🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1:CHAPTER 115-116
__________________________Bayan ta dawo ta yiwa Ameen wanka ta bashi biscuit sannan ta nufi kitchen ta karasa girkin da ta fara.
Tunda wannan abin ya faru Lubna bata kara shiga sabgar Hauwa ba,wani irin shakkar ta take.
Bayan sati daya Hauwa ta karbi girki,ko kadan bata doki don har lokacin jiya i yau.
Zaune take a parlor hannun ta rike da remote ta kurawa tv ido amman sam hankalin ta baya kan kallon,tunanin gamon ta da shi kawai take,raban da su kwana daki daya har ta manta,yau kuma bata san yanda abin zai kasance ba......................
Dagowa ta yi da sauri sakamakon karan faduwar abu da ta ji,ido biyu tayi da Lubna,murtuke fuska Hauwa tayi tamau dan karma ta kawo mata wargi.
Wuri ta naima ta zauna ta daura kafa daya kan daya tana hura hanci da kebe baki.
Gyara zama Hauwa tayi ta chanja tasha.
Dagowa Lubna ta yi tai ficin-ficin da ido tace"ki chanza tashar,wanchan nake san kallo ba wannan ba",ta fada tare da hade fuska tana danna wayar ta.
Dagowa Hauwa tayi da mamaki tana kallan ta tsawon minti biyu kafin ta dauke kai ta ciza leben ta na kasa tana girgiza kai.
Jin shiru yasa Lubna dagowa zuciyar ta na bugu tace"baki ji bane".
Tsit Hauwa tayi kamar bata falan.
A zuciye Lubna ta mike tana huci ta nufe ta gadan-gadan kamar za ta bige ta,a rayuwar ta babu abinda ta tsana kamar shariya.
Tana zuwa ta anshe remote din tace"tunda ba na gidan ku bane i sai ki bani".
Juyowa Hauwa tayi da mugun mamaki tana kallan ta baki bude,ganin tana kokarin barin wurin yasa ta damko rigar ta ta baya ta jawo ta gaban ta tace"ke tv na gidan ku ne,har kin isa kizo ina kallo ki amshe remote a hannu na,kina hauka ne?".
Bige mata hannu tayi tace"keh malama sake ni ban san shashanci da rashin hankali".
A mugun fusace Hauwa ta dago ta bige mata baki da hannu tace"keh ki shiga taitayin ki,wlh zan iya karya ki,bana san raini da shashanci,kuma daga yau kar na kuskura na ganki a gaban tv nan tunda bana gyatumin ki bane ko gadon gidan ku".
Tuni Lubna ta kawo wiya tana huci tace"ni kika bigewa baki? har da tsarabar zagi?".
Kishingida Hauwa tayi tana lumshe ido tace"kina da abinda za kiyi nehhh!?".
Cije baki Lubna tayi tace"ni ko ke da abin yi kuwa wlh,bari ki gani,za ki ga abinda zai faru,za ki ce na gaya miki",tana gama magana ta wuce fuuuuu! kamar zata tashi sama.
Kyabe baki Hauwa tayi tace"aikin banza yiwa kare wanka",duk abinda za ki yi dai baki isa kiyi abinda Allah bai yi ba,so a banza.
Bayan Sallar isha'i Sani ya shigo gidan,direct dakin shi ya shiga ba tare da ya naimi ko wacce a cikin su ba.
Lubna na jin ya shigo ta fito cikin wata figaggiyar riga ta nufi dakin shi,ba jimawa ya fito yana huci ya nufi dakin Hauwa.
Daure take da towel iyakar shi cinyar ta ta ji an banko kofa,a razane ta juyo tana salati.
Ba karamin Faduwa gaban ta yayi ba ganin yanayin fuskar shi kamar hadari ya hadu a gabas.
Gintse fuskar ta tayi tana kokarin kawar da yanayin da zuciyar ta ya shiga tace"Sannu da zuwa barka"..........
Daga mata hannu yayi yana huci yace"uban meh ya hada ki da matata da har kika naimi ki zage ta?".
Kallan shi ta yi ta kau da kai gefe tace"mai kuma ta ce na mata?".
Kara harzuka yayi yace"ni kike tanbaya dan ba kida kunya,ni sa'an ki ne dan uban ki".
A fusace Hauwa ta dago tace"kar ka kara zagan min Baba,babu ruwan shi a wannan lamarin,idan za kayi ka yi da ni kadai amman banda"............
Ba taga zuwan shi ba sai saukar marin da ta ji a kan kuncin ta.
Dagowa tayi dafe da kunci tana kallan shi da dinbin mamaki tace"mai nayi maka da za ka mare ni".
Ba tare da shakkah ko dar ba yace"sabida kin yiwa matata rashin kunya".
Binshi da kallo kawai Hauwa take ta kasa ko da kwakwaran motsi,sai maimaita abinda ya fada take.
katse mata tunani yayi da fadin"wlh na kara jin irin hakan ta faru a ranar sai kin gane babbancin baki da fari da kore da ja,kin dai ji na fada miki",ya fada tare da ficewa daga dakin kaman zai tashi sama.
Ba Karamin farin ciki Lubna ta shiga ba domin duk abinda aka fada akan kunnen ta.
Saurin dafa bango tayi sakamakon jirin dake kokarin dibar ta,kasa yarda da kalaman shi tayi,sulalewa tayi dabas a kasa hawayen bakin ciki na zuba daga idan ta,ta dau tsawon lokaci tana kuka ba tare da ta san abin yi ba.
A ranar kasa barcin kirki ta yi,data kwanta sai abin ya fado mata a rai,washe gari da ciwon kai mai tsanani ta farka wanda yasa ta kasa yin komi.
Waya ta lalaba da kyar ta sanarwa Maman Fauzan,ba bata lokaci ta karaso gidan da basket a hannun ta,duba agogon dake dakin ta yi taga bakwai da minti sha daya,fita ta yi ta nufi kitchen ta dau plate da spoon ta zuba abinci a ciki tana bata a baki,da kyar ta samu ta ci kadan ta bata magani sannan ta gyara mata kwanciya,a gurguje ta ba Ameen abinci sannan ta dube mai kaya ta mai wanka ta shirya shi cikin sport wear,Allah yasa Friday ne ba sai an saka mishi abinci ba,kayan kwalama kawai ta saka mishi a jaka,sallama tai mata suka fice da zummar duba ta zuwa anjima.............................
Comment
Vote
ShareBy Gimbiya Ayshu💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Исторические романы"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...