PAGE 51-52

48 14 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
             (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 51&52

___________________________Direct gida suka nufa,a hayar su ta dawowa Mami tasa driver yayi parking ya siyo musu fruit laida biyu irin wannan mai blue and black cike da fruit.

Cikin minti sha biyar suka isa gida.

Daukan laidodin Hauwa tayi ta shiga cikin gida da shi,kitchen ta nufa ta saka laidodin a fridge.

Zama Hauwa tayi kusa da Mami tace"Mami gyaran gashin nan yayi miki kyau sossai".

Murmushi Mami tayi tace"i nawa bai kai na ki ba,kin gan ki kuwa kamar wata yar india".

Dariya sossai Hauwa tayi tana rufe fuskar ta tace"ummmmm Mamiiiiii".

Dariya Mami tayi ta rungumo ta jikin ta.

A haka Jalal ya shigo ya same su suna sheka dariya.

Dagowa Mami tayi jin an bude kofa,ganin Jalal ne yasa ta fadin"a'a kayi mantuwa ne?".

Girgiza kai Jalal yayi ya nufi inda Mami ke zaune ya zauna kusa da ita ya daura kan shi a kafadar ta yana shagwabe fuska.

Bin shi da kallo Hauwa tayi har ya zauna kusa da Mami fuskar ta a hade.

Dagowa yayi suka hada ido,sossai gaban shi ya fadi ganin yanda tayi kicin-kicin da fuska ko alamun dariya babu bayan yanzu ya ji muryar ta tana dariya.

Gani yayi ta kara kyau sossai ba kadan ba,gyaran gashin ya mugun amshe ta,gashi an saki jelan gashin sai reto yake a baya.

"Toh oga hadari ka zo ita kuma ta dauke wuta,na rasa gane kan wannan kiyayyar dake tsakanin ku,ko da yake banga laifin ta ba,duk kai ne sila ba shakkah",ta fada tare da dungure mishi kai.

Turo baki Jalal yayi ya bata fuska yace"Mami ni kumaaaa! mai na yiiiiii!".

"Murmushi Hauwa tayi ta kawar da kan ta gefe,sossai yanda yayi maganar ya bata dariya sai yayi kama da wani baby".

Dungure mishi kai Mami tayi tace"i ka fini sani ba sai na fada ba".

"Beside mai ya dawo da kai yanzu?".

Shiru Jalal yayi ya nuna mata kan shi da yatsa yace"headache Mami".

Ayyyahhh! naga kana yawan ciwon kai  kwanan nan ko muje hospital ne,ta fada tare fa taba goshin shi har zuwa wiyan shi.

Juyowa Hauwa tayi suka hada ido,turo baki tayi ta dauke kai.a zuciyar ta tace"dan rainin wayau sai shegen kallo kaman maye"mtswwwwwww!.

Murmushi Jalal yayi yace"yarinya zaki sani ne bari ki shigo hannu".

Daka mai duka Mami tayi a baya tace"dan kaniyar ka murmushin uban meh kake".

Sosa kai Jalal yayi yace"babu komi Mami abu kawai na tuna".

Hmmmmm! shikenan tashi kaje ka watsa ruwa ka sha magani,amman sai munje hospital  yau duk iskancin ka kuwa,am i clear.

Girgiza mata kai Jalal yayi murya kasa-kasa yace"dan Allah Mami ki bar zuwa Asibitin nan pls,ba fa wani ciwon kai sossai bane fahh!,kadan-kadan ne, kuma ina shan magani na kwanta yanzu zai sake ni,kinji Mami naaaaa",ya karasa maganar shi yana shagwabe mata fuska.

Jan hancin shi Mami tayi tace"wlh baka isa ba,gwara aje a gani in ma zazzabin ne a tare shi tun da wuri,dan in na bari ya kama ka na shiga uku,ni za'a bari da wahala dan wannan matar naka ba komi ta iya ba".

Murmushi Jalal yayi yace"shikenan Mami Allah ya kaimu anjiman".

Yauwa My Son Allah ya kaimu rai da lafiya.

"Ameeen Mami na",ya fada tare da mikewa tsaye ya nufi stairs.

Hararan shi Hauwa tayi tace"kana ganin shi kaman wani boss ashe mugun mataoraci ne,i kuwa da ni za'aje Asibitin nan yau duk bala'i ahaaa!".

Da misalin karfe daya da minti arba'in suka gama shirin tafiya Asibiti har da Hauwa.

Jameela ce tsaye a upstairs ta hade giran sama da kasa sai cika take tana batsewa,kasa danne zuciyar ta tayi tace"ke kuma karere ina za ki,ni matar gida banje ba sai ke yar aikiiiiiii!",ta fada ranta a bace tana nunata da yatsa.

Murmushi Mami tayi tace"idan kin isa ki hana faruwan hakan,ni kuma sai na saukar miki da takamar da kike da shi na matar gida".

Da ace akwai mutun a gefen Jameela da sai ya ji sautin da cikin ta yayi kulllllllllllll!.

Wani irin miyau ta hadiye da kyar tana zazzare ido.

Sossai Jalal yayi farin ciki jin Mami tayi maganin ta,sossai ya ji shi wasai duk wani ciwon da yake ji ya kau.

Yana murmushin shi mai kyau ya fice daga parlor yana gyara kwalan rigan shi.

Bayan sun kai Asibiti aka mishi test,bayan result ya fito aka tabbatar yana dauke da cutar malaria.

Bayan Doctor ya gama dube-duben shi yace"Mama bincike ya tabbatar mana cewa yana da cutar Malaria,za'a iya daura shi a kan magani amman due to na shi complain din ciwon kai akai-akai  da so samu ne yayi Allura zai fi sauka da sauri".

Jalal na jin an anbaci allura ya juyar da kai gefe ya hada rai.

murmushi Mami tayi tace"ayi alluran kawai doctor tunda shi ya fi".

Ayyah Mami a ban maganin kawai zan sha Allah.

Hauwa bata san lokacin da dariya ya zubuce mata ba,saurin toshe bakin ta tayi ganin kowa na kallan ta.

Harara Jalal ya dallawa Hauwa ya turo baki.

Murmushi Doctor yayi yace"halan wannan ne Auta".

Dariya Mami tayi tace"shi kadai ne ma".

Ba mamaki kam dan ga alamomi,sai kace ba namiji ba,common allura haba malan karka bada mu fahhhhh!.

Shiru Jalal yayi bai ce komi ba,Allah ma ya sani bayan son allura ko kadan,shi duk wani abu da zai shiga jikin shi ba so yake ba.

Da kyar da boni aka mai alluran,shima sai da aka ce za'a kira Hauwa kafin ya ya yarda aka mai.......................

Ku yi hakuri da wanan

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.


🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now