imran yayi shi ba. Murya can 'kasa ya ce "Ji na ke fa tamkar na had'iye ki? Ban ta'ba tunanin zuwan wannan ranar ba, ke fa ya kika ji?" Ya fad'a yana jan karan hancinta. Murmushi kawai ta saki ta ce "Kaje Yaya Ammar fa jiranka ya ke." Ya ri'ke kansa cikin fad'in "Ouch ni na manta dashi ma, ya zama dole na kuma yau na faranta masa, kamar yarda ya faranta min da abinda tunda na ke a rayuwata ban ta'ba ganin abinda na so sama dashi ba. Sauri zan yi in sallameshi in dawo yau kwana zan yi muna hira bayan mun yi addu'ar godiya ga Allah." Yana fad'in haka ya fita da sauri har yanayi kamar zai fad'in garin juyowa yana kallonta.
Murmushi ta saki cikin tarin farin ciki ta isa mudubi tana 'karewa kanta kallo ta tabbata dai MATAR IMRAN. Samun kanta kawai ta yi da dur'kusawa ta kai goshinta a 'kasa. Ta dad'e tana addu'a. Sannan ta d'ago tana dariya a hankali ta furta yanzu wasan zai fara kada ka yi tunanin ka sameni a 'bagas bayan tarin wula'kancin da ka yi min duka sai na fanshe kafin na sakar maka jikina ka yi yarda kake so dashi, sai ka amsa laifinka sai na jigata ka son raina sai kuma na nuna maka Shatun yanzu Aysha ce Ba Shatun Mommah ba........
Saduwar alheri!
Love you lodi-lodi
Jikar Nashe.