🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
BOOK 1: CHAPTER 61&62
__________________________A ranan da mugun zazzabi Jalal ya kwana,sossai Mami ta wahala da shi dan kwana yayi yana rafka amai,ta mai tanbayar duniya amman amsar daya ce babu komai Mami zazzabi ne kawai Mami.
Shiru Mami tayi ta buga uban tagumi idan ta ya taru da hawaye tace"Jalal dan Allah ka gaya min damuwar ka,na san ba zazzabi ke damun ka ba damuwa ce,Jalal mai ke damun ka,matar ka ce tayi maka wani abu?,an maka wani abu a wurin aiki ne?,haka tayi ta tanbayar shi amman shiru dan bai ma san tana yi ba,tuni ya luluka diniyar tunanin "kaunar shi" da son ta ke masifar azabtar da shi.
Bige kafadar shi Mami tayi tace"Jalal tunanin meh kake haka Ina ta maka magana kamin shiru",ta karasa maganar ta idan ta taf da ruwan hawaye.
Lallausar murmushi Jalal yayi ya kamo hannun Mami yana murzawa yace"ki taya ni da Addu'a Mami"ya fada Idan shi na tsiyayar da ruwan hawaye.
Sakin baki Mami tayi tana kallan shi da alamun mamaki ganin hawaye na zuba daga idan shi,ba karamin abu ke sa Jalal kuka ba,tun da taga ya zubar da hawaye toh tabbas abun ya girmama.
Tausasa murya Mami tayi tana shafa fuskad Jalal tace"bbyna,mai ke damun ka,ka gaya min damuwar ka pls,ka san kai kadai gare ni bana so na rasa ka pls,ka gaya min damuwar ka na dau alkawarin shige maka gaba matukar bai fi karfi na ba,pls boy tell me your problem kajiiiiii",ta karasa maganar ta idan ta na zubar da hawaye.
Hannun Jalal yasa ya share hawayen shi yace"Mami na kar ki sa wa ranki damuwa pls kinji,zazzabi ne kawai ke damuna kuma insha Allahu zan warke Mami na kinji ki bar kuka".
Girgiza kai kawai Mami tayi ba dan ta yarda ba.
Bai jima ba barci ya dauke shi,
Rufe shi tayi da bargo ta dan kara karfin Ac ta dawo