PAGE 107-108

49 11 2
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
               (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

BOOK 1: CHAPTER 107-108

__________________________Wannan al'amari daya bullo kai.

Washe gari tun da sanyin Asuba Ammi ta dokawa Sani kira,bayan ya daga ta fara masifa,ta inda take shiga ba tanan take fita ba,daga karshe tace"ko da wasa ban yarda kayi wannan auren ba inko kayi toh ka kuka da kan ka akan duk abinda ya biyo baya",tana gama magana ta katse kiran.

Hannu biyu yasa ya rike kan shi dake masifar ciwo ya rintse ido,kiran sallan da aka yi ne yasa shi bude idan shi a hankali ya dubi agogo.

Tashi yayi a hankali ya nufi bayi,bayan ya fito ya zira jallabiya ya nufi masallaci.

Ba shi ya shigo gidan ba sai bakwai na safe.

A kofar parlor suka kusa cin karo,da sauri Hauwa ta matsa tana zare idanuwa ta gaishe shi,ba tare daya amsa ba yayi gaba abin shi.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan tafiyar shi,a fili kuma tace"a yita zama a haka matukar ba za'a taba lafiyar jiki na dana yaro na ba har zuwa lokacin da Allah zai yaye",jin alamun bude kofa ne ya sata yin tsit ta fice kamar walkiya.

Bayan awa daya ya fito da shirin shi na zuwa shago,ko takan kulolin dake ajiye bai biba ya fice abin shi.

Bai zarce ko ina ba sai gidan su Lubna,yana parking yasa a kira mishi ita.

Bayan minti goma ta fito sanye da doguwar rigar atanfa kanta nade da gyale daya shiga da kayan.

Fuskar ta dauke da murmushi ta dube shi tace"masoyi ina kwana,ya kake ya hanya?,fatan ka iso lafiya?",ta karasa magana tana fari da ido.

Dariyar daya bayyanar da kyawawan fararan hakoran shi yayi yace"masoyiya muddin ina tare dake babu abinda zai same ni ko da ace baki kusa dani toh kina cikin zuciya ta".

Kulle fuskar ta tayi da hannun biyu tana dariya.

Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke yace"masoyiya akwaiatsala fahhhh!".

A firgice Lubna ta dago tana duban shi tace"matsala kuma!?,toh na meh?".

Jingina yayi da jikin bango ya cire hulan shi yana fifita da shi yace"Ammi na bata yarda da zanchan auren ba,kuma a gaskiya bazan iya auren ki ba muddin bata bada hadin kai ba".

Saurin dafa bango tayi sakamakon jirin daya dibe ta,a kidime ta dube shi baki na rawa,kasa furta komai tayi sai hawaye sharrrr!.

Hawaye na zuba daga idan ta ta dube shi tace"toh yanzu ya za'a yi kenan?".

Ajiyar zuciya yayi yana duba agogon dake daure a tsitsiyar hannun shi yace"abin yi kwai shine ta amince,inko taki toh sai dai mu hakura da juna".

A zabure ta dago ta kalle shi da alamun mamaki tace"mu hakura fah kace?".

Ba tare daya amsa ba yace"toh bari na tafi lokaci na tafiya".

Ko motsi bata iyayi ba har ya tafi.

Kuka ta fashe da shi tace"na shiga uku,wannan wace kalar rayuwa ce,ina murnar na kammala komai sai gashi wani matsalar ya cinno kai".

Cikin gida ta shiga ba jimawa ta fito hannun ta rike da jaka.

Zaune Sani yake a kan kujera da misalin karfe sha biyun dare yana kallan tv amman gaba daya hankalin shi ba ga kallan yake ba,tunanin yanda zai gamsar da Ammi ta amince da Auren da zai yi yake,gabadaya dabarar shi ya kare,ya rasa yanda zai bullowa al'amarin,wani bangare na zuciyar shi tace"ita kuma uban gayyar fah,gana ganin zata amince kuwa?".

Wani dogon tsaki yaja ya gyara zama yace"aikin banza yiwa Kare wanka,ko ta amince ko karta amince ni ba damuwa na bane,aure ne dai sai nayi kuma bata isa ta hana ni ba".

Wani bangare na zuciyar shi tace"Sai ka yi fa kace?,idan Ammi bata amince ba i babu yanda za'ayi ka aure ta".

Wani iska mai zafi ya furzar daga bakin shi yace"wannan shi ake kira da tsaka mai wiya".

Zaune Sani yake a shago bayan sallan la'asar yana tunanin halin da yake ciki wayar shi ya dau ruri,kamar ba zai dauka ba sai kuma ya mika hannu ya dauki wayar ya amsa kiran ba tare daya duba mai kiran ba,bai san lokacin daya mike tsaye ba fuskar shi dauke da tsantsar mamaki,duba fuskar wayar yayi dan tabbatar da mai kiran duk da ya shaida muryar,kasa magana yayi har ta gaji ta katse kiran,sai a lokacin yace"Hello ina ji,jin shiru ba'a amsa ba yasa shi cire wayar a kunne ya duba fuskar wayar,ajiyar zuciya yayi ganin ta katse kiran".

Tsalle yayi yace"ta amince,yessssss!".

Duk wainar nan da ake toyawa Hauwa ba tada labari.

A ranar Sani ya nufi gidan Baffah ya gaya mai.

Da mamaki Baffah yace lafiyar ka kuwa?,aure da rana tsaka,wai yaushe kayi wanchan da har kake naiman karowa,inaji dududu shekara uku ne da dan kai,toh auren kuma yanzu na meh,iya sanina matar ka yarinya ce mai ladabi da biyayya,ga sanin girman na gaba da ita,ba iya ni ba hatta duk yan uwanka sun shaida haka.

Tuni Sani ya cika yayi fam,jira yake a taba shi ya fashe.

Da Baffah ya lura da haka sai yace"ita Ammin naka tasan da zanchan?".

Cikin sauri ya girgiza kai yana washe baki.

Girgiza kai Baffah yayi yana jinjina girman lamarin,shi kadai yasan tunanin da yake amman babu komi zai shige mishi gaba wurin yin komai na auren.

Sallama Sani ya mai zai mike Baffah yace"ita matar taka fah ka fada mata?".

Hada rai yayi yace"tukunna dai,amman zan gaya mata".

Nazarin shi Baffah yayi sannan yace"babu komai a sauka lafiya".

Yana fita daga gidan Lubna ya fara kira,nan ya shaida mata yanda aka yi,baki har kunne tsabar murna,ji take kaman ta zuba ruwa a kasa ta sha,burin ta ya kusa ciki.

Kaman yanda Baffah ya fada hakan aka yi,yaje ya naiman mishi aure kuma an bashi har an tsayar da rana ba tare da anyi wani dogon bincike ba.

Bayan kwana biyu Sani yazo har gida ya bawa Ammi damin kudin da zata hada mai kayan laife amman taki amsa,chan cikin kasar zuciyar ta tana kin auren amman bakin ta ya mata nauyi,baza ta iya cewa komai akan bikin ba.

Ganin dagaske Ammi taki amsar kudin yasa shi naiman kanwar shi dan ta raka shi kasuwa amman fir taki,wani irin mugun haushin shi take ji tun da taji labarin,ita abinda ke bakanta mata rai shine amincewar da Ammi tayi,ji take ta tsani yarinyar tun kafin a auro ta..............................................

COMMENT
VOTE
AND
SHARE

BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now