20

246 14 0
                                    

*🤍ME  ZAN YI DA ITA?*🤍

        NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-20

ELEGANT ONLINE WRITERS.....

"Babu wanda aurensa zai mutu saboda son zuciyarki,ashe abinda kike aikatawa kenan a gidan d'anki Hindatu duk abinda kike ciki labari yana zuwar min,kamar na san hakan zata faru nace a kawo ni nan d'in kafin na wuce gida na, gaskiya Hindatu kin bani mamaki kuma sam ba jinin y'ar uwata ce a jikinkiba ita d'in macece mai kara mai mutunci mai yakana da alkunya idan Banda ma zamani mai ya kawoki gidan d'anki saboda abin kunya kuma kizo ki saka matarsa a gaba da rashin mutunci saboda siyawa kai raini,to bakin ki ya mutu anan wajen,aure dai ya d'auru kuma ba mai warwareshi manga ya sanar dani komai,don mai ita ba zata yi iko da d'anta ba alhali kema da naki d'an kike iko babu wacce zaka saki a cikinsu duka matanka ne kuma ban amince da saki ba zancen banza zancen wofi wa yace maka ana sakin mace haka kawai,to kada in sake jin makamancin wannan zancen, duk abinda kuke ina zaune ina jinku dama don inga kamun ludayin kowa shi yasa nayi bakam a waje na zauna, to hindatu naji duk tijararki."sai a sannan dattijon arzikin yaja ajiyar numfashi ransa a matu'kar 'bace yana kallon hindatu (Hajja yau dai munji sunan hajja na gaskiya a bakin kawunta kawu sa'idu)Hajja tana shakkarsa sosai don duk dangi yanzu shine babba shine kuma mai fad'a aji, gashi dama mafad'aci ne ba'a kuma isa yace ga abinda za'ayi ba a canja ba, kaifi d'aya ne kuma wargi yake dai-dai 'kugun ko wani ja'iri. Parlourn shiru yayi kowa yana jin kawu yana ta fad'a Hajja zuciyarta sai tafasa take, tabbas kawu ya kawo mata cikas kuma sai taci uban manga da yaje ya sanar dashi. Kawu yayi fad'ansa son ransa sannan ya kalli Imran "Na jiyo gareka ko gaba naji magana makamancin ta rabuwa da za'bin uwarka sai naci mutuncinka,wa ya gaya maka ana jayayya da maganar uwa? Kada in sake jin haka ba and mamaki abinda ta hango kai baka hangoshi ba." Haka ya gama fad'ansa ya kuma ce gobe ana gama biki Hajja ta had'a karonta ta tafi kada kuma ya sake ganin 'kafarta a gidan d'anta ba da wani muhimmin daliliba.

