'Kirjinta ya cigaba da bugu, lokacin da ta ji ance Ayshatu ta angwance da mijinta Ammar......
Sosai zufa ta shiga keto mata ta ko ina bata ta'ba tsammanin Mommah ba zata janye furucinta ba. Wace irin uwace Mommah da ba zata iya yi musu afuwa ba?
Hawaye tuni ya wanke kwalliyar fuskarta tas, ta mi'ke da mugun gudu ta shige bedroom, dai-dai lokacin kuma angwayen suka danno kai, fuskokinsu tamkar auduga musamman fuskar Ammar da yake ta sakar murmushi na zallar farin ciki, tamkar wanda aka yiwa bushara da Aljannah. Zugar abokansu ce a bayansu duka suna baza babbar riga.
Shatu tana shiga d'aki ta yi wurgi da d'ankwalinta da duk wasu abubuwa da aka yi mata kwalliya dasu.
Sosai ta ke jin tsanar Ammar a zuciyarta, ta kuma ha'kkake a ranta ba zancen zaman lafiya tsakaninta da shi, tunda shi ya nace sai ya aureta idan banda haka ai da ya janye da Mommah da ba ta tilasta mata aurensa ba. Kuka ta ke yi sosai tamkar ranta zai fita.
Dai-dai lokacin da Mommah ta turo 'kofa ta shigo da niyyar ta sanar da ita ta shirya a yi hotuna, turus tayi ganin da tayi duk ta hargitse jikinta harta d'ankwalinta ta yi wurgi dashi, gashin kanta kuwa ta barbaza shi, kana ganinta zaka yi zaton mahaukaciya ce sabon Kamu. Mommah ta saka salati ta ce "Me zan gani haka ni khadijatu?" Jin Maganar Mommah ya sa ta ji zuciyarta ta sake hassala ta ji a ranta ko kallon Mommahn bata so ta yi, zahiri kamar ma Mommahn ta nunawa duniya ta fi son farin cikin Ammar fiye da nasu.
"Ba kya Jine? Ina yi miki magana kika yi kunnen uwar shegu dani?"
Tana hawayen ta d'ago idanunta a runtse ta ce "Bakomai"
Mommah ta ja tsaki "Allah yasa bakomai d'in ya zama bakoman, idan banda shashashanci duk kud'in da aka 'batar wajen yi miki kwalliya ya tashi a banza kenan ko hoton ba a yi ba kin shigo d'aki kina risgar kuka kamar wacce aka yiwa auren dole"
Da sauri ta runtse idonta, dama da Mommah abokiyar maganarta ce da direct zata ce "Me ye marabar wannan auren da na dole tunda ni dai ba a nemi amincewata ba da an nemi amincewata da direct zance gidan miji na zan koma, amma anzo an had'ani da wannan da ban ta'ba jin d'igon sonsa ba, wallahi sai yayi regretting aurena don duk wasu munanan halaye na sai na sake renew d'insu."
Mommah da ta gaji da kallonta ta yi tsaki ta ce "Idan ma auren ne ba kya so kin makaro don gobe jirgin asuba za ku bi zuwa Qatar idan kun koma makarantar ya dawo da ke, sai na ga kuma ya zaki yi shashashar banza ba ki san gata na yi miki ba." Ta fice tana ta mita kamar ta ari baki.
Shatu ta sake zunduma ihu jin wai gobe zasu wuce Qatar, ihun da ya janyo hankalin jama'ar da suke parlour suka bazamo cikin d'akin da tunanin ko ba lafiya ba? Ciki kuwa har da Ammar da ya kasance sahun gaba.
Turus suka yi ganin ta yi buzubuzu da gashinta ga hawaye a fuskarta sai kuka ta ke tana "Na shiga uku, ni ban ta'ba jin irin wannan ba." Kowa kuma sai ya yi turus jin maganganun da ta ke saki kamar bata cikin hankalinta.
Ammar ne ya 'karasa tsakiyar d'akin ransa a 'bace da maganganun da ta ke furtawa ya d'au mayafinta yana yafa mata zuciyarsa cike da tarin haushinta da tausayinta duk a lokaci d'aya ya ji dama yana da iko da ya furta mata abinda take so. Tsaki ta ja ganin mutanen sun cika mata d'aki ta shige toilet ta datse da key, tana furta munafukan banza duk a cikinku aka rasa wanda zai bawa Mommah shawara sai da komai ya lalace sannan zaku dinga jifana da kallon tausayi."
Mutane duk suka juya suna mamakin me yasa ta aikata hakan wasu ma har sun fara hasashen ko bata da hankali ko kuma tana da jinnu.
————————————-
A ranar aka sada amare da d'akunansu amaryar Imran kuwa nan gidan aka kawota kafin ya zo ya tafi da ita ko yayi mata visa ta tafi da kanta.
Gidajensu kam sun yi kyau sosai sun kuma yi tsari irin tsarin 'yan boko, sun sha nasiha da fad'a daga bakin 'yan uwa da
Abokan arxiki kafin su tafi kowacce a barta da halinta.