9

218 12 0
                                    

*🤍ME  ZAN YI DA ITA?*🤍

        NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-9

ELEGANT ONLINE WRITERS........

Tana shiga d'akinta hawaye ya fara zubo mata, Tunani take sosai a zuciyarta so take ta hango laifin da takewa dangin mijinta suka tsaneta har haka, mai tayi musu? Shine abinda take tunani a zuciyarta, har ga Allah bata nufin kowa da sharri rayuwarta take free ba tare da kowa a ranta ba amma sun bi sun tsaneta.

A gefen gadon ta zauna, shatu data gefe jikinta yayi sanyi ganin mommah na hawaye, taji duk duniya ta tsani waccan Almasifatun tsohuwar a hankali ta zauna jikin mommah itama ta saki nata kukayi. Momma dafa kanta kawai tayi alamar rarrashi. Daidai lokacin Ammar da Imran suka shigo d'akin jikinsu a sanyaye suka zauna kan cushion chair d'in da take gefe fuskarsu sam ba walwala musamman ammar, sam baya son abinda zai saka mahaifiyarsa a 'bacin rai. Ammar yayi'kasa da muryarsa " Momma kiyi hakuri komai lokacine, kuma wata rana sai labari." Girgiza kai tayi " Na kai ma'kura Ammar iya ha'kurin da zan iya kenan kun san iya lokacin da nake'kunsar ba'kin cikin hajja tun ranar da na kwana d'aya a gidannan duk a dalilin mahaifinku bai auri za'binta ba, kuma ba kowa bace za'bin nata sai wannan matar da sai da ta san yarda tayi yanzu ta auro masa ita, to lamarin ya isa zan tattara in tafi amma ba zan zauna ba'kin ciki ya kashe ni ba just like bani da iyaye, gidan ubanku ne ku zauna, bare shi gashi nan zasu aura masa wacce suke so, tun yaushe nake jan kunmensa ya rabu da yarinyarnan ya'ki, saboda kawai kyanta da kwalliyarsa yana rud'arta to yaje ya aureta amma ka san Allah ba hannuna a cikin lamarin aurenka, wanda dama don a gasa min ba'kin ciki aka'kir'kiresa."
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta mi'ke ta shiga had'a kayanta, Ammar ya ri'ke akwatin " please mommah kada kiyi abinda baki ta'ba yi ba da yarintarki balle da girmanki please ki rabu dasu,ko mu kad'ai zamu iya share miki hawaye, kuma wallahi at this point sunyi na'karshe, kaima yaya Imran don Allah kayi hakuri ka kyale musu'yarsu ko don kwanciyar hankalin Mommah " wani kallo Imran ya zuba masa " meye laifin shaheeda da zan rabu da ita, ko kana tunanin a bayansu take? To kullum maganar ta tana jin haushin abinda suke wa mommah." Wani kallo momma ta wurga masa sai kuma tayi kwafa " mhmn ba dai shaheeda bace Imran ka aureta ban hanaka ba, tunda lokacin da na hanakan ai baka ji ba, sai dai bahaushe yace wanda bai ji bari ba.... kai kuma Ammar kada ka sake masa magana idan ta nice ma barin gidan zanyi ba sai na zauna zanga kayan takaici ba ." Imran shiru yayi yana sake zabgawa Ammar harara sai kuma yayi kwafa ya fice. Mommah tabi bayansa da kallo tana masa addu'ar shiriya a zuciyarta ji take kamar ta rusa kuka gaba d'aya sun cusawa Imran soyayyar shaheeda ta 'karfi da yaji da yaudara da komai. " ka rabu dashi Ammar tsakaninka dashi Addu'a ya riga yayi nisa a soyayyar shaheeda ba zai ta'ba ganin aibunta ba." Ammar ji yayi ransa ya sake'baci idan dai da shine ko da gold aka'kera shahida sai ya ha'kura aurenta balle shi dai ban da kyan fuska bai ga mai ya gani tare da shahidan ba tana tafiya kamar sillan kara,sai iyayi da kwainane. Shatu dai tana gefe tana kallon ikon Allah, takaicin Imran kuwa ya gama cikata. Har so take taga wacece wannan da ya fi sonta akan'bacin ran mahaifiyarsa. Ammar ya cigaba da bawa mommah ha'kuri ganin ta'ki ha'kura yasa ya fita wajen bayan ya danna kiran hajiya mama mahaifiyar mommah a cikin wayarsa. Basu san me yace ba sun ga dai ya dawo da sauri ya mi'kawa mommahn wayar, ya wurga masa harara don ta san'kara ya kai ta wajen hajiya maman. Tana sallama hajiya mama ta shiga fad'a tuni mommah ta sa kuka ta fara bata labari. Hajiya mama cikin zafi ta katseta " kishiya saboda kishiya zaki bar gidanki akan ki aka fara kishiya?da girman ki da komai kike neman zubar da mutuncin ki to ahir ki kiyayeni kina shirin auren da'kanne da 'ya'ya, nan gaba su kuma idan sunyi wa zai musu fad'a? To ki saurareni da kyau ki mayar da akwatinnan kafin ma su gani su ji dad'i gobe insha Allah'kannenki sun zo hutu daga turkey zasu zo kanon suyi miki hutu hisham ma dama yana ta son zuwa wajen mutuminsa Ammar. Ina shatu?" Momma ta mi'kawa shatu wayar " maza ki masa hajia mama ce ". Shatu ta kar'bi wayar cikin rashin sabo ta fara gaisheta " lafiya lau shatu ya ba'kunta? Gobe zaki ga aunties d'inki suna ta son ganinki." Murmushi shatu kawai tayi saboda ba 'yan hayaniyar a kanta. Hajiya mama ta sake cewa " Ba dai matsala dai ko?" Shatu ta girgiza kai " Bakomai mama" To masha Allah sai kin ga sa'ko " hajiya mama ta fad'a tana kshe wayar. A hankali shatu ta mi'ka wa Ammar waya, ganin yarda jikinta yayi sanyi yasa Ammar ya shiga janta da wasa" shatun mommah'kalau kuwa yau na ganki jiki ya mutu? Ko don ki had'u da Babarki a masifa " harararsa shatu tayi " Ai wallahi ba tsoronta naji ba, don dai kawai mommah ta hana ne amma wallahi da tuni ta d'ebi kashinta a hannu yo Allah na tuba wannan  'karamar alhakin, ka san Allah da 'kauyenmu ne yau sai na saka yara sun mata kid'an Atire." Ammar mai zaiyi banda dariya mommah kuwa bud'e ido tayi tana kallon shatu yarda take yi da baki " To shatu ba 'kauyenku bane kuma anan idan kayi wa wanda ya girme ka rashin kunya kulleka ake a gidan yara don haka be careful." Ammar ya fad'a fuskarsa d'auke da alamar tsoratarwa. Shatu ta kya'be baki " Ai in dai ba kayi a fili ba sai mutum yayi ta bayan fage yarda za 'a gane ba." Ammar girgiza kai kawai yayi yace "Allah ya shiryeki shatu." " Tashi maza kije kiyi sallah Ayshata ai Na san kina jin maganata ba zaki jawo min abin fad'a ba ".murmushi tayi tana mi'kewa dad'in yabon da momma tayi mata da sauri ta shige toilet ta bar momma da ta zuba tagumi tunani yyi mata katutu.

