PAGE 15-16

81 13 1
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 15&16

________________________Zaune Mami take a gefen gado ta jingina kanta da jikin gado idan ta a kulle.

"Sallama Hauwa tayi".

Ba tare da Mami ta bude ido ba ta bata izinin shiga.

Zama tayi kusa da Mami murya a sanyaye tace"Maminaaa?".

Bude ido Mami tayi a hankali ta kalle ta sabida yanda taji ta kira sunan ta tace"Ya akayi daughter,ina fatan ranki bai baci da abinda wannan yaran yayi miki ba".

Murmushi sossai Hauwa tayi tace"gaskiya Mami naji ba dadi ne kawai da naga ranki ya baci,bancin haka ni kam babu abinda ya bata min rai".

"Kiyi hakuri Mami,kinsan halin kayan ki,Addu'a kawai zaki mai tare da lallaba shi,abinka da Auta,ta fada tana murmushi".

Gode-Gode da shi zan lallaba shi,mutun da Matar shi,"tabdi" iko da yayi asara.

Murmushi Hauwa tayi a boye tace"ba shakkah alamu sun nuna".

Dariya sossai Hauwa tayi tace"Mami i ko yara gare shi zaki lallaba shi dan har gobe yaro yake a gunki".

"Mami kiyi hakuri ki daina fushi da shi,kinji pls Mamina",ta fada tana rike kunnuwan ta da hannu biyu.

Murmushi Mami tayi tace"toh shikenan na hakura".

"Toh Mamina nagode,muje parlor ki tarbi bakin ki".

Tashi Mami tayi zuciyar ta fari kal"har zuciyar ta take son yarinyar,badan jini jini bane da hmmm"................

Ko da suka sauko down stairs basu iske kowa ba.

Kujeran dining Hauwa ta jawa Mami ta zauna tana murmushi zuciyar ta fari kal,"tana san yanda yarinyar ke lallaba ta,take kuma kula da ita,ko da wasa bata son ta ganta cikin damuwa".

Muryar Hauwa ne ya katse mata tunanin da take,"Mami naje na kira su ne?".

Eh toh,i yanzu yaci ace sun gama kimstawa dai koh?,ki dubo su dai,in sun gama su fito,in kuma basu gama ba sai kiyi dawowar ki,dama daga shi har matar tashi duk kanwar ja ce,halin su daya,suyi ta yin abu kaman marasa jini a jiki,Allah dai ya kyauta.

"Da badan an nuna min yaran nan san dana haife shi a Asibiti ba da nace chanja min shi aka yi wlh,kaman ba namiji ba,komi na shi da sanyi yake yin shi,ni da nake mace na fishi kuzari da kazar-kazar".

"Wlh ko lagwani Albarka,Allah kuwa".

tun tana iya rike dariyar ta har ta kasa ta saki abin ta,a haka ta hau stairs tana cin dariya.

"Ji kake gummm"...........

"Baya Hauwa tayi da sauri ta dafa goshin ta".

"Keh!,ke wace irin mahaukaciya ce,baki gani ne,kina shaye-shaye ne,ohhh! ko da yake daga local area kika fito,banga fault dinki ba,Nonsense kawai",ya karasa maganar shi yana jan wani dogon tsaki yabi ta gefen ta ya wuce.

"Tun da ya fara magana jinta da koman ta ya dauke,zuciyar ta kuwa sai tafarfasa take,tunda take duniya,tunda uwarta ta haife ta babu mahlukin daya taba mata irin wannan zagin,share hawayen daya gangaro mata tayi ta juya ta nufi dakin ta.

Shiru-shiru Mami na jiran saukowar Hauwa amman taji shiru,gashi dai wanda aka sa ta kira sun sauko ita kuma shiru.

Kallan Jalal Mami tayi tace"kai ina Hauwa".

"Maiimaita sunan yayi a zuciyar shi".

"Ba da kai nake magana ba".

Dago kanshi yayi ya kalli Mami da shanyayyun idanun shi yace"Mami who is that,mai ma kika kira sunan,don't want to know self".

Sakin baki Mami tayi tana kallan shi kafin a harzuke tace" kaci gidan ku Jalal,nace kaci gidan ku,toh uwar ka ce mai sunan,kana jina kohhhh!".

"Dago kai yayi yana kallan Mami jin yanda take magana a zafafe".

"Wai Mami mai yasa kike min haka ne,na kula yarinyar nan ta miki tsafi,duk tasa kin manta dani,kin kwashe duka son da kike min kin maida kanta,yarinyar daba jinin mu ba,kika sani ko trap aka hada da ita,kawai ta miki dadin baki kin amince da ita".ya karasa maganar shi ran shi a bace.

"Ni kake dagawa murya Abduljalal,hmmmm! Yanzu naga illar kai yaro waje karatu,toh ka sani Jalal in dai da wannan halin zaka cigaba toh wlh sai na fifita kuluwa a kanka,kaji na rantse".

Kuma yanzu ka mike kaje ka kira min ita,wlh ko kallan banza ka mata sai ranka yayi mugun baci,kaji na gaya maka.
Zaka tashi ko kuwa.

"Mikewa yayi ya nufi upstairs fuuuu! Kaman zai tashi sama".

"Oho dai,kafi iska gudu,dakin dake kusa da nawa",ta fada dadan karfi..........................................



Kuyi hakuri da wannan

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now