🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 2 IS LOADING,WASU SUN FARA BIYAN KUDIN SU,KU HANZARTA BIYA AKAN DARI UKU KACHAL KAFIN WA'ADI YA CIKA,ALLAH YA BAKU IKON BIYA AMEEEEN.
BOOK 1:CHAPTER 119-120
_________________________Bayan sallar isha'i Sani ya shigo,ko zama Lubna bata bari yayi ba ta fada mishi karya da gaskiya shi ko ya hau kai ya zauna,a harzuke ya fito daga dakin yana kwalawa Hauwa Kira.
Gaban ta ne yayi mugun faduwa,tun da ta ji wannan kiran ta san ba lafiya ba,kasa motsi ta yi daga kan darduman da take zaune.
Bugo kofar yayi ya tako har gaban ta yace"ubanwa ya baki izinin fita?,kuma daga gidan ubanwa kike?".
Shiru Hauwa ta yi dan ta san aikin Lubna ce,daga ganin yanda ya harzuka ta san ko ta fada mishi gaskiya ba yarda zai yi ba hakan yasa ta fadin"daga inda ka aike ni".
Wani wawan mari ya dauke ta da shi,saurin dafe kuncin ta tayi tana kokarin tantance zafin marin ya kuma kai mata wani ta gefen hagu da sai da yasa ta faduwa.
Kuka ta fashe da shi tace"meh na maka da ka mare ni?".
Kokarin kwance belt din shi yake yace"za ki sami amsar ki yanzun nan",dukan ta ya fara yi da belt din hannun shi yana fadin daga yau baza ki kara min rashin kunya ba kuma ko uwar ki ce ta zo baza kiyi gigin rakata ba balle ki yi tunanin fita.
Cikin kuka da zafin duka tace"wlh ba dai uwata ba sai dai na mutun".
Ji kake tasssss!,wurgar da belt din hannun shi yayi ya fara ball da ita,yana yi yana hadawa da hannu.
Dungule jikin ta tayi wuri daya tana kuka tana chanja direction,duk inda ya bugo ta nan za ta nufa,sai da ya gaji dan kan shi sannan ya kyale ta.
Lubna dake ta kwasar shoki a bakin kofar ta ruga da gudu jin ya bar dukar ta.
Da rarrafe Ameen ya karaso ya rungume Mamin shi yana share mata hawaye yana kuka yace"srry Mami,zan kashe Daddy idan na gir"..............
Rufe mishi baki tayi tana girgiza mishi kai hawaye na zuba daga idan ta tace"babu kyau ka ji, don't say that again,wasa kawai muke da shi ka jiiii!".
Girgiza kai yayi alamun bai yarda ba yace"y are u crying Mami?".
Rungume shi ta yi da karfi sakamakon kukan dake kokarin kufce mata,da haka barci ya kwashe ta,ba ita ta farka ba sai da aka tayar da sallan Asuba,tana mikewa Ameen ya tashi,a tare suka shiga bayi, electric kettle ta jona sannan ta juye ruwan flask ta yiwa Ameen wanka ta nade shi a towel ta shiga ta hada ruwa mai zafi sossai ta gasa jikin ta da shi.
Tun daga ranar abu ya kara tsamari,wani lokaci haka kawai zai shigo ya kwada mata mari babu gaira ba dalili,idan ta yi magana yace"bata gaishe shi ba".
Tun Hauwa na hakuri har ta fara gazawa,gashi babu wanda za ta gayawa ta ji sanyi,Maman Fauzan ta yi tafiya kuma number ta baya shiga,hakan ya kara sata shiga cikin damuwa na daban.
Zaune Hauwa take a parlor Lubna ta shigo tana wani toshe hanci,kallan ta Hauwa ta yi da mamaki tana karewa parlor kallo tare da jan hanci duk a son ta na gano abinda ke wari a parlor amman bata gano ba.
Muryar ta ta tsinkaya tana fadin"ki je ki cire kayan jikin ki tularen bai yi min ba".
Galala Hauwa ta yi da baki tana kallon ta da alamun mamaki ta kuma maimaita abinda ta ce.
Gyara tsayuwa Lubna tayi tana turo shafafan cikin ta tace"za ki yi ko baza ki yi ba?".
Kai tsaye Hauwa tace"bazan yi ba sai ki dau mataki,iskancin banza da wofi,yau na fara sa tularen da zaki gaya min maganar banza,ina ji ko jiya shi nasa",ta karasa maganar ta tare da jan tsaki ta gyara zama.
Waya Lubna ta dauka ta dan yi dan latse-latsen ta ta kara a kunne tana kukan makirci tace"Honey kaga Anty ta saka wani tulare da babu dadi shine na roke ta ta cire kayan in yaso ko tulare na ne sai na bata ta fesa amman taki,gashi nata tularen amai yake sa ni,sahu na uku ina amai,daga karshe na gaya mata dalili amman ta ce in dai haka ne sai dai ya bare",ta karasa maganar ta na kuka ta kuma fadin shine ta je ta dauko tularen ta fesa a parlor har da daki naaaa!,ta karasa maganar ta na kuka sossai,sai ka rantse da Allah rasuwa aka mata.
Jin ya katse wayar yasa Lubna cire wayar a kunnen ta tace"ya ki ka ga kafcen",na tabbatar yau sai dai wata ba ke ba,ta fada tare da fashewa da dariya tana zagaye ta tana tafa hannu.
Tun da ta fara magana Hauwa ke kallon ta baki bude har ta gama,gaba daya jin ta da ganin ta ne ya dauke na wucin gadi,saukar marin da ta ji akan kuncin ta ne yasa ta farfadowa daga mutuwar zaunen sa ta yi.
Saurin dagowa ta yi dan ganin wanda ya mare ta,ido biyu tayi da Sani da idan shi yayi jazir sai huci yake kaman zai ci babu.
Ja da baya ta yi bakin ta na rawa tana kokarin yin magana ya kai mata marin da sai da yasa ta wuntsulowa daga kan kujera,zare belt din dake jinkin shi yayi ya hau jibgar ta,ganin belt din ba zai mai ba yasa ya naimo wayar wuta mai kauri ya fara jibgar ta da shi,tana kuka tana rokon shi amman fir ya ki.
Wurin receiver Lubna ta nufa ta saki kida tare da kara volume sossai ta koma baya tana tikar rawa sai murna take tana kwaso shoki.
Tun daga kofar gida Ummi ta ji kida na tashi,da mamaki take bin gidan da kallo,ita dai ba taga sha'anin da ake da zai sa a kunna uban wakar nan ba,ta san sam Kulu baza ta yi wannan shashancin ba sai dai kishiyar ta,tana surutu ta doshi parlor,ko sallama bata tsaya yi ba dan ta san baza'a ji ba.
Dai-dai nan Sani yasa kafa ya tokare ta a ciki,wani irin kara Hauwa ta saki ta dafe marar ta ta sulale kasa sumammiya jini na bin kafar.
Ihu Ummi tayi ta nufe shi gadan-gadan ta dauke shi da mari.
Ko kadan bai ji zuwan ta ba illa saukar marin daya ji hagu da dama.
Dafe kuncin shi yayi yana kallan ta.
Tana huci ta nuna shi da yatsa tace"wlh wani abu ya same ta na rantse da Allah kotu ce za ta raba mu da kai,kuma wlh tunda ka bige ta ka bigi auren ka,sabida haka ina jiran takardan ta,ta karasa maganar a tsawacen da sai da yasa Sani ya razana,dama chan yana shakkar ta.
Tuni Lubna ta sha jinin jikin ta,sai kifta ido take kamar kazar data fada ruwan zafi.
Tallabo ta Ummi ta yi ta fita da ita,tana fita kofar gida ta ga mai a daidaita,cikin hanzari ta tsayar da shi ta gaya mai inda zai kai su.
Kashe wakar Lubna ta yi ta nufe shi tana kokarin kwantawa a jikin shi,a zuciye ya juyo tare da aika mata da wani irin kallon daya kusa tsinka hanjin cikin ta yace"..........................................
Book 2 is loading,wasu sun fara biyan kudin su,bana san bonus payment ya wuce ku.
Bonus 300
Nrlm 500
Complete 1000.Ku hanzar ta biyan kudin ku,kar ku bari a yi ba ku,taken na daban ne.
Ga masu wattpad za su iya karantawa ta nan dan an saki page daya.
Account number 2245462427
Account name Aisha Maaruf
Bank Name UBA.
Evidence of payment 08076119294Comment
Vote
ShareBy Gimbiya Ayshu💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficção Histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...