🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AYSHU💞💞💞ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
BOOK 1:CHAPTER 65&66
_________________________Bige kanta tayi da bango ta fadi a nan kasa sumammiya,ficewa Abba yayi daga gidan ya kwashe yaran shi ya maida su gidan Amaryar shi,yana ajiye yaran ya juyo da niyyan kwashe kayan su.
Yana shiga bai ko bi ta kanta ba ya shige dakin yaran ya hada kayan su a akwati ya ja shi ya fito,har ya gifta ta sai ya ga kaman bata motsi,dakatawa yayi ya juyo ya kalle ta yaga dagaske bata nunfashi,ijiye akwatin yayi ya juyo gare ta ya saka yatsar shi biyu dai-dai hancin ta yaga bata nunfashi,juya ta yayi ya jijjiga ta ya kira sunan ta amman shiru,daukar ta yayi ya fice daga gidan da ita ya nufi bakin titi,bai jima da tsayuwa ba ya sami abin hawa ya gaya mai inda za shi.
Bayan minti ashirin suka isa,nan aka amshe ta da gaggawa aka nufi bata kulawa dan a cece rayuwar ta.
Bayan tsawon minti talatin wani doctor ya fito daga dakin da aka kwantar da ita.
Da sauri doctor ya nufe shi yace"kai ne mijin wannan patient din".
Girgiza kai Abba yayi yace"ehhhhh! nine Doctor ta farfado ne?".
Sharce zufa doctor yayi yace"mun yi nasaran ceto rayuwar ta sai dai ta samu buguwa a cikin kanta sakamakon buguwar data yi".
Da baya da baya Abba ya ja ya zauna a kujerar dake bayan shi ya dafa kan shi da hannu biyu yana daya sanin abin da yayi,ya dau tsawon lokaci a haka kafin ya mike ya wuce gida sabida bata farfado ba.
Yana shiga cikin gidan ya kulle duka dakunan gidan ya ja akwatin ya fice da shi ya kulle gidan.
Zaune yake akan doguwar kujera ya rike kan shi da hannu biyu idan shi yayi ja sossai har wani kyali-kyali yake sabida hawayen dake kwance a ciki.
Dafa shi Zaituna tayi tace"Abban yara mai ya faru ya na gan ka haka",ta fada tare da zagayowa ta zauna gefen shi ta kwatar da kan shi akan kafadar ta tana lallashin shi,sai data tabbatar hankalin shi ya kwanta sossai kafin ta tanbaye shi silar shigar shi damuwa.
(Mata yana da kyau idan miji ya shiga damuwa ki kula da shi ki rarrashe shi har sai kin tabbatar hankalin shi ya kwanta,yin hakan na karawa mace daraja da kima kuma yana linka soyyayar mace a zuciyar mijin ta,mata a kula,wasu matan sai kaji sun ce"un ni kyale ni,ba zan iya ba ya je chan ya ji da damuwar shi shi ya sani,toh kina tafka babban kuskure baki sani ba,mata ku kula,rashin nuna kulawa ga miji shi ke sa wasun su kara aure,wasu matan da zaran sun haihu sai su tattara soyayyar miji su ajiye a gefe,dan an yi magana sai tace"yaro na yaro na",hakan ba karamin bata ran miji yake ba,ku kula mata,ba'a ce kar ki so dan ki ko yar ki ba a'a ki nuna mishi so da kauna kamar yanda aka fara tun farko,yauwa sauran ba sai na fada ba kun san yan da za kuyi,wacce bata sani ba kuma ta iya naiman karin bayani).
Nan ya labarta mata komai ba tare da ya boye ba.
Nan ya gaya mata abin da ya faru ba tare daya boye komai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah sarki banji dadin hukuncin da ka yanke ba sam,i dama zaman aure sai da hakuri,nan ta fara kwantar mai da hankali tare da nusar da shi har ta samu ya mayar da ita dakin ta".
(Duniya idan ka auri mata ta gari ka huta wlh).
Bayan wata hudu da yan kwanaki ta warke sai yan abubuwan da baza'a rasa ba.
Sossai ta shiga taitayin ta dan tana gudun tayi wani abu da zai taba Auren ta,duk iskancin ta da rashin kunyar ta tana tsoron Auren ta ya mutu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda aka ja shekaru.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Tiểu thuyết Lịch sử"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...