🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1:CHAPTER 123-124
___________________________Bayan sallar magariba Ummi ta faki idan Mama ta fice daga Asibitin,bata zarce ko ina ba sai gidan Hauwa.
Kai tsaye ta shige cikin gidan ba tare da sallama ba,ganin banu kowa a parlor yasa ta naimi wuri ta zauna ta ha daura kafa daya kan daya tana karewa parlor kallo.
Sauri Lubna take ta gama wanka dan duk a tunanin ta mijin ta ne ya dawo,tana fita daga bayin ta nufi parlor ganin baya daki,tana shiga idan ta ya fada kan Ummi,kadan ya rage nunfashin ta ya dauke tsabar tsoro,sossai ta shata mamaki dazu, murya ta na rawa tace"ehm...em"....
Katse ta Ummi ta yi da fadin"keh dalla malama yi min shiru,ba na bukatar karin bayanin ki,ina mijin ki yake?".
Jiki na rawa Lubna ta ce"bai....bai shigo ba",ta fada tana zare ido.
Lumshe ido Ummi ta yi ba tare da ta tanka ta ba,ganin haka yasa Lubna ta koma daki sim sim kamar wata munafuka.
Bayan sallar Isha'i Sani ya shigo hannum shi rike da laida sai fara'a yake.
Da mamaki Ummi ta dinga bin shi da kallo,kasa shanye mamakin ta ta yi ta budi baki ta ce"hankalin ka ya kwanta tunda ka kusa aikata barzahu,yanzu sai ka zuba ruwa a kasa ka sha".
Da sauri ya kalli bangaran da ya ji muryar ta,mikewa Ummi tayi ta karaso gaban shi tace"takarda za kaban".
Da mamaki yake bin ta da kallo dan sam bai fahimci mai take nufi ba.
Murmushi Ummi ta yi tana kada kai tace"takardar saki nake nufi,so nake ka saki Hauwa yanzun nan,dan wlh baza ta zauna da kai ba,sabida haka ba tare da bata lokaci ba ka rubuta takardar ka bani".
Zuru ya yi yana kallan ta kaman wawa,a fusace Ummi ta daka mai tsawa tace"wlh ko kaban takardar cikin salin alin ko kuma na maka ka kotu kuma wlh sai an ci ka tara,sabida haka zabi ya rage ga mai shiga rijiya",ta fada tare da mika mishi hannun ta alamun ya bata takardar.
Ajiyar zuciya ya sauke yace"toh shikenan zan bayar",ya fada tare da juyawa ya nufi dakin shi.
Bin shi Ummi ta yi har dakin ta tsaya mishi a kai har sai da ta tabbatar ya rubuta.
Amsar takardar ta yi fuskar ta kunshe da farin ciki tace"Alhamdulillah,mun yarda mangwaro mun huta da kuda",ta fada tare da linke takardan ta damke shi da kyau ta turo dankwalin ta gaba ta fice daga gidan tana murmushi kaman ta taka rawa.
In ran Mama ya yi dubu toh ya tashi dan ta naimi Ummi sama da kasa ta rasa,har taya ta Dr yayi amman babu ita babu alamun ta,safa da marawa kawai Mama take a harabar dakin da aka kwantar da Hauwa idan ta cike da hawaye.
Da gudu Ummi ta rungume ta tana murna,a fusace Mama ta janye ta daga jikin ta ta sharara mata marin daya dauke mata jin ta da ganin ta na tsawon dakika biyu.
Tana shirin rufe ta da duka likita ya janye ta ya sa ta a bayan shi yace"Mama dan Allah ki yi hakuri ki kwantar da hankalin ki".
A fusace Mama tace"daga ina kike Ummi?".
Turo baki Ummi ta yi tana labe a bayan Dr tace"naje amso takardar Hauwa ne".
Dafe kirji Mama ta yi tace"na shiga uku Ummi,kika ce meh?".
Ja da baya ta yi dan ta san tsaf Mama za ta iya janyo ta daga bayan likita,turo baki ta yi tana gyara gyalan jikin ta tace"takardar sakin Hauwa na amso"ta fada tare da miko mata takardar daga nesa.
Ja da baya Mama ta yi ta zauna a kan kujera tace"na shiga uku ni Mairo,kin kashe ni,kin tona min asiri".ta fada tare da rafka uban tagumi.
Juyowa Dr ya yi ya kalli Ummi ya ga ko girgiza bata yi ba,idan ta tar a bushe.
Murmushi likitan ya yi ya ce"Ummiiiiiii!".
Wani irin sanyi ne ya diran mata a zuciya sakamakon kiran sunan ta da ya yi,dagowa Ummi ta yi tana turo baki ta ce"ummmm".
Murya a sanyaye ya ce"mai yasa kika yi haka?",ba tare da ta kalle shi ba tace"sabida ya bige ta,ni kuma bazan laminta ba".
Kura mata ido Dr yayi yana kallan dan karamin bakin ta.
Harara ta dalla mishi tace"ni kam ka bar kallo na haka kar idan ka ya leke min a goshi".
Murmushi ya yi ya shafa keyar shi ya ce"Allah ya baki hakuri gimbiyar mata,tuba nake",ya fada tare da barin ta a wurin ya nufi wurin Mama yana lallashin ta.
Bayan tafiyan likita Ummi ta lallaba ta karaso kusa da Mama ta yi kneel down ta hade hannayen ta wuri daya ta fashe da kuka tace"Mama dan Allah ki yi hakuri ki yafe min,wlh bazan kara baaaaa!".
Shiru Mama ta yi ba tare da ta kalli bangaran da take ba.
Kara karfin kukan nata ta yi tana yiwa Mama magiya,ganin tana kokarin tara mata mutane yasa ta jawo ta ta rungume ta tace"mai yasa za ki yi haka Ummiiiiii?,mai yasa kika kashe mata aure?,ko wace mace da kika gani tana da matsalar da ta ke fuskanta a gidan miji,ita na ta"MATSALAR GIDAN MIJI"kenan,hakika Ummi banji dadin abinda kika yi ba,ni bama shi ne babban damuwa na ba,damuwa na shine ya zan yi idan Hajiya ta ji zanchan nan.
Murmushi Ummi tayi tace"anzo wurin",washe baki Ummi ta yi tace"in dai Hajiya ce matsalar ki Mama toh ki kwantar da hankalin ki,na san yanda zan tafiyar da al-amarin ta yanda ko kadan Hajiya baza ta zarge ki ba".
Girgiza kai kawai Mama ta yi ba tare da ta amsa mata ba.
Washe gari tun da sanyin safiya Ummi ta nufi gidan Hajiya taje ta shirya mata karya da gaskiya,sai da ta tabbatar ta hura wutan kin Sani a zuciyar kafin ta barta.
Nan Hajiya ta fara sababi har zani na faduwa daga jikin ta,ko gyale bata dauka ba ta nufi hanyar fita daga gidan dan zuwa ciwa Sani mutunci sannan ta amso takardar sakin ta.
Saurin riko ta Ummi ta yi tana sharan hawaye tace"yi hakuri Hajiya,zo ki zauna na miki bayani,tana jan ta tana tirjewa,da kyar ta samu ta lallaba ta sannan ta ce"tuni na hutarshe ki Hajiya,i na amso takardar".
Da sauri Hajiya ta zauna ta ce"ki ce Allah"........................
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficción histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...