Dahda da daddare da kansa ya shigo d'akin mommah ganin ko nemansa ba tayi ba. A zaune ya sameta kan sallaya da alama lazimi takeyi, jikinsa a sanyaye yake dubanta yana son matarsa shi kad'ai kuma ya san irin son da yake mata, ba don komai ba sai don yarda bata tsallake umarninsa kuma iya iyawarta take kyautata masa ba ta son 'bacin ransa sam.
Tana ganinsa ta d'an d'auke kai idanunta yana kawo hawaye. A gefenta ya zauna had'e da ri'ko hannunta tayi'ko'karin zamewa ya matse hannun murya a 'kasa yace"Deejah yau mantawa aka yi da abincinka?" Wani kallo tayi masa kafin hawayen idonta su zubo. Hawayen ya dinga bi da ido " kukan na menene?" Murya can'kasa tace " abincinka yana wajen amaryarka" fuska ya sake tamkewa kafin yace " wace irin magana ce wannan? Kema kin san sarai ba da amincewata aka yi aurennan ba, to me yasa zaki damu kanki yarda ta shigo haka zata koma, bani da tsarin ajiye mata biyu a gidana, ba ra'ayina bane tashi muje ki bani abinci kada ki sake'bata min rai" Ya jata ya mi'kar tsaye suka fita. Hanyar part d'insa direct suka nufa. Dai-Dai lokacin hafsa'yar hajjan ta ganosu itace auta a d'akinsu da sauri taje ta sanar da hajjan. Hajja kuwa tayi saurin fitowa fad'i take muje ba dani za'a yi wannan iskancin ba muje da kaina in kai masa amaryar in kuma nuna masa ni Na haifeshi ba shi ya haifeni ba...

A bakin 'kofar part d'in nasa ta tsaya tana buga  'kofar da 'karfi kamar zata  'balle 'kofar. Dahda ransa a 'bace ya bud'e 'kofar, murya a sar'ke yace "Hajja lafiya?" Kallon sama da 'kasa ta jefa masa " sannu isashshe har kana da bakin tambayata lafiya to ita lafiyar tana gidan ubanka wuce muje ka taho da amaryarka ita ta cancanta ta kwana a d'akinnan sai an mata kwananta uku rus da bazawara ta bata, kuma ban amince da ko bakin'kofar nan naga sillan'kafafunta ba wuce muje ka taho da matarka." Mommah da take cikin parlourn tana jiyo duk abinda yake wakana ta mi'ke zaune zauciyrta na tafarfasa ta fice daga palrlourn.

Shatu dake zaune a main parlour tana jiyo duk abinda yake wakana tayi al'kawarin yau tsohuwar nan ba zata kwana da lafiya ba. Ta shige d'akinta tana'kissama irin abinda za tayi mata. Da sauri ta shiga tanadin kayan duk da zata yi amfani dasu. Cikin dare ta nufi d'akin da aka sauke hajja, a hankali ta murd'a'kofar Ta shiga, Hajja ta tarar ta saki baki tana barci taci sa'a kuwa hajjan ita kad'aice a d'akin tabbas shirinta zai tafi yarda take so, Ta sake kallon shigar da tayi a mudubi'kusumbi tayi sosai a bayanta ga gashinta da ta saka ya rufe mata fuska gaba d'aya sai wani farin hjibin momma da ta sin'kife jikinta dashi, ba'a ganin fuskrta Sam, Ta dur'kushe sosai kamar wada tana lan'kwashe 'kafarta kamar a shanye take. Tsaye tayi gefen gadon hajjan kafin tasa sandar hannunta ta zunguri  'kafar Hajjan " Ke tashi ajalinki yau yazo tsohuwar banza mai takurawa jama'a....... A razane Hajja ta rusa wani ihu fad'i take " ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba innahu ala raja'ihi la'kadir......

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now