*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-18ELEGANT ONLINE WRITERS
Sosai take hawayen saboda kalaman Imran sun 'bata mata rai. Momma ta jata jikinta da sauri tana jifan Imran d'in da harara "fice min daga nan tunda burinka ya cika ka saka shatu kuka yo itama su'butar baki Tayi idan banda haka mai za tayi da kai a haife ka haifeta tunda ka ninka shekarunta." Ficewa yayi ba tare da yace komai ba Allah ya tsari gatari da saran shuka" ya raya a zuciyarsa.
Ana gobe kamu masu tafiya abuja suka dinga dandazon tafiya dangin mommah dai ba suje ba a cewarsu bikin namiji suke zo ba ruwansu da dangin mace sun san ma kun sunje wula'kanci zasu sha,gida ya d'ad'e ba kowa daga mommah sai danginta suke Ta tsara yarda bikinsu zai kasance.Juma'a ne d'aurin aure don haka ranar asabar za suyi dinner lahadi suyi bud'ar kai ango ma alhamis d'in zasu wuce da abokansa da suka zo daga wurare da dama wasu ma ba 'yan 'kasar nan bane.
Don haka yau part d'insu na samarin gidan a cike yake sosai don ma babban parlour ne sai bedrooms guda hud'u a ciki don gidan dahda ba dai girma ba gari guda ne. Tana zaune a gefen dada tsohuwa tana shan dariyar labarin da dadan take bata na Imran da yake yaro yana tsoron saniya ita kuwa sai dariya take su antynta nahna suna zaune suna cire mata jan lallen da akayi mata na salatip ba 'karamin kyau yayi ba ya haskaka kyakykyawar 'kafarta ta.tana mi'kewa mommah Ta shigo parlourn tana dubanta daga ita sai wata riga da tsayinta yaje mata gwiwa sai skinny black pant ajikinta gashinta kuwa an tufke mata shi guda biyu ya sauka har fin gefen Kafad'unta duk da ba kwalliya tayi ba tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu"maza jeki ki kira wo min yayanku Imran" mommah tace tana zama a kujera had'e da ri'ke kai alamar a gajiye take sosai. Ba tare da jin komai ba shatu ta fice tana jin dada na 'kwala mata kira amma tayi shiru dada tayi tsaki "kaji y'ar banzan yarinya a haka zata fita kai ba kallabi ke kuma dijah kina kallonta ta fara fa 'kirgar dangi ita ko ta ido bata dashi ne? 'yar nan" mommah murmushi kawai tayi "To dada nawa shatun take?" Dada ta girgiza kai "nawa take? Wannan d'irkekiyar budurwar ake kira nawa take yarinya ta fara 'kirgamu yanzu haka ma ta fara al'ada" mommah ta girgiza kai "Bata fara ba wallahi dada ai da ta fara nima ba zan bari ta dinga zama haka ba na san shari'a ta hau kanta" "zancen banza shari'a kuma ta yaushe tunda ga abubuwa nan sun fara bayyana" ita dai mommah shiru tayi tana jin dada na ta masifa.
Ta dad'e tsaye tana knocking a 'kofar ba a bud'e ba
ga hayaniya ta cika gurin,ba tare da tunanin komai ba ta tura 'kofar ta shiga. Sai kuma sannan tayi turus ganin maza duk kunya ta lullu'beta gashi duk sun zuba mata ido gaba d'aya ta diririce,idonta akan Imran da yake zabga mata harara cikin 'bacin rai yace "fice daga nan kafin inzo nan shashasha kawai ko kunya ba kya ji wai ma mai kika zo yi?" Idonta ya kawo raurau za tayi kuka haka kawai taji tana son yin kuka ganin kallon da suke binta dashi tana ji masu fad'ar masha Allah na fad'a masu cewa wow na fad'a. Da sauri ta fara wasa da hannunta kafin tace"mommah ce ke kiranka" tana fad'a ta fita a guje ashe shatu an fara girma ana tsoron maza tana ji suka tuntsire da dariya d'aya daga abokansa yace "Imran manga wannan wacece?" Kallo d'aya yayi masa yace "Sister"duk ido suka zuba masa abdul yace "Na zata baku da sister mace koma dai menene gaskiya babyn ta had'u ina ciki." Sai aka d'au hayaniya guri kowa yana fadin bai isaba suma suna so Aliyu da yafi kowa serious ya dafa shi "Don Allah Imran ya kuke da yarinyar nan ni dai na san ku biyu ne kacal a gidannan" mi'kewa yayi yana gyara wristwatch d'insa fuska a d'aure yace"cousin" daga haka ya fice amsa kiran mommah a zuciyarsa ya furta "mayun mata abin nasu kuma har da 'kwailaye"yana jin su suna sake yaba surarta Ali yana cewa yarinyarnan idan ta girma wallahi za'a ja kaya musamman idan ta samu kula ni wallahi ya dawo ko yanzu ya raka ni wajen mommah na nemi aurenta. Imran murmushi kawai yake yana tafiya don ya san basu san wacece shatu ba.
