🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION 📚
BOOK 1:CHAPTER 109-110
_____________________________A fusace ya bar gidan yana mazurai.
Tsaki taja tace"Allah raka taki gona,banza kawai,wanda bai san halaci ba,mtswwwwwwww!,wlh ko kafa ta ba za'a gani a gurin bikin ba,inaga ranar ma barin garin zan yi dan kar na hadiyi zuciya na mutu",haka tai ta bala'i Ammi na sauraron ta amman bata ce komi ba.
Biki saura sati biyu amman har lokacin Sani bai sanar da Hauwa ba.
Zaune Maman Fauzan take a salon din dake saman layin su ana mata gyaran gashi wasu mata biyu suka shigo suka zauna,nan taji sun fara zanchan auren da Sani zai yi,tun bata gane wanda ake magana a kai ba har ta gane sakamakon kwatanchan matar shi da akewa dayar matar,nan Maman Fauzan ta gane da Hauwa suke amman tsabar mamaki da alajabi yasa ta kasa yarda,ana kammalawa ta sallami matar ta fice daga shagon ba tare data bari sun ga fuskar ta ba jikin ta a sanyaye.
Bata zarce ko ina ba sai gidan Hauwa,ko sallama bata iyayi ba ta shiga parlor ta zube a kan kujera tana sauke ajiyar zuciya,wani irin suya zuciyar ta yake,ji take kamar ita za'a yiwa kishiyar.
Dauriye hannun ta Hauwa tayi da sauri ta bi bayan ta tana fadin lafiya Maman Fauzan,meh ke damun ki.
Dagowa Maman Fauzan tayi idan ta yayi ja tana kare mata kallo.
Bin jikin ta da kallo Hauwa tayi tana mamakin abinda take kallo,murya a sanyaye tace"mai ya faru Anty?".
Dauke kai tayi ba tare da ta ce komai ba,a hankali tace"ga dukkan alamu bata san da zanchan ba".
"Mai kika ce Antyyyy!".
Da sauri ta mike zaune tana share hawayen dake zuba daga idan ta tace"babu komi".
Kallan tuguma take binta da shi tace"ban gane babu komi ba,mai ya Sami Fauzan ko Nurhan ko baban su ne,waye ba lafiya".
Ajiyar zuciya ta sauke tace"babu ko daya".
Dukar da kai Maman Fauzan tayi tace"naimi wuri ki zauna kar maganar yasa ki fadi kasa ba shiri".
Wuri ta naima ta zauna jiki a sanyaye tace"meh nayi Antyyyy!?,wani abu ne ya faru?,ki gaya min dan Allah gabana faduwa yake".
Ajiyar zuciya ta sauke ta sharce hawayen dake idan ta ta rike hannayen ta tace"ina san ki kwantar da hankalin ki Hauwa'u,kisawa ranki salama,ki dauka komai mukaddari ne".
Shiru Hauwa tayi ta kasa magana sai hawaye sharrrrr!.
Dan jimm! tayi ta rasa yanda zata bullowa al'amarin,daga karshe tayi karfin halin fadin"kin yi wata magana da mai gidan ki ne?".
Shiru Hauwa tayi tsawon minti daya kafin ta girgiza mata kai alamun a'a.
"Toh shikenan bari na tafi",ta fada tare da kokarin barin parlor tana sharce hawayen idan ta wani na koran wani.
Da sauri Hauwa ta mike ta rike mata hannu tace"dan Allah ki gaya min,na tabbata akwai abinda kike boye min,ki sanar da ni dan Allah ko hankali na zai kwanta,tashin hankalin da nake ciki a yanzu ya fi wanda kike kokarin gaya min na tabbata".
Murmushi Maman Fauzan tayi tace"hmmmm! Allah yasa hakan ya baki ikon danne zuciyar ki Ameeeen",zan gaya miki amman ina tsoron halin da zaki shiga,naso na boye miki lamarin amman naga baze yiwu ba sabida abinda kake da labarin shi tun farko ya fi ace sai aski ya kai gaban goshi za ka sani,dalilin da yasa zan gaya miki shine ta iya yiwuwa ba zai fada miki ba sai dai ki gani wanda a lokacin sai ya fi bugar da ke.
Hauwa'u mijin ki na shirin kara aure wanda a yanzu haka bai fi sati biyu ba a daura..............................
Salati Maman Fauzan tayi tace"na shiga ukuuuuu!........dan Allah ki tashi karki min hakaaaaaa!"............ta fada tare da fashewa da kuka hawaye shabe-shabe a fuskar ta,dai-dai nan Sani ya shigo,da sauri ta nufe shi tace"dan Allah ka taimaka min mu kaita asibitiiiii!".............
Ba tare da ya kalli bangaran da take ba ya ja tsaki ya shige daki abin shi.
Bin shi da kallo tayi fuskar ta dauke da tsantsar mamaki,sossai abinda yayi ya masifar bata mata rai,amman ba komai zai ga sakayyah,waya ta lalaba da sauri ta kira mijin ta,bugu biyu ya daga,cikin sauri ta mai bayani yace"su fito yana kofar gida dama fita zai yi",daga ta tayi ta saka ta a bayan ta kafar ta na jan kasa har suka fita daga gidan.
A hanyar su na tafiya mijin ta yace"ina mijin nata yake?".
Kawar da kai tayi tana kallan waje tace"baya gida",ta fada tare da dauke kai".
Shiru yayi ba tare daya furta komai ba.
Suna isa Asibiti aka nufi emergency ward da ita,nan aka fara bata taimakon gaggawa.
Ba ita ta farka ba sai washe gari da misalin karfe sha biyu na rana,da kuka ta farka hawaye shabe-shabe,da kyar Maman Fauzan ta samu tayi shiru.
Kwanan su biyu a Asibiti aka sallame su.
Zaune take a parlor bayan sun dawo daga Asibiti hannun ta rike da kwanon fruit salad da Maman Fauzan ta kawo mata tana sha tana hawaye.
Turo kofar Sani yayi ya shigo ba tare da sallama ba,ko bangaran da yake bata kallaba balle yayi tunanin ta san da halittar mutun a wurin,haka zalika shima baice mata ci kanki ba ya shige daki,sossai abin nan da yayi ya masifar bata mata rai, dauke hawayen dake idan ta tayi tana girgiza kai.
Hadiye kukan dake kokarin kufce mata tayi tana toshe bakin ta da Apple din dake hannun ta
Biki ya rage saura Kwana biyar kuma har lokacin Sani baida niyyar sanar da ita,hakan yasa ta share shi ta fita batun shi gaba daya.
Ko da wasa bata sanar da Mama abinda ke faruwa ba,duk da Mama ta gane akwai masala amman bata zurfafa ba jin ta ce babu komi yasa ta bar shi a hakan ba dan taso ba.
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,bayan sallar juma'a aka daura Auren Sani Bashir da Lubna Hamza a bisa sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba.
Lubna na jin an daura aure ta zuba ruwa a kasa ta sha tsabar farin ciki.
Kamar yanda Kanwar Sani ta fada hakan ta kasance domin ko da aka daura auren ba su gari,hakan ba karamin dadi ya mata ba,sai dai tana mugun tausayawa Anty Hauwa kuma tana fatan inta koma za ta kai mata ziyara....................................
COMMENT
VOTE
SHAREBY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
![](https://img.wattpad.com/cover/316204785-288-k292975.jpg)
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficción histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...