PAGE 13-14

68 11 1
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
               (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 13-14

_______________________"Tun karfe shida da rabi Hauwa tazo gidan Hajiya",bayan sun gama breakfast suka daura da abincin tarban Son.

Anyi abinci kala-kala,Zobo,kunun Aya fruit juice da dai sauran su,sai da aka cika dinin tab har babu masaka sinke.

Basu suka gama girki ba sai wuraran sha biyu.

Daki Mami ta shiga ta fito hannun ta rike da Abaya kalan baki,an mishi Ado da stones sai kyalli da daukan ido yake.

Bude dakin Hauwa tayi taga bata ciki,ba tare data sauka down stairs ba ta kwalawa mata kira,ba jimawa ta hauro,mika mata kayan Mami tayi tace"je kiyi wanka ki chanza kayan nan".

A'a Mami ba sai na chanza ba wannan na jiki na ma yayi,"ita ba komi ke daga mata hankali ba face gargadin da Mama tayi mata".

Binta da kallo Mami tayi tace"Mama ta hanaki amsa kohhh!".

"Daga mata kai Hauwa tayi a hankali".

Murmushi Mami tayi tace"hakan da Mama tayi dai-dai ne,duk wata uwa ta gari abinda zata ce kenan",amman kisa wannan sabida bakin da zamuyi,kinga in kin tashi tafiya sai ki cire sabida kar Mama ta miki fada.

Murmushi Hauwa tayi alamun gamsuwa ta amshi kayan ta nufi dakin ta.

Binta da kallo Mami tayi tana murmushi.

"Kwance Hauwa take akan doguwar kujera tayi rubda ciki tana kallo kanta daure da gyalan kayan".
"Jin alamun saukowar Mami yasa Hauwa mikewa ta zauna".

Murmushi Mami tayi tace"yar gidan Mami kinyi kyau sossai,kaman dan ke aka yi kayan nan.

Dariya Hauwa tayi ta rufe ido da tafin hannun ta tace"Nagode Mami".

Zama Mami tayi tana jiran kiran Jalal.

Bayan kaman minti goma taji alamun shigowar message,duba wayar tayi da sauri,a fili ta furta na sani i,dan rainin wayau kawai,wai shi bin ka'ida bai phone call a jirgi,kai wannan yaran sai a hankali.

Tashi Mami tayi ta nada kyalan jikin ta da kyau ta dau jakar ta.

"Hauwa na ganin haka ta kwanta tana  gyara kwanciyar ta".

Ko da Mami ta juyo ta ganta a kwance,sakin baki Mami tayi tace"ya haka,ya da gyara kwanciya,common tashi tare zamu tafi tarban su".

Tashi Hauwa tayi tana murna amman bata bari ya fito fili ba,dama tana son ganin airport,toh ga dama ta samu.

"Toh Mami bari na saka hijabi",ta fada tana kokarin nufan upstairs.

Dakatar da ita Mami tayi da sauri tace"wani hijabi kuma ana zaune kalau",zo muje,shigar ki yayi ba wani matsala tunda ba matse ki kayan yayi ba.

"Unnnm Mami kaina babu wula fahhh!".

Murmushi Mami tayi tace"duk salan doje ma zuwa ne,i nasan maganin ki".
Jeki dakina ki duba drawer akwai hulluna ki zabi daya.

Murmushi Hauwa tayi a zuciyar ta tace"bakisan zumudin da nake ba Mami,har na kosa na ganni a airport.

Dawowa tayi hannun ta rike da hulan

Kallan ta Mami tayi tace"ikon Allah hulan kuma yace kar asa shi ne,"Oni!" Allah ya hada ni da yara kala-kala,ba ke ba ba Jalal ba,zan sha fama".
Yi dai mu tafi ya na iya dake.

"Dariya Hauwa tayi ta saka hulan ta yafa gyalan daya tsaya mata dai-dai wiya".

Bayan kaman minti sha biyar suka isa Airport.

Basufi minti biyar da isa Airport ba jirgin su ya sauka.

Sai wulwulga ido Mami take tana naiman inda zata hango su.

Tana juyawa tagan su,murmushi Mami tayi tace"gasuchan daughter".

"Gasuchan kuma?,su su nawa kenan?",

Bata gama tunanin datake ba taji Mami na fadin oyoyo sannun ku da zuwa ya hanya,ta fada tana rungumar matashiyar budurwar dake kusa da guy din data tabbatar yaran Mami ne,dan taga kamanni sossai.

A sanyaye tace"sannun ku da zuwa".
Matashiyar budurwa ce kawai ta amsa tace ykk?.

"Alhmd ya hanya".

"Lfy lau Alhmd".

Bin Jalal Mami tayi da kallo jin bai amsa ba.

"Jalal bakaji ana gaida kai ba"

Juyowa yayi ya kalli Mami ranshi a hade yace"naji Mami".

"Toh mai ya hana ka amsawa,ko dai salan iskancin ka ne ya taso?".

Shiru Jalal yayi zuciyar shi na tafarfasa ba tare daya ko kalle taba yace"Hy" yayi gaba abinsa.

Bin shi da kallo Mami tayi ranta a mugun bace,ta rasa wani irin hali Jalal yake da shi,sam bai gadi halin ta ko na Baban shi ba.

Wani makirin murmushi yarinyar dake kusa da Mami tayi murya chan kasa tace"Good".

Ganin har ya shiga mota yasa Mami tayi kwafa ta rike hannu Hauwa suka tafi.

Driver na gama parking ya balle marfin motar ya fice.

Har ya kai kofar parlor Mami tayi magana strictly tace"what the hell is wrong with u Abduljalal?,bana san irin abin da kake,ba kada niyyar dawowa ka dawo,kayan da ka bari ni zan kwaso maka shi,ka kiyaye ni fahhh! Abduljalal ranka zaiyi mugun baci",tana gama magana ta nufi parlor fuuuui! kaman zata tashi sama.

"Bin bayan ta Hauwa tayi dan ta kwanyar mata da hankali ta lallashe ta.

"A tsanyaye ya dawo wurin motar ji yake kamar zuciyar shi zai fashe,wani irin bakin ciki ne ke cin shi,sossai yake jin tsanar wannan yarinyar da a saboda ita aka mai fada da girman shi...............................

Chakwakiyar haduwa

Hate at first site

Hmmm muje zuwa masu karatu

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now