🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
https://www.wattpad.com/user/AishaMaaruf1?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🖕
Follow me on whattpad
BOOK 1:CHAPTER 25&26
__________________________Kin yarda da batun su Mami tayi tace"Wlh ni babu ruwana,in dai har baza kuzo muci tare ba toh nima ba zanci ba",ta fada tana kawar da kai gefe.
Dariya Hauwa tayi ta rungume Mami tace"kai Mamina fushi kike damu".
Girgiza kai Mami tayi tace"tabbas zanyi fushi in dai baku yarda munci tare ba".
"Toh shikenan Mamina za muci,yi hakuri kar kiyi fushi damu",ta fada tana rike kunnuwan ta duka biyu.
Kinji Mamin mu yi hakuri za muci kinji ta fada itama tana rike kunnuwan ta.
Murmushi Mami tayi tace toh shikenan oya ku dau chokali.
Dariya duk su kayi suka mike.
Mama dake tsaye a kofar kitchen tun lokacin da suka fara dramar su tayi murmushi ta dauke hawayen da suka gangaro mata ta karaso gare su.
Ahhh! Yaran Mami ina zaku ku bar Mamin ku.
"Wlh Mama cewa tayi idan ba muci abinci tare da ita ba za tayi fushi damu",cewar Ummi.
Murmushi Mama tayi tace"toh shikenan je ku dauko chokalin".
Zama Mama tayi a kan tabarma tace"sannu Mami,sun dame ki da surutun su kohhh!".
Dariya Mami tayi tace"a'a ba Mami za kice min ba,cewa za kiyi Yaya",ta fada tana murmushi.
Dariya Mama tayi tace"toh shikenan Yaya".
Dai-dai nan su Hauwa suka dawo,zama su kayi suka saka Mami a tsakiya,Hauwa tace"Bismillah Mamin mu mun dau chokalin".
Yauwa yarana muci ta fada tana daukan chokali.
Nan suka fara cin abinci.
Tagumi Mama tayi tana kallan su,hawayen dake kokarin zuba daga idan ta tayi saurin hadiyewa.
Hakika Mami mutun ce,babu dangin uba ba na uwa amman take gwada musu tsantsar son da babu mix din algush a ciki,ko jini daya ta hada da Mami iyakar son da zata gwada mata kenan........
Katse mata tunani Mami tayi da fadin Maman yarana,baza kici abinci ba,kin tasa shi a gaba kin buga uban tagumi,
mai ya faru?.Murmushi Mama tayi tace"wlh babu komi kawai dai abu na tuna".
Kallanta Mami tayi tace"anya",ko dai baza ki fada min bane.
"A'a wlh ba haka bane,i kin wuce komai a guna,wlh babu komi".
"Toh shikenan tunda kince haka".
Bayan sun kammala cin abinci su Hauwa suka tattara kwanonin suka kai kitchen.
Sai wurin shida Mami ta shirya tafiya.
Mama tace"Yaya wannan kayan abincin fah mai za ayi da su?".
Dariyar tanbayar da Mama tayi mata tayi sannan tace"inba ke bahhh! fisabillilahi mai akeyi da abinci".
"A'a wai ba haka nake nifi ba,gani nayi abincin sunyi yawa,kuma idan nace ki barshi ba bari za kiyi ba kuma babu dadi mutun yayi maka kyauta ka maida mishi,shine nace mai zai hana a dan rage,dan naga sunyi yawa wlh"
"Ohhhh!" Idan na fahimce ki kina nufin sun yi kadan kohhh!,toh babu damuwa insha Allah zan sa a karo linkin wannan,nasan zasu isa kohhh!,ta fada tana daga gira.
"A'a wlh ba haka nake nufi ba,ina nufin a rage ne".
"Ohhhh!" Kin raina bari na kira nasa a karo.
A'a Hajiya barsu an gode Allah anfana ya karo arziki mai anfani,Allah ya bar zumunci mai dorewa yayiwa iyaye Albarka.
Da Ameeen Ameeen Mami ta amsa tace"ko keh fah,abinda ya kamata kiyi kenan tun dazu ba wai kice sunyi yawa ba,ni a wuri na sunyi kadan wlh".
Murmushi Mama tayi suka rakata har bakin Mota inda driver ke jiranta.
Gaisawa Hauwa tayi da Driver yayi mata ya jiki tare da fatan samun sauki.
Yauwa daughter kiyi zaman ki har sai kinji sauki kinyi garau kinji,infact na baki sati daya.
*****BAYAN KWANA BIYU*****
Sossai Jalal yaji ba dadi rashin ganin Hauwa da bai yiba kwana biyu,yaso tanbayar Mami amman nauyi da kunya ya hana shi.
"Toma shi ina ruwan shi da yarinyar ne,akan meh zai dinga tunanin ta har yana damuwa da ita".
"Mtswwww",ni babu ma ruwana da ita ina da matata kuma ta fita kyau,girma, ilimi,kudi kai da komai ma ta fita,ya fada yana kulle idan shi tare da gyara kwanciyar shi ya kulle ido.
Yana kulle ido yaga hoton Hauwa kawai yake gani lokacin daya take mata kafa tana kuka.
Tsaki yaja ya kara gyara kwanciya yana kulle idan shi da karfi dan dai kar ya ganta amman abin ya chitura,"dan da duk ya kulle ido ita yake gani".
"Karshe dai haka yayita tunanin ta har barci ya dauke shi".
Zaune Hauwa da su Mama suke a tsakar gida suna hira wani yaro ya shigo da sallama yace"ana naiman Hauwa'u inji wani a waje".
Yaron na gama magana baiko jira amsar su ba ya fita waje da gudu abinshi.
Gabadaya duk kallan Hauwa su kayi.
Marmar tayi da ido tace"Mama wlh ni bansan ko waye bane,ni ban".............
Daga mata hannu Mama tayi tace"ni ban tanbayi ba'asi ba,tashi kije amman ki kuka ki rike mutuncin kanki".
Turo baki Hauwa tayi ta mike a zuciyar ta tace"badai wannan dan rainin hankalin bane yazo,iko in shine sai nayi mishi rashin mutunci iya san rai dan yanzu gidan mu yazo ba gidan su nake ba da yake min iskanci da gadara iya san ran shi".ta fada tana fari da ido.
Tana fita ta jingina da bango tare da harde hannayen ta a kirji ta bashi keya.
Murmushi gayen yayi yace"Assalamualikum barkanki da wannan lokaci Gimbiyar Mata".
Saurin juyowa tayi tana kallan shi da dinbin mamaki.......................
Toh masu karatu wa kuke tunanin yazo wurin Hauwa?.
Ina jiran amsar ku a comment
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Fiction Historique"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...