PAGE 39-40

48 11 3
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

Gaisuwa ta musamman ga

Maryam
Maryudah
Sis Hafsy
Abdou Manzo

BOOK 1:CHAPTER 39&40

____________________________Bayan kamar minti biyar Kawu Lado ya karaso.

Har kasa Sani ya duka ya gaida Kawu Lado da Ladabi da biyayyah.

Murmushi Kawu Lado yayi dan sossai yaran ya birge shi,ya yaba da halin shi sossai,a zuciyar shi yace"dama ana samin irin wannan yaran a wannan zamanin".

Mike ka zauna yaro Allah yama albarka.

"Da Ameeen Ameeen Baba Sani ya amsa ya dosana duwawun shi kan kujera kan shi a kasa".

Magana su kayi inda Kawu ya tabbatar an bashi izinin zuwa zance wurin ta in har ta amince da shi.

"Godiya sossai Sani yayi tare da yiwa kawu Addu'a da isani".

"A'a kabar shi yaro angode".

"A'a Baba dan Allah ka amsa wannan kyauta ce".

"Toh shikenan yaro Allah yayi Albarka ya kara budi ya tsare ka".

"Ameeen Ameeen Baba nagode Allah ya kara nisan kwana".

Toh yaro bari na turo ta,ya fada yana mikew tsaye.

Ko daya fito babu kowa a tsakar gida,kofar dakin su Hauwa Kawu ya nufa yayi sallama Mama ta fito jikin ta sanye da hijabi tace"sannu kawu barka da fitowa".

"Yauwa barka Mairo,nayi magana da shi kuma nima na yaba da hankalin shi na ba shi izini in dai ta yarda shikenan sai ya fara zuwa zance".

"Toh nagode kawu Allah anfana ya bar zumunci Ameeen".

"Yauwa Mairo na tafi ki gaida yara".

"Toh Kawu ka gaida su Maman Hamida".

"Toh Mairo za su ji insha Allah".har ya juya zai tafi sai yace"yauwa na manta kicewa Hauwa taje yana jiran ta.

Toh shikenan Kawu nagode Allah ya tsare ya kiyaye hanya.

Daki Mama ta shiga ta sanar da Hauwa sakon Kawu.

Tashi Hauwa tayi ta fita kamar wacce ba tada lakka a jiki.

Zama tayi a kan doguwar jujera kanta a kasa tace"ina wuni".

Murmushi Sani yayi yace"lafiya kalau ykk Gimbiyar Mata fatar na same ku lafiya?".

"Alhmd ya gida ya hanya".

"Hanya Alhmd gida kuma suna lfy".

Yauwa Gimbiyar Mata nace ina maganar mu ta kwana?.

Shiru Hauwa tayi ta kasa magana.

Murmushi Sani yayi,kunyar yarinyar na daya daga cikin abinda ke birge shi.

"Hauwaa!"

Dagowa tayi ta kalle shi sabida yanda ya kira sunan ta,ji tayi kamar duk duniya babu wanda ya kai shi iya kiran sunan.

Da ummmm....kawai ta amsa ba tare data furta ko uffan ba.

"Hauwa kin amince kin bani dama na zama abokin rayuwar ki?".

"Daga mishi kai tayi kirjin ta na bugun tara-tara".

Salati tayi a zuciyar ta tace"Allah know's best,na amsa ba tare dana shirya ba,ya Allah kasa hakan shine alkairi,ya Allah kai kadai kasan gaibu,ya Allah kamin zabi na gari Ameeeen".

Sossai Sani yayi hamdala da murna yace"ina yiwa Allah godiya da yasa kika amince da ni,kuma ina rokon Allah daya kaimu ga Aure ya bamu ikon zama lafiya da fahimtar juna na har abada".

"Da Ameen Hauwa ta amsa tana jin wani iri a zuciyar ta".

Tuna abinda Jalal yayi mata dazu tayi,sossai tayi mamakin ceton ta da yayi a hannun wannan tsaburarran matar tashi mai kama da muciya.

Har da share mata jini a gefen baki,da kare ta daga wannan muciyar matar tashi,anya kuwa ba gadar zare suka shirya mata ba,anya kuwa.......shiru tayi tana tunani.

Sani yayi mata magana ya kai sau uku amman shiru,buga hannun kujerar da take zaune yayi yace"lafiyar ki kuwa?,na kira ki ya kai sau uku amman shiru".

A firgice Hauwa ta dago tace"emmmm.........ummmm wlh babu komi,na dan tuna da wani abu ne".

"Okh toh shikenan Allah yasa lafiya".

"Ameeeen"

Hira suka dan taba kadan,tun Hauwa na shiru har ta fara amsa mai,ba jimawa yayi mata sallama,raka shi Hauwa tayi har waje ya hau babur din shi ya tafi.


A bangaran Oga Jalal a ranar kwana yayi yana tunanin Hauwa,most especially rungumar data mai,ji yake kamar har lokacin tana jikin shi,sabida kamshin tularan ta dake tashi a jikin shi.

Wani bangare na zuciyar shi yace"anya  Jalal lafiyan ka kuwa?,akan meh zaka na tunanin wannan village girl,ba dai ka fara sonta ba".

A fili ya furta"noooo! inaaaaa! baze yiwu ba".

"Juyowa Jameela dake zaune kan dressing mirror tayi tana kallan shi da alamun mamaki".

"Ganin irin kallan da Jameela ke mai yasa shi gane katobarar da yayi,hade rai yayi ya mike yana mazurai ta shige bayi".............................................

Kuyi hakuri da wannan way ta babu charge wlh.

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now