PAGE 75-76

40 10 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
             (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚

*****FOLLOW MY ACCOUNT*****

WATTPAD:Aishamaaruf1
AREWABOOKS:gimbiyaayshu2503
TWITTER: Gimbiya Ayshu
I.G: Official_gimbiya_ayshu
TIKTOK:gimbiyaayshu2503.

BOOK 1: CHAPTER 75&76

___________________________"Hajiya ki zo office dan na miki bayani",ya fada tare da ficewa daga dakin.

Da toh Mami ta amsa,daga ta Mamma ta yi ta kwantar da ita akan doguwar gujera sannan ta fice daga dakin.

Sallama ta yi a bakin kofa aka bata izinin shiga.

Nuna mata wurin zama ya yi ta zauna.

Gyaran murya yayi yace"wato Hajiya Alhamdulillah jiki yayi kyau a kan lokacin da aka kawo shi,sai dai har yanzu abin na ran shi wanda shi ne dalilin da yasa na yi mishi alluran barci wanda zai kai daga yanzu zuwa gobe kafin ya farfado,kuma insha Allah idan ya farfado muna fatan muga chanji".

"Insha Allahu Dr muma haka muke fata,amman Dr baka san dalilin shigar shi wannan halin baaa?".

Dan dariya Dr yayi sannan yace"abubuwa dayawa na jawowa,nan ya shiga mata bayani har ta gamsu".

Ajiyar zuciya Mamma ta sauke tace"aiki ya gan mu,wannan yaran da shegen zurfin ciki yake ga bakin rai kaman mutanan farko,yanzun ko ya farfado idan an tanbaye shi cewa zai yi babu komai,mu kam Allah ya hada mu da jaraba",ta fada tana tafa hannu.

Dariya Dr yayi yace"ba haka bane Hajiya ku lallabe shi,nan ya fara bata shawarar yan da za su yi har a samu ya fadi matsalar shi".

Dariya Mamma tayi tace"likita bokan turai wannan shawarar taka tayi, insha Allahu za'ayi aiki da shi,Allah ya tashi kafadun shi",a tare suka amsa da Ameeeen.

Ko da Mamma ta koma dakin ta iske Mami har ta yi barci.

Yanzu satin Hauwa daya a gidan miji,sossai suke shan soyayyar su ba kama hannun yaro.

Tana san kiran Mami amman babu waya a hannun ta dan har lokacin ba'a kawo mata wayar ta ba.

Tana cikin wannan tunanin ta ji sallamar Ummi.

Ihu Hauwa tayi ta daka tsalle ta rungume ta tana kukan murna.

Dariya Ummi tayi tace"wato har yanzu baki girma ba kina nan da halin ki".

Murmushi Hauwa tayi tace"wlh nayi kewar ku sossai barin ma Mamana,ya take?".

Dariya Ummi tayi tana daga gira tace"fada gaskiya dai ni banga alama ba,kin ga yanda kika wani kara fresh da girma a cikin sati daya kachal,umm ummm gaskiya oga na aiki".

Daka mata duka Hauwa tayi tana bubbuga kafar ta tace"kai Anty Ummi ni fa banyi komai baaaa!",ta fada tana bubbuga kafa.

Dariya Ummi tayi ta zauna kan kujera tace"i'in Amarya dakin ki yayi kyau Allah yasa mu a danshin ku".

Ko kula ta Hauwa bata yi ba ta shige kitchen tana turo baki,ba jimawa ta dawo hannun ta rike da babban tray.

Ajiye mata shi tayi tace"bismillah ga shi ki dan taba".

Dariya Ummi tayi tace"un ga ni a gidan Hajiya Hauwa waii".

Bubbuga kafa Hauwa tayi tace"dan Allah Anty ki bari manaaaa".

Dariya Ummi tayi tace"ga wayar ki ta fada tare da mika mata wayar".

Amsa Hauwa tayi fuskar ta dauke da farin ciki.

Duba balance din ta tayi taga akwai kati sossai a ciki.

Ba bata lokaci ta lalabi number Mami ta danna mata.

Tagumi Ummi tayi tace"ohhhhh! ni daga kawo miki waya,sai kace dama jira kike".

Dariya Hauwa tayi tace"baza ki gane ba".

Fitowar Mami daga bayi kenan taga wayar ta na ringing,da sauri ta karasa ta dau wayar ba tare da ta duba sunan da ke rubuce a kai ba ta kara a kunne ta yi sallama.

Amsawa Hauwa tayi fuskar ta dauke da tsantsar farin ciki idan ta cike da hawaye.

Kara bude idan ta Mami tayi ta cire wayar ta duba sunan ta mayar,murya a sanyaye Mami tace"Daughter ykk ya gidan naki ina fatan komai lafiya?".

Amsawa Hauwa tayi idan ta na tsiyayar da ruwan hawaye,bayan sun gama gaisawa tayi tanbayar Anty Jameela da Ya Jalal,ajiyar zuciya Mami ta sauke tace"sai dai muce Alhamdulillah,Jalal ba lafiya,tun randa aka daura auren ki aka kwantar da shi sai yau Allah yasa ya farfado,insha Allah kila nan da kwana hudu zuwa biyar za mu koma gida.

Baki na rawa Hauwa tace"toh mai ke damun shi Mami,mai nene matsalar shi"?.

Ajiyar Zuciya Mami ta sauke tace"Allah ne masani amman ni na kasa gane kan Jalal,idan ma na tanbaye shi ce min yake babu komai ban san ya zan yi da shi ba ban san mai zan mishi baaaaa!,ta fada hawaye na zuba daga idan ta".

Lumshe idan ta Hauwa tayi hawaye na gangarowa,sossai take jin zafin hawayen da Mami ke yi.

Sai data dai-dai ta kan ta sannan ta kwantarwa Mami da hankali.

Sossai kuwa hankalin ta ya kwanta har take ji kaman kashi 60 daga cikin damuwar ta ya kau.

Sai da Jalal ya kara sati daya a Asibiti kafin aka sallame shi.sossai jikin shi yayi kyau sai dai har lokacin ya ki fadawa kowa damuwar shi,Mami tayi-tayi amman ya ki gaya mata wai bai da wani anfani ko ya fada.

Jalal ko dai matar ka ce baka jin dadin zama da ita?.

Murmushi Jalal yayi yace"a'a Mami ko kadan ba haka bane,damuwata bai da hadi da Jameela,ko kadan bata min komai ba".

"Mami ko na gaya miki bai da wani fa'ida a yanzu dan is too late,kawai ki taya ni da Addu'a Mami Allah ya bani ikon dangana".ya fada tare da ficewa daga dakin ya nufi nashi.

Bin shi da kallo Mami tayi har ya fice.

Ajiyar zuciya Mami ta sauke tace"Allah ya maka magani ya baka ikon dangana ya zabar maka abin da ya fi zama alkairi Ameeeen".

Dai-dai nan Mamma ta shigo tace"ina yake?".

Ajiyar zuciya Mami ta sauke tace"ya wuce dakin shi".

"Kina nufin bai gaya miki ba?".

"Girgiza kai Mami tayi alamun ehhhhh".

Girgiza kai Mamma tayi tace"wanna yaran naki sai ke ni kam bazan iya ba".

Bayan sallan la'asar zan koma tunda Alhamdulillah jiki yayi sauki.....................................

Comment
Vote
   &
Share

By Gimbiya Ayshu 💞💞💞.



🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now