PAGE 113-114

33 6 5
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

BOOK 1:CHAPTER 113-114

________________________Ba ita ta fito daga dakin ba har sai da ta tabbatar ya fice daga gidan.

Tana ajiye kwanonin ta daura indomie a wuta,Allah Allah take ya nuna kafin ya shigo,har indomie ya nuna bai shigo ba,plate da fork kawai ta dauka ta dauki tukunyar gaba daya ta nufi daki da shi,a nan bakin kofa ta dire kayan hannun ta ta murza makulli sabida tsaro ba dan tsoro ba.

A ranar ko da wasa bata bari sun hade ba,kwana uku ta dauka tana wasan buya da shi,da dai taga hakan ba zai fishe ta ba sai ta bari.

Tunda aka kawo Amarya ba su hadu ba,so take taga wannan Amaryar da tasa mijin ta ya manta da ita ya fita batun ta,kallo take amman rabi da kwatan hankalin ta na ga kofar dakin Amarya,turo kofar dakin tayi ta fito tana mika idan ta a kulle.

Sakin baki Hauwa tayi fuskar ta dauke da tsantsar mamaki.

Tana bude idan ta tayi ido hudu da Hauwa,ba karamin rikitata kyawun ta yayi ba,saurin ja da baya tayi bakin ta na rawa tace"keh malama mai kike yi a nan".

Wani irin shu'umin murmushi Hauwa tayi tace"ke ya kamata na yiwa wannan tanbayar,mai kike yi a gidana?".

Dariyar rainin hankali Lubna tayi tace"ohhh! kice fah ke ce matar gidan wacce ba ta da maraba da babu",ta karasa maganar ta tare da fashewa da dariya har da tafa hannu.

Sossai kalaman ta na karshe ya daki zuciyar ta wanda ya haddasa mata daukewar jin ta da ganin ta na tsawon dakika biyu.

Wani irin ciwon kai ne ya riske ta far daya,ji tayi gaba daya duniyar na juya mata,murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi ta mike tana tafiya tana murmushi kanta a kasa har ta karaso inda take ta fara zagaye ta tana kare mata kallo tace"Amarya kin sha kamshi,Amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida",ta karasa maganar ta tare da jan kujera ta zauna ta daura kafa daya kan daya tana kallon ta tace"gaskiya kwakwalwar kifin ki bai auno miki dai-dai ba,ki dube ni ki dubi kanki ki bawa kanki amsa da kanki",ta fada tare da mikewa tsaye tana murmushi tana ja da baya har ta bacewa ganin ta.

A fili ta furta na shiga uku,na aunowa kaina abinda bazan iya dauka ba,ashe dama haka matar tashi take?,wace india,wani irin dariyar shakiyanci tayi tace"kyanki na banza,kyawunki ba zai cece ki ba dan mijin naki a tafin hannu na yake sai yanda nayi da shi".

Ta karasa tana dariya mai sauti wanda har Hauwa dake daki na jiyo ta.

Girgiza kai tayi ta daga hannun ta sama tace"ya Rabbi ka taimake ni ka kare ni daga sharrin wannan matar,dan ga dukkan alamu ba ta da kyau".

Ba ita ta fito daga dakin ta ba sai sha daya,ko da ta fito babu kowa a parlor, kitchen ta nufa kai tsaye,tana cikin girki ta tsinkayi muryar Lubna tana fadin"yauwa uwar gida girki ake mana ne?,a hada girkin da ni dan kin san ni amarya ce bazan iya shiga kitchen ba sabida ban gama warkewa daga radadin daran farko ba,kuma kinga har yanzu ban gama cin amarci na ba".

Rintse idanuwan ta Hauwa tayi zuciyar ta na suya,ji take kamar ta wulla mata wukar dake hannun ta.

Danne zuciyar ta tayi ba tare data tanka mata ba ta cigaba da aikin da take.

Dan murmushi Lubna tayi ganin maganar da ta yi ya bata mata rai.

Kara karkace baki tayi wurin fadin,baki ji ba,mijin nan namu ya iya soyayyah,hmmm! ke dai bari abun ba'a magana,idan nace.............

Watsa mata ruwan barkonon dake cikin roba tayi tana huci ,idan ta yayi jajazir kamar an kwaba yaji da manja.

Dai-dai nan Sani ya shigo,da sauri ya karasa gun Lubna ya dago ta yana fadin"menene?,mai ya faru?,mai ta miki?"

Kasa amsa ko da daya daga cikin tanbayar tayi sabida tsananin azabar dake nukurkusar ta.

A fusace Sani ya mike ya nufe ta gadan-gadan yana huci,bai yi wata-wata ba ya dauke ta da mari,yana  sauke hannun shi ya ji saukar nasa marin.

Dafe kuncin shi yayi yana kallan ta da dinbin mamaki,a hankali ya budi baki yace"ni kika mara?",shiru Hauwa tayi ta kasa magana illa hawayen dake ambaliya a fuskar ta,Allah ma ya sani ba da gangan ta mare shi ba,tsabar bakin ciki ne da takaici ya kaita ga aikata haka.

Murya na rawa tace"kayi hakuri",ta fada tare da wucewa daki idan ta na zubar da hawaye,girkin da bata karasa ba kenan.

Kasa kwakwaran motsi yayi,chan kuma yayi kwafa ya daga matar shi suka wuce daki.

Tana shiga daki ta fada kan gado ta ringa risgan kuka,da haka barci ya dauke ta,ba ita ta farka ba sai biyu da minti sha biyar,da sauri ta mike bakin ta dauke da Addu'a,bayi ta nufa tayi brush sannan ta wanke fuskar ta ta fito,a gurguje ta chanja kayan dake jikin ta ta zura hijabi ta fice daga gidan...................................

Ku yi hakuri da wannan.

Comment
Vote
Share

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now