🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
BOOK 1:CHAPTER 69&70
__________________________Duk wanan shirye shiryen da ake Jalal bai sani ba.
Ana saura sati biyu biki wani tafiyan gaggawa ya kama Jalal.
Hada kayan shi yayi ya nufi dakin Mami dan yayi mata sallama,rako shi Mami tayi har wurin bakin motar shi.
"Ina matar taka take?".
"Tana daki".
"Ban gane tana daki ba,ba tare zaku tafi ba?".
Daga mata kai Jalal yayi ya shige mota da sauri ya kulle sabida kar ta kuma tanbayar shi,kunna motar yayi ya zuge glass yana daga mata hannu fuskar shi dauke da murmushi ya fice daga gidan.
Sai da motar shi ya fice daga gidan kafin Mami ta rufe bakin ta mamaki na cin ta,iya sanin ta da Jalal ko kwana biyu zai yi sai ya tafi da matar shi sai gashi zai yi har sati biyu amman hmmmmm.........da alamun tanbaya a wannan alamarin,dama tun kwana biyu daya wuce ta ke lura da su kaman akwai wani matsala,amman babu komai in tayi wari za muji.
Wasa-wasa biki ya rage saura sati daya,sai shirye shirye ake ta ko wani bangare,Sossai Mami ta kashe kudi wurin yiwa yar ta kayan daki da kitchen,Mama bata so ba amman babu yanda ta iya dan fir Mami ta ki wai i yar ta ce.
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya.
Bayan an idar da sallar Juma'a aka daura auren Sani Bashir da Hauwa'u Mu'azu Sa'id akan sadaki dubu dari lakadan ba ajalan ba.
Hauwa na jin an daura aure ta fashe da kukan da ita kan ta bata san dalili ba.
Zama Ummi tayi kusa da ita tana lallashin ta amman ta ki shiru sai kara karfin kukan nata take.
Da abin ya ishe Ummi sai ta mike ta dungure mata kai tace"iskancin banza iskancin wofi yanzu kukan uban me kike,ina jin ke kika kawo shi kika ce kina son shi,kuma an aura miki shi,toh kukan kuma na mehh iskanci kawai mtswwww" ta fada tare da ficewa daga dakin ranta a bace tana banbami,ta kula da ita tunda auren ya kusa take ta wani bata rai,da an mata maganan shi sai ta bata rai sai kace wani ya naimo mata shi ko kuma dole aka mata.
Zaune Mami take a gefen gado ta jingina da katakon gadon hannun ta rike da waya tana latsawa call din Jalal ya shigo,da mamaki Mami ke kallon number tayi picking,tun kafin tayi magana taji yace"Mamina ina wuni,na dawo ban same ki ba ina kika je"ya fada muryar shi na dan cracking.
A dan rude Mami tace"mai ke damun ka son,ya naji muryar ka haka".
Murmushin yake Jalal yayi yace"babu komai Mami kawai gajiya ne"ya fada tare da zama kan kujera.
Toh shikenan je kayi wanka ka huta tunda dawowar ba zata kayi mana ni dai sai ka ganni domin naje bikin diya ta.
Da mamaki Jalal ya dago yace"ban gane diyar ki ba Mami,daya daga cikin yaran big Mum ke auree?".
Dariya Mami tayi tace"noooo Hauwa ce fahhhhh! ko ka manta ta ne a cikin sati biyu?",ta karasa maganar ta tana dariya.
Mikewa Jalal yayi idan shi yayi ja yace"Mami ban gane ba,wace Hauwa kike nufi?",ya karasa maganar shi muryar shi na rawa.
"Hmmm Jalal wace irin magana ce wannan,Hauwa ce baka sani ba,toh bari na fito maka a yanda zaka gane,Hauwa mai min girki da gyaran daki,daughter ta,ina fatan ka gane yanzu".
Salati Jalal yayi ya sulale a gurin sumamme.
Zulai dake aiki a kitchen ne ta leko jin faduwar abu,da sauri ta karasa in da yake tace"Ya Jalal Ya Jalal,ta fada tana girgiza shi amman shiru ba amsa".
Wayar shi dake kusa da shi ta jawo jin muryar mutun na fita ta wayar,tana dubawa taga yasa Mamina da heart uku,kara wayar tayi a kunne da sauri muryar ta na rawa tace"Hajiya Ya Jalal ya fadi kuma baya nunfashi ban san mai ya faru baaaa!".
A zabure Mami ta mike tace"whatttttttt!".kashe wayar ta yi ta dauki jakar ta da gyalan ta ta rataya a kafada ta nufi kofar dakin idan ta ya tara hawaye,a kofar parlor tayi kicibis da Mama,zata bi ta gefen ta ta wuce Mama ta riko ta tace"Yaya mai ya faru?".
Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro daga idan Mami tasa hannu ta share shi da sauri muryar ta na rawa tace"Jalal ne".
Da mamaki Mama ke kallon ta tace"mai ya same shi?".
Hanki tasa tana share hawayen ta tace"ya suma,ban san mai ya same shi baaaa",ta fada tare da barin wurin.
Sam Mami ba tada juriya indai akan Jalal ne.
Cikin minti 10 suka isa gida,bata bari driver ya gama parking ba ta balle marfin motar ta fice da gudu,tana shiga parlor tayi ihun sunan Jalal.
Da sauri ta karasa inda yake kwance tana jijjiga shi tana kiran sunan shi amman shiru ba amsa,kuka Mami ta fashe da shi ta rungume Jalal,dai-dai nan driver da Baba suka shigo suka kinkime Jalal,sai a lokacin Jameela ta fito jin hayaniya yayi yawa,da sauri ta nufi saukowa a stairs ganin Jalal rike a hannu.
Dai-dai tana isa baki motar ana kulle kofa,wani mugun kallo Mami ta aila mata da shi sannan ta bude kofa ta shiga.
Cikin minti sha takwas suka isa,ba bata lokaci aka amshe shi aka nufi emergency room da shi dan ba shi taimakon gaggawa.
Bayan sallah la'asar aka dauki Amarya zuwa gidan mijin ta dake Zaria.
Tunda aka daura aure Hauwa take kukan da aka kasa gano dalilin shi har aka kai ta gidan ta bata bar kuka ba.
Bayan sallan magariba aka zo daukar kawayan Amarya da su Inna da wasu kawayen ta da Aminan Mama biyu.
Riko hannun Ummi Hauwa tayi tace"Anty Ummi mai yasa banga Mami na ba?".
Bata fuska Ummi yayi tace"naji Mama ta ce yaron ta ba lafiya wai ya suma".
Ta fada yana mikewa da sauri jin an danna horn.
Rungume Hauwa tayi ta fashe da kuka,sai a lokacin ta fara jin kewar yar uwar ta rayuwa kenan.
Tun da su Ummi suka wuce hankalin ta yaki kwanciya gashi ita kadai ne a gidan gashi ba waya balle ta kira Mami,ta san Mami na cikin damuwa sossai ga shi ba mai lallashi................................
BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficción histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...