Tana jikin mommah a kanainaye kamar ta shige ciki ya lura tana da son jiki kamr mage.mommah na ganinsa tace "Yauwa Imran abincinku nace ya za'a yi dashi?" "Momma wannan yarinyar me yasa take fita haka kai ba tie" mommah harara ta watsa masa "Ga maganar da nake maka kana min wata banzar magana" dada Ta gyara zama "a to kai ma dai ka fad'a kai da yake kafi uwar taka hankali nayi magana ance yarinya ce wai wannan baligar ce yarinya?shiga sai kace a garin 'kedarai to ni da ban isa ba ance yarinyace ai 'kafata 'kafar yarinyar nan don na lura uwarka lalata ta za tayi ta sangarta 'ya kullum tana cinya kamar mai shan mama to ba dani ba." Hajiya mama dai sai murmushi take.Imran ya shige kitchen yana cewa "ki rabu dasu dada gashi nan ai samari sun fara kawo mata farmaki ba sun ganta da shigar banza ba."Dada ta zabga salati "kai Imrana ka rantse da Allah mhmnn to dai wallahi Allah ya kyauta lamarin uwarka ni kuwa 'kafata 'kafar bararo wallahi"dariya yayi yana shigewa kitchen a zuciyarsa yace Ai gwara ki d'auketa wallahi dada.Ko da ya koma zancen dai Ali ya ya tayar masa tsaki yayi "ku dai Allah ya shiryeku duk 'yan matan garinnan ku rasa ta kulawa sai wannan 'kwailar" Abdul tsaki yayi "Ai wallahi Imran kayi ba'kar dabara ya za'a yi da wannan a gidanmu inje neman auran wata ba zaka zauna ka jira wannan d'in ka kiwatata kaje kana auren wata 'kemasashshiya zubin turawa ga zubin larabawa haba Alhaji wallahi ka cuci kanka." Imran ya masa wani duban banza"God forbid Allah ya kiyaye kai ka sanni ka san waye ni kuma ka san burina na auren matured wacce ta san ciwon kanta kuma mace mai tsafta ba kuma na san mace mai tsananin kyau saboda bana son ko wani rubbish ya dinga kai idonsa kan matata so wannan bata cikin layin matan da nake so mace mai kyau ai hatsarice." Gaba d'aya ta'be baki suka yi suna kallonsa su basu ta'ba jin mutum ma mai irin ra'ayinsa ba.Ali yace "Allah ya raba mu da auren mummuna mun fi son kyakykyawa ta shiga taro."Imran tsaki yayi "Allah ya kyauta sai ku shirya kar'bar ciwon hawan jini don ba abinda 'kananan yara zasu saka muku idan ba su saka muku hawan jini ba."
Ranar Alhamis da daddare su hajja suka dawo saboda ranar juma'a ne d'aurin aure kuma sun fi son su kar'bi amarya da kansu. Ko kallon arziki ba wanda yayiwa su mommah da suke zaune a general parlour suna tayi musu sannu da zuwa, a ciki suke amsawa Hajja zube a parlour ana Ta d'aga kai 'kafa d'aya kan d'aya tana 'karewa Hajiya mama kallon banza ita dole sai dai Ta nuna gidan d'anta ne. Hajiya mama da yake bata iya fad'a ba ta mi'ke tana kallon mommah da dada tace "Dada muje daga ciki ku barsu su huta."Dada ta girgiza kai "oh oh babu inda zani anan zan zauna ina kallon mai shige da fice to ina dalili zaki turani can ciki ban san mai duniya take ciki ba wanda yaga ba zai iya zama ba shi dai ya tafi amma dada kam zama daram"Hajiya mama ba tayi magana ba tayi shigewarta d'aki.dama su nahna basa nan sun tafi kar'bar d'inki tana ji hameedah na shewa tana cewa "Oh Hajja aure dai ya d'auru Allah yaso ba'a ruguza shi da surkullen fulani ba" Hajja ta masa "Da wallahi kuwa" Mommah tana jinsu ta shige kitchen ranta a 'bace tasa masu aiki suka kai musu abinci daga haka Ta shige part d'inta wajen Hajiya mama tana dialling call d'in dahda.
Da daddare kuwa ta sake jaddadawa dahda burinta Na son d'aura auren gaba d'aya a gobe "ka d'aura a can abujan kawai dangin Ubanta ba matsala bane daga baya ta kaini har garin nayi musu bayani duk da dai basu damu da ita ba da sun damu da ita ai da sun biyo sahu."Dahda yayi murmushi yana jan hannunta "Your wish is my command Dija na I do as you said." Murmushi tayi tana had'a goshinsu waje d'aya.
********RANA BATA 'KARYA******
Dandazon mutanene suka halarci d'aurin auren a babban masallacin Na garin Abuja, duk inda ka juya jama'a ce Imran fuskarsa d'auke da fara'a at last dai zai mallaki burin ransa shaheedah da ya dad'e yana mafarki a matsayin matarsa matured mai tsafta kuma 'yar gayu kuma 'yar 'kwalisa kamar yarda yake son matarsa ta kasance. Suna zaune shida abokansa suka ji an fara shelar za'a d'aura auren ayi shiri jama'a. Ai kuwa cikin yardar Allah aka samu ba'kuncin shiru mai shela bayan mintuna kad'an ya shela cewar an d'aura auren Imran da Haleemah shaheeda akan kud'in miliyan d'aya lakadan ba ajalan ba Alhamdulillah Imran ya fad'a a zuciyarsa Finally angon shaheedah inji abokansa sai kuma suka ji an sake d'aura auren Imran da Aysha mujittafa....... gaba d'aya abokansa suka waro ido suna kallonsa shi d'in ma kallonsu yake....