PAGE 127-128

52 6 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

BOOK 1:CHAPTER 127-128

___________________________Bayan tafiyar Hajiya Mama ta zaunar da Hauwa ta ce"ina san ki bani labarin zaman auren ki tun daga farko har karshe,ban yarda ki boye min komi ba,kin ji na gaya miki",ta fada tare da jan kunnen ta.

Zaro ido Hauwa ta yi tana tunanin abinda za ta ce.

Murya a kausashe Mama ta ce"wlh zan ci mutuncin ki,ina wasa da ke ne?,ba magana nake miki ba?".

Girgiza mata kai ta yi hawaye na zuba daga idan ta,bayan hannun ta tasa ta share hawayen sannan ta fara bata labari tun daga ranar da aka kai ta gidan har zuwa dukan da ya mata na karshe.

Duk iya juriyar Mama na ganin ta tsayar da hawayen idan ta sai da abin ya citura,sosai ta yi kuka domin abin ya taba ta,bata taba tunanin abin ya kai har haka ba,murya na rawa Mama ta ce"mai yasa kika rufe ni Hawa'u?,mai yasa baki gaya min ba tun far"..........kuka ne ya kufcewa Mama.

Tashi Ummi ta yi ta bar dakin,dan idan ta cigaba da zama Allah dai ya san abin da zai faru.

Da rarrafe Hauwa ta karaso gaban Mama ta hade hannayen ta tana kuka ta ce"ki yi hakuri Mama,na san na yi laifi,ban yi hakan dan na rufe ki ba,na ki gaya miki ne kawai sabida ban san hankalin ki ya tashi,kuma na yi hakuri ne dan a tunani na wata rana sai labari,kuma ke kika hore ni da yin hakuri,ke kika ce nayi hakuri a gidan mijina,na rike sirrin shi duk rint"..............kuka ne ya ci karfin ta.

Dago ta Mama ta yi ta rungume ta tana lallashin ta,sun dau tsawon lokaci a haka,da kyar Mama ta samu ta tsayar da hawayen idan ta sannan ta dago Hauwa ta ce"shikenan Allah yasa hakan shi ya fi zama Allhairi,Allah kuma ya saka miki chutar daya miki,ki yi hakuri,Allah na tare da masu hakuri,tashi muje ki watsa ruwa".

Mikewa Hauwa ta yi ta fara cire rigar ta,rintse ido Mama ta yi sakamakon ganin shaidan duka duk a jikin ta,shanye hawayen dake kokarin zubo mata ta yi ta fice daga dakin.

Bayan kwana biyu da dawowar ta gida ta kira Maman Fauzan,ba karamin farin ciki Maman Fauzan ta yi ba jin Hauwa ce,har kuka sai da ta yi,murya na rawa ta ce"ina kika shige Hauwa?,mai ke faruwa?,mai yasa kika bar gidan ki?".

Murmushi Hauwa ta yi ta ce"abinda aka saba ne Anty,ke kin san komai i,kar ki damu zan baki labari da zaran na dawo".

Girgiza kai kawai ta yi ta kasa amsawa,da haka su kayi sallama.

Ummi dake tsaye a bayan ta ta ce"ina za ki koma?".

Juyowa Hauwa ta yi a tsorace dan bata yi tunanin da mutun a dakin ba,a dan daburce ta ce"gidan mijina mana",ta karasa tana turo baki.

Dariyar shakiyanci Ummi ta yi tana tafa hannu ta ce"wani mijin,ko kin kuma aure ne ban sani ba".

Gyra zama Hauwa ta yi tana kallan ta da alamun mamaki,chan kuma ta ce"ban gane mai kike nufi ba?,Abban Ameen ne baki sani bahh?,ko kuma kin manta shi ne".

Gyra tsayuwa Ummi ta yi ta ce"au na manta fahhh!ashe ban gaya miki ba,yanzun ba ki da aure".

A rikice Ummi ta mike ta ce"whatttttt!",dafe bango ta yi sakamakon jirin dake kokarin kwashe ta.

Dariya Ummi ta yi ta ce"kina tantama ne,gaskiyar magana kenan,tun wuri idan kin san da burbushin son shi a zuciyar ki gwara ki yi saurin cire shi,dan wlh idan har ina raye baza ki taba komawa gidan shi ba,kin dai ji na rantse,sabida haka zabi ya rage ga mai shiga rijiya",ta karasa maganar ta tare da ficewa daga dakin,tana jin kukan Hauwa amman ta yi biris da ita.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now