PAGE 23-24

61 12 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 23&24

__________________________Sai da Mami ta musu siyayyan kayan abinci sossai kafin suka kama hanya,parking su kayi a kantin mai fruit,ta siya laimu,pineapple,apple da dai sauran su,an cika black and yellow laida biyu da fruit.

Tafiyar minti goma su kayi suka isa.

Yaran unguwar Mami ta tara suka kwashi kayan zuwa cikin gidan.

Zaune Mama take a tsakar gida tana gyara wake,jin an turo kofa ba izini yasa ta dago taga ko waye,Bude baki tayi tsabar mamaki,sai da suka gama jibge uban kayan kaf kafin Mami ta sallame su tayi sallama a bakin kofar,Mama da mamaki ya  gama kashe tane ta amsa sallamar jikin ta a mace.

Tarban ta tayi da mutunci ta shinfida mata tabarma,daki ta shiga ta dauko mata ruwa mai sanyi a gora da cup,bayan ta ajiye ta zauna suka gaisa.

Siyaya ruwan Mami tayi ta sha sossai.

Murmushi Mama tayi ganin yanda matar ta sha ruwan babu kyama.

Nazo na zauna na kwankwadi ruwa ba tare da nayi bayanin kaina ba.

Murmushi Mama tayi tace"ayyyah babu komi wlh,i sai da natsuwa ake komi".

Nan Mami tayi mata bayani tare da fadin ya jikin Hauwan ina take.

Sossai Mama ta yaba da karamcin matar.

Tana daki,bari na duba ta,ta fada tana mikewa tsaye.

Har ta kai bakin kofa Mami tace"in dai tayi barci dan Allah kar a taso ta,ni da kaina zan karaso na duba ta.

A kwance ta sameta a kan gado ta kishingida da jikin gadon tana kallon tashar Arewa24.

Ahh ba kiyi barcin ba.

"Ehhh! Mama wlh na kwanta barcin yaki daukana shine na zauna kallo".

Toh shikenan kin kyauta,ga Hajiyar ki nan tazo.

"Mama kina nufin Mamina".
Girgiza mata kai tayi alamun tabbatarwa.

"I da sauri Hauwa ta sauko daga kan gadon ta nufi sakar gidan da gudu,tama manta da wani batun kafa".

Uh
Tana zuwa ta fada kan Mami ta rungume ta sossai tana murna tace"oyoyo Mamina Oyoyo Mamina,nayi missing dinki sossai Mamina.

Murmushi Mami tayi tace"miss u too more my daughter".

Mama dake tsaye a bakin kofa tana kallan su tace"Allah mai iko,jibe su kamar sun shekara basuga juna ba,ashe dama a cikin masu kudin yanzu akwai wa'inda ba suda bakin hali,tabbas ta ganewa idanta,matar nan ta ciri tuta.

Jan kafarta tayi a hankali ta karasa ta zauna.

Dai-dai nan Ummi ta shigo bakin ta dauke da sallama.

Tsayawa tayi turus tana kallan su,chan kuma ta karaso,ta gaida Hajiya tare da Mama ta shige kitchen ta ajiye aiken da  Mama tayi mata ta dawo ta zauna kusa da Mama tana kallan Hauwa data makale matar tana mamakin inda tasanta da har ta wani makalkale ta haka.

"Anty Ummi kinga Mamina".

Zaro ido Ummi tayi hakoranta kamar gonar auduga,"tunda take duniya bayan iyyenta da sis babu wanda take so kaman Mami,sai gashi yau gata ga Mami".

I bata san lokacin data daka tsalle ta fada kan Mami ta rungume taba tace"Maminmu Maminmu,Maminmu oyoyo,oyoyo Maminmu,Mamin mu ina sonki sossai sabida kina san Hauwar mu".

Dariya kawai Mami ta dinga yi dan ta kula yariyar akwai shirme da shiririta.

Tagumi Mama ta buga tana kallon su tace"idan kuka karyata i kun huta".

Dariya Ummi tayi tace"ko kusa Mama,i in muka karyata bamu ba zama".

Nan suka tasa Mami a gaba sunata Mata surutu.

Tashi Mama tayi ta wanke waken ta ta zuba a ruwan daya tafasa.

gyara kayan miya tayi ta fara jajjage.

Sossai Mami ta saki jiki da su tana hira,(tana mugun san yaran barinma Hauwa,ko dan ba tada yara mata ne oho,amman yaran sun mugun shiga ranta kamar Mama ta bata su.

Sai wuraran uku Mama ta gama girki,ta sakawa Mami a plate da spoon ta kawo,daki ta shiga ta dauko mata jug din zobo da cup.

Allah sarki yar uwa nagode da dawainiya,Allah bar zumunci.

Ummina tashi ki dauko muku spoon muci tare

"Girgiza kai Ummi tayi tace kici Mami zamuci namu yanzu..........................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now