PAGE 81-82

49 9 0
                                    

🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION📚

BOOK 1: CHAPTER 81&82

_________________________Murmushi Ammi tayi tace"idan kin gama rawar sai ki saurare ni".

Dariya ta yi tai tsalle ta dira a gaban Ammi tace"gani Ammi na,baza ki gane bane,wlh farin ciki nake sossai dan na kusa zama Mama wlh",ta karasa maganar ta tana dariya.

Rike baki Ammi tayi tace"naga abinda ya ishe ni,sannu su Mama manya".

Murmushi kawai Hauwa take har lokacin kanta na kasa.

Ni dai tashi ki dauko hijabi kizo na aike ki.

Mikewa tayi da sauri tana tsalle tace"toh Ammi,i kuwa yanzu zan biya gidan su Rahma na gaya mata cewa na kusa zama Mama,kila ma mu dawo tare",ta fada tare da shigewa daki.

I kuwa zanci mutuncin ki in har kika kuskura kika gaya mata,keh ba ma ita ba,bana san kowa ya ji har sai cikin ya girma,ina fatan kin jini.

Girgiza kai kawai tayi ba tare da ta furta komai ba tana turo baki.


*******BAYAN WATA UKU*******

A yanzu cikin Hauwa na da wata biyar,sossai cikin yayi mata kyau ya zauna das a jikin ta,ta kara haske da cika kaman an hura ta.

Zaune take akan one seater hannun ta rike da remote tana kallo.

Turo kofar da aka yi ne yasa ta juyawa ta kalli bangaran, murmushi tayi tace"Hayati oyoyo",ta fada tare da mikewa tsaye.

"Oyo Orobo ta",ya fada tare da fashewa da dariya.

Tsayawa Hauwa tayi ta bata rai tace"Ayyyahhh nace maka bana san sunan nan kohhh!"ta fada tana bubbuga kafa a kasa.

Da sauri ya karasa gaban ta ya rike ta yace"kai zaki jiwa kanki da baby na ciwo,baki san wannan abin da kike zai iya affecting baby na baaaa",ya fada tare da kashe mata ido daya.

Dariya Hauwa tayi ta boye fuskar ta a jikin shi.

Zaune Jalal yake a parlor hannun shi rike da waya amman gaba daya hankalin shi ba kan wayar take ba,tunanin sabon sauyin da Jameela ta bullo da shi yake,shi dai iya sanin shi da ita bata cin alaiyahu,bata sha pineapple,bata cin soyayyan kwai,amman yanzu duk tana cin su,inko bata ci ba toh ranar ba barci har sai an bata shi,ga wani shegen kasala da take fama da shi,in ko dare yayi ba barci jikin ta zai yi zafi kaman a kunna mata wuta amman da zaran garin Allah ya waye shikenan kuma zaka naimi zafin jikin ka rasa,tun yana jurewa har ya kasa,wata daya kenan ana fama da abu daya,yayi yayi suje asibiti taki gashi Mami bata nan balle ya sanar mata,duk abin ya bi ya daure mai kai,amman dole suje asibiti yau ko taki ko taso.

Mikewa yayi ya nufi upstairs dadan gudu-gudun shi ya tura kofar dakin ya shiga,ganin bata dakin yasa shi zama bakin gado,a tunanin shi ta shiga wanka ko kuma toilet,chan ya ji kamar kakarin amai,kara kunnan shi yayi da kyau dan ya tabbatar da abinda ya ji,da sauri ya mike ya nufi bayin.

Dai-dai ya turo kofar ita kuma ta fadi sabida ta mugun galabaita.

Da sauri ya karasa inda take yana Kiran sunan ta amman shiru kake ji ba amsa"kamam mushriki ya ci shurwa ya sha ruwa".

Tashi yayi da sauri ya hada ruwa mai zafi yayi mata wanka ya nade ta a towel ya fito da ita,bude drawer yayi ya dau dogon riga mara nauyi sannan ya bude dayan bangaran ya dau pant ya shirya ta,Hijabin ta dake kan gado ya dauka ya saka mata ya kinkime ta ya nufi mota da ita.

Cikin mintinan da basu fi minti goma ba suka isa asibitin sabida gudun da ya sharar.

Da sauri aka amshe ta aka nufi  emergency room da ita,nan aka fara bata taimakon gaggawa.

Wuri Jalal ya samu ya zauna ya rike kan shi da hannu biyu idan shi cike da hawaye,Addu'a yake Allah ya tashi kafadun ta,baya so ya rasa ta a dai-dai gabar data fara zama mutun.

Sai bayan minti arba'in kafin Dr ya fito yana sharce zufa yace"Abduljalal kwantar da hankalin ka,munyi nasarar ceto rayuwar ta sai dai bamu gama sanin matsalar ta ba amman yanzu za'ayi dan gwaje-gwajen daya kamata".

Ajiyar zuciya mai karfi Jalal ya sauke yace"nagode Dr amman dan Allah zan iya ganin ta".

Murmushi Dr yayi yace"gaskiya ba zai yu ka ganta yanzu ba sai anjima idan ta farfado".

Komawa Jalal yayi ya zauna tare da lumshe ido.

Bayan awa daya Dr ya kira Jalal inda ya Shaida mishi cewa matar shi na dauke da ciki.

Mutuwar zaune Jalal yayi,sai da yayi minti biyar a haka kafin ya dawo hayyacin shi yace"dan Allah Dr da gaske kake".

Murmushi Dr yayi yana dan rubuce-rubucen shi yace"bayan ta ji sauki za'a mata scanning dan musan watannin cikin",ya fada tare da linke paper dake hannun shi ya mika mai.

Amsa Jalal yayi still ya kasa gasgata maganar Dr har sai da ya karan ta paper da kanshi kusan sau biyar.

Da misalin Tara na dare Jameela ta farka,da sauri ya danna alarm din dake gefen shi,ba bata lokaci wata Nurse ta shigo,nan yace"ta farka a kira Dr".

Bayan Dr ya zo yayi dan dube-duben shi sannan ya cire mata drip din daya kare yana kokarin saka wani.

Yamutsa fuska tayi tace"I want to use the toilet".

Dakatar da saka mata drip din yayi yace"ka kaita idan ta gama sai ka dannan bell duk Nurse din da ta zo sai kace nace ta saka mata drip.

"Okh Dr mungode".

Bayan ta gama abinda za tayi ta dauro alwala suka fito tare ya shinfida mata darduma ta zauna ya saka mata hijabi,sai data rama sallolin da ake bin ta kafin ta mike ya taimaka mata ta koma kan gado ya saka mata pillow a bayan ta ta jingina,tea mai kauri ya hada mata sannan ya hado mata da kwai da bread,sai data cinye kwan sannan ta sha tea kwantan cup tace ta koshi.

Bell ya danna wata Nurse ta shigo ta saka mata drip din.

Hira suka dinga yi bayan fitar Nurse har barci ya dauke ta....................................

Kuyi hakuri da wannan.

By Gimbiya Ayshu 💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now