Shatu kuwa tana can d'aki bata san budirin da ake ba, tana kwance saman bed d'in mommah da wayar mommah a hannunta tana buga game. Har sai da anty nahna ta shigo murmushi fal fuskarta ta dafa shatun "Amaryar Imran." Shatu ta mi'ke zaune hankalinta na kan game tace "mai tayi amaryar tasa? Nahna tsaki tayi tace "akwai wata amaryar bayan ke." Sam bata d'au zancen serious ba don ko a mafarki bata ta'ba sawa zuciyarta Imran ba balle har tayi tunanin zama amaryarsa tsokana ce dai irin ta Anty Nahna ina ita ina Imran da ko inuwa guda basa had'awa. Shigowar mommah da fad'a da mitar Hajiya mama ne yasa su kayi shiru da zancen fad'a take tana 'karawa "Haba addarsu ai wallahi kin yi wauta ta ina aka ta'ba wasa da aure anyi magana kince wai nuna musu iko za kiyi to ikon me ki jefa yara cikin matsala, yaushe shatu ta isa aure fisabilillahi nawa shatun take? Ai shirme dai kinyi shi wallahi kuma ina jiye miki fad'an Babanku kin saka yrinya a matsala ke baki fita daga ciki ba kin jefa y'arki a ciki wannan dangin mijinnaki da ba kirki bane dasu." Shatu dai mi'kewa tayi daga kwancen da take tana kallonsu d'aya bayan d'aya wai mai take ji ne? Ita dai shatu aka d'aurawa aure da Imran da take ji duk duniya ba wanda ya kaishi tsanar ta ina ita ina Imran d'an gayu mai ji da kansa? Muryar Dada ce ta dawo da shatu duniyar su mommah tana jin Dada ta fara masifa "Ah to ni ban ga laifin dijah ba ai maganin shege d'an banza yanzu Na san ashe Dijah jini na ta d'auko, ba naki ba solo'biyo da abinda kika sani sai ha'kuri,yo akan me? Wani shegen yayi mata na'kudar d'an sun d'auki wata 'kanjamammiyar mata sun bashi, bayan a haka an zauna ana yi mata isa da iko da fankamar banza sai kace a kansu aka fara arziki ko da yake ba'ko a arziki shi yake nuna shi wani ne. Yanzu kuwa da tayi musu haka ai sa san annabi ya faku, to ina dalili idan ban da tsiya ma ace 'yar kishiyarka d'anka zai aura ban ta'ba ganin wannan iskancin ba sai a dangin mijin dijah.ai gasu can dai wancan jarababben kawunnasu ya kashe bakin tsanya yayi min dai-dai wallahi." Hajiya mama shiru kawai tayi tana jin fad'an Dada.ita kuwa shatu tayi zugum ba tare da ta san mai 'kwa'kwalwarta zata tuna ba.wai ita shatu 'yar 'karamar nan aka yiwa aure? Lura da haka da mommah tayi yasa ta isa bakin gadon ta kamata,rungumeta tayi a jikinta tana shafa bayanta "kwantar da hankalinki daughter na ba yanzu zaki tare ba sai kin girma kin gama karatu sannan zaki tare kin ga ko ai da dad'ewa." Sai sannan shatu ta saki ajiyar zuciya tana dariya ta rungume mommah. Gaba d'aya d'akin murmushi su kayi banda Dada da ta 'bata fuska cikin masifa tace "zancen wofi kenan kaji shashancin banza shikkenan ita kuma sai ta 'kare a gantale a titi to ba zai yiwuba yanzun zata tare mu da akayi mana aure yaushe muka kaita yarinya ta fara 'kirgar dangi sannan ace wani sai ta girma yo girma na me? Kin san da hakan kika d'aura mata aure, to ban amince ba a sada ta da d'akin mijin ta cikin mutunci da kima wallahi kafin ayi abin kunya yayi mata ciki a gadonki." Gaba d'aya d'akin kunya ce ta kama su wannan sakin baki na Dada, murya can 'kasa mommah tace "To shikkenan zata tare amma ai sai an gama shirya mata abinda za'a kaita d'aki dashi ko?" Dada ta mi'ke tana fad'in "To shine zance amma kya ajiye budurwa zangangan a gaba kice wani sai ta girma,girmo nace ba girma ba." ficewa tayi tana 'kananun mita. Hajiya mama fuska ba walwala tace "Ba dai maganar Dada zaki bi ba na tariya ban amince da wannan shashancin ba ki bari ta girma ta san ciwon kanta tukunna." Mommah d'aga mata kai tayi kafin tace "ko d'aya Na dai amsa mata ne don mu huta da mita kafin ta tara mana gayyar jama'a ba wani tarewa da zata yi sai ta gama makaranta tsaf tukun." Hafsa tace "wannan shine dai-dai wallahi Addarmu gwara ma da kika yi maganin mutanen can haba ikon yayi yawa."haka dai aka yi ta tattauna zancen har Ammar da Hisham suka shigo hundred percent sun goyi bayan mommah.
Shi kuwa ango yana can zuciyarsa tamkar ta fashe bak'in ciki ya gama cika shi.yana ji abokansa suna ta tambayarsa wacece Amaryarsa ta biyu amma ya kasa basu amsa,sun lura ransa a matu'kar 'bace yake don haka suka kyaleshi suna cigaba da shirin dinner shi kuwa ko kallonsu bai yi ba balle ya nuna alamar shirin.

A can 'bangaren Amarya an sha ba'kin gumurzu kafin ta ha'kura ta saduda bayan mahaifiyarta ta tabbatar mata ko za tayi yawo tsirara sai ta raba auren Imran da wannan mai kama da bararojin.hakan yasa ta share hawayenta ta fara shirin dinner don mai kwalliya Nashe glam wato khadija Nashe tazo za tayi mata, kafin a fara kuwa tace bari ta je ta ga angon.

Cikin part d'insu ta shiga duk da abokansa da suke zaune dam'kar a parlourn bai hana ta kutsa kai ba, ba tare da wani shakka ba tace musu "sannunku" Gaba d'aya suka amsa ta dubi Ali da shi suka fi d'an sabawa tace Imran fa?nuna mata cikin bedroom yayi yana sakin murmushi a zuciyarsa yake tunanin ko mai Imran zai yi da wannan ai shi cetonsa aka yi da aka bashi wata duk da waccen d'in ma basu san wacece ba. Suna kallo ta shige uwar d'aka ba tare da shakka ko kunya ba Amarya ta kawo kanta kenan sabon salo abdul ya fad'a yana dariyar sha'kiyanci.
Tana shiga ta tarar dashi kwance a rigingine saman carpet idonsa a lumshe da alama dai ba barci yake ba,zama tayi a gefensa tana jan yatsun hannunsa, a hankali ya bud'e idonsa yana ganinta ya d'an saki murmushi tare da mi'kewa zaune ya jawo ta yayi mata kyakykyawar runguma ita ma 'kan'kameshi tayi kawai ta saki kuka kasa ce mata komai yayi shima yana sakin ajiyar zuciyar suka lula wata duniyar ranar da yake jira ga shi ta zo masa a baibai ranar da shaheedah zata zama mallakinsa. Sun dad'e a wani yanayi na romancing juna kafin ta janye jikinta a hankali bata shirya kar'barsa a wannan lokacin ba kamar yarda antyn ta ta ja mata kunne sai komai ya kammala sannan zata amince dashi akwai aikin da tasa malaminta yayi mata.wani kallo yayi mata "why shaheedah?" Murmushi ta sakar masa "ka tashi kayi shirin dinner mu tafi wani dalili can ba zai ruguza mana farin cikin da muka dad'e muna arranging ba,an dai riga an gama cutar mu kuma wallahi bana jin zan iya zaman kishi da kowacce mace akan ka don haka kayi shirin rabuwa da ita wallahi ta kowani hali ma" murmushi ya sakar mata yana shafa kumatunta "ki sha kuruminki my lovely wife ni na san abinda nake shirya mana bana son ki 'kara d'aga hankalinki aure dai an d'aura amma ba wanda zai saka ni dole nayi acecpting d'inta as a wife kallon arziki ma ba yi mata zanyi ba."
Murmushi ta saki murna fal ran ta tace "yauwa tnx so much dearie ai ko cewa aka yi ta tare ka amince sai ta zame mana house girl ko?" 'Daga kai yayi yana shafa kanta murya can 'kasa tace "Amma don Allah kada tace dinner yau bana son ganinta wallahi raina 'baci yake." "Tohm shikkenan ba zata ba zan san yarda zan yi da ita yanzu jeki a fara shirya min ke ki fito kamar 'yar tsana." Tana dariya ta mi'ke Ta fice daga d'akin. Gaba d'aya suka zuba mata ido barin Ammar da Hisham da basu san tana ciki ba. ko kallonsu ba tayi ba ta fice da Sauri.

Ali ya kalli Ammar yana dariya "kun ga abin mamaki ko? Amaren yanzu basu da ta ido they are shameless yanzu fa ita ta kawo kanta wajen mijin ko da yake dama ya fi son irinsu matured in ji shi da fad'a" gaba d'aya suka tuntsire da dariya. Ammar yace "Da kun ga wacce aka aura masa da kun san ba 'karamin gata aka yi masa ba." Ali yace "yauwa wa aka aura masa please?" Hisham yace "shatu ce fa." Gaba d'aya suka zaro ido Ali ya tuntsire da dariya "wai wannan yarinyar mai kama da larabawa ita ce yake tuejewar baya so?cab ni fa nan har ina cewa ina ciki to ai shi ba 'karamin gata aka yi masa ba." fitowar Imran daga d'aki ce yasa su kayi tsit suna kallonsa fuskarsa a tamke kamar tunda aka halicceshi bai ta'ba dariya ba. harararsu yayi ya fice daga d'akin yana jin suna tuntsira masa dariya.

Mutane ne 'yan biki a zaune a parlourn haushi ya kama shi hakan yasa yace saratu mai aiki ta kira masa shatu, ta amsa tana 'kunshe dariyar da take cin ta don duk sun san labarin, ta shige a d'akin mommah ta samu shatu tana dariya tace "shatun momma kizo in ji Babban yaya." Sak shatu tayi tana kallon jama'ar d'akin..

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now