*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-25Dada ta masa kallon she'ke'ke kafin ta furta "Lafiya tana gidan ubanka Manga,tunda nan ban ga ana zaman lafiyar ba, ba ma wannan , mai kake nufi da ka barmu muke barci she'ke'ke kamar shi aka kawo mu muyi ko siyan baki baka zo ba,balle ka ja amarya ku tafi turakarka." Fuska ya d'aure sosai yana kallon Shatu yace "Ba yanzu na shirya kar'bar aurenta ba duk san da na shirya zan zo siyan bakin yanzu dai ku tafi don Allah." Dada salati ta saka tana fad'in "Ni jikar fad'imatu wallahi Dijah dai ba tayi sa'ar haifoka ba, wallahi shashasha ta haifa idan ban da dolo waye zai zubar da wannan indiyar dajin ya kama mai suffar turawa,mace a 'kanjame to ai shikkenan ke wuce muje shi yasa mai za'a yi da auren cushe." Fuska a d'aure Shatu tace "Ai sai da nace miki kar muzo kika 'ki." "Ki wuce nace muje ai wallahi yayi da 'yar halak Moddibo uban Dijah ya wula'kanta bani ba da na haife kakansa shi kuma ya haifi uban Dijah, ita kuma ta haifo mana jaraba." Bai yi magana ba ya mayar da 'kofa ya rufe yana jin zuciyarsa na sake tsanar auren alamar aikin su Zainab ya fara ci.
Suna komawa d'aki,Shatu ta saka masifa tana jan pillow zata mayar da kai ta kwanta, Dada ta kwad'a mata duka "Tashi shashasha wannan mijin naki sai kin dage masa da addu'a da alama mutanen 'boye sun shafeshi. Nima nan yau ba zan runtsa ba,yarda ya wula'kantamu d'in nan alfarmar manzo sai yazo yana binki." Shatu mi'kewa tayi ta shiga toilet d'in don ta tuna a nasihun Mommah har da sallahr dare da tace ta ri'keta gam-gam itace makamin 'kare dangi.
Da sassafe wayar Mommah ce ta tashe shi, lokacin bai fi 30mints da komawa barci ba,idon sa a rufe ya jawo wayar had'e da sata a kunnensa. Cikin muryar barci yace "Hello" Mommah tace "kana jina Shatu ta shirya ka kaita school kada tayi late." Daga haka ta kashe Imran ya mi'ke zaune yana dafe kansa a ransa yace "Kai oh my God wannan Shatu wannan Shatu wallahi Mommah ko don haka dole na koma turkey gurin harkar company na dama can nafi wayo ba sai an ganni ba balle a d'ora min wata hidimar Shatu."
Shaheedah ta mi'ke tana kallonsa, kafin ta yi tsaki ta furta "Wai lafiya naji kana ta magana kai kad'ai?" Mi'kewa yayi ya fice yana ce mata "Am coming."Yana murd'a 'kofar bedroom d'in ya jita a bud'e, da sauri ya shiga ciki, idanunsa akan Shatu da take barci, santala-santalan cinyoyinta farare sol a waje, ya saka hannu ya d'aka mata duka a cinyarta. Da sauri Shatu ta mi'ke tana murtsika idanunta, ta ware idonta a kansa fuska a had'e tace "Lafiya?" Ya girgiza kai "Ni kike tambaya lafiya? Ki tashi ki wuce ki yi shirin school kafin in murtsike bakinki, kuma daga yau ki san yarda zaki dinga tashin kanki ki tafi school ba zan juri tashinki ba." Daga haka yasa kai ya fice. Tilas Shatu ta mi'ke ta shige toilet, kafin tayi wankan sai da ta and wanke toilet d'in tas kamar yarda Mommah ta ja kunnenta. Ta kuma fito ta koma parlour ta gyara duk yarda yake son gyara. Duk da Mommah tace zata saka a samo mata mai aiki. Ta kunna burnerr turaren wuta gidan gaba d'aya ya d'auki 'kamshi. A kitchen ake yinta don ba abinda ta iya dafawa sai indomie ita d'in ma ba wani 'kwarewa tayi ba. Haka dai ta zauna ta cacca'ba musu indomien sai dai tayi ruwa jingim.
Da sauri ta fito taje tayi wankan,ta zura uniform d'inta, sannan ta tashi Dada ta sanar mata ta tafi school. Dada ta zaro ido "Makaranta kuma? Kai Allah wadaran naka ya lalace,jiya a kawo ki gidan miji yau ki tafi makaranta, sai kace makarantar ganin Annabi." Shatu dai mi'kewa tayi da sauri ta fice, tana jin Dadan na ta mita ita kad'ai.
Turus tayi a kitchen bayan ta bud'e indomie d'in taga ta ca'be kamar me? Haka dole ta fice daga kitchen d'in kamar tayi kuka,saboda bala'in yunwar da taje ji.A parlourn ta ta gan shi zaune yana danna waya,sai zabga 'kamshin turarensa yake. Ta tsaya tana matsar 'kwalla, jin idanu a kansa ya tabbatar ta shigo parlourn ba tare da ya kalleta ba yace "wuce muje." Murya na rawa tace "Yunwa fa nake ji." A harzu'ke ya d'ago yana kallonta,sai kuma yaja tsaki " Maza ki mayar dani abinci ki ci." Yayi tsaki ya fice don dole ta d'au school bag d'inta ta bi shi.