PAGE 67-68

44 9 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEFANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 67-68

___________________________Bayan shekara biyar da Auren su Mama ta samu ciki,zo kuga murna gun family,tattalin ta Abba da mijin ta su ke kaman kwai,ya hana ta yin komai ko tsintsiya bata dauka,shi ke yin komai kafin ya bar gida,sossai wannan abin ke kuntatawa Inna rai amman tayi shiru ba halin magana,bayan wata tara Mama ta haifi diyar ta kyakyawa,bayan suna taci sunan Asiya ana kiran ta da ummi,bayan shekara uku Mama ta kara haihuwar mace,ran suna yarinya taci suna Hauwa'u,tun daga kan Hauwa haihuwa ya tsaya,sossai Mama ke nunawa yaran ta kula da soyayyah.

Bayan shekara ashirin da auren su Allah ya yiwa Baba rasuwa,sossai Mama tayi kukan rashin mijin ta,bayan kwana arba'in Inna tasa aka siyar da duk wani kadaran Baba da ke bayyane ta rike kudin ba tare da ta ba Mama da yaran ta ko sisi ba,ko kadan Mama bata nuna damuwa a kan hakan ba,ta hakura ta bar wa Allah komai.

Alhaji Abdulkaeeem Danbatta haifaffan dan garin Kano ne kuma babban dan kasuwa wanda ya gada daga wurin mahaifin shi,ya hadu da matar shi Hajiya Juwairiyyah a Airport ya je taran mahaifin shi ita kuma saukar ta daga Dubai kenan ita da yan uwan ta sun je shakatawa.

Tun da Abie ya kyallara ido akan Mami ya ji duk duniya ba wata sai ita.

Saka driver yayi ya bi motar su ya gane mai gidan su,hakan ko aka yi,bayan kwana biyu Abie yayi diran mikiya a gidan,kai tsaye yasa aka yi mai sallama da Alhaji,ya ko ci sa'a yana gida,nan take Alhaji ya bada izinin a shigo da shi,bayan Abie ya shigo sai ya zauna a kasan carpet kan shi a kasa,Alhaji yayi-yayi ya zauna kan kujera amman yaki,murmushi Alhaji yayi sannan ya naimi jin mai ke tafe da shi,ba bata lokaci Abie ya sanar mishi a kunyace.

Murmushi Alhaji yayi yace"kai dan gidan waye".

Kan shi a kasa yace"Alhaji Abdulkareem Danbatta".

Da sauri Alhaji ya dago ya kalle shi yace"dama kai dan gidan Danbatta ne" ya fada da alamun mamaki sannan yace"ikon Allah ya wuce gaban misali".

"Toh shikenan yaro jeka zan duba lamarin".

Mikewa Abie yayi da niyyan tafiya,nan Alhaji ya maida shi yace dole sai yaci abin da aka kawo mai.

Hakanan Abie ya dan tsakura ganin da gaske ba zai fita ba.

Yana fita Alhaji ya dau waya ya kira Abban Abie ya sanar mai,kabbara Abban Abie yayi yace"ikon Allah,muna shirin hada su sai ga shi ya riga mu,wannan ake cewa riga malan masallaci",Allah ya tabbatar mana da al-khairi yasa matar shi ce Ameeen.

Nan suka dan taba hira Alhaji ya mai a huta gajiya.

Wasa-wasa soyayya ya kullu a tsakanin su.

Bayan wata biyar su kayi aure Abie ya dauki matar shi suka dawo kaduna ya cigaba da kula da company Abban shi dake kaduna.

Bayan shekara uku da Auren su Mami ta haifi danta fari Saul ta hanyar cs.

Bayan sati biyu da haihuwar ta aka yi suna yaro yaci suna AbdulJalal,haka Mami ta cigaba da rainon dan ta cikin gata da kulawa,bayan ya kammala karatun shi na secondary Abban shi ya tura shi USA karatu inda ya karanci business(kadon kado kenan).

A chan U.S.A ya hadu da Jameela suka fara soyayyah,bayan sun dawo mid semester aka daura musu aure a lokacin Jalal na ajin karahe ita kuma tana Level 2 dama three years program ne.

Ko da Jalal ya gama bai dawo ba iyaka su zo hutu,sai da Jameela ta gama kafin suka tattaro suka dawo nan gida Nigeria.

Alhaji Bashir Shu'aibu haifaffan dan Zaria ne,yana da babban shagon siyar da atanfa da materials har da shaddodi,yana da mata daya da yara biyu.

Hajiya Rabi mata ce ga Alhaji Bashir,bayan auren su da wata biyu ta samu ciki,cikin na da wata hudu ya bare.

Hajiya Rabi tayi bari sau uku ta haifi biyu sun rasu.

Ana haka ta samu ciki bata ma sani ba har sai da cikin ya kai wata biyar,haka dai ta cigaba da kula da cikin cikin tsoro da zullumi har ta haihu aka yi suna yaro ya ci suna Sani,sati daya biyu wata daya biyu har shekara ta ga yaran bai rasu ba,nan ta fauwalawa Allah komai,bayan shekara takwas da haihuwar Sani ta sami ciki ta haifi Mace yarinya taci suna Hafsat.

Bayan wasu shekaru Baba ya kamu da ciwon diabities,ya dau tswaon shekara biyu yana fama da ciwon kafin rai yayi halin shi..............................

       *****CIGABAN LABARI*****

COMMENT
VOTE
   &
SHARE.

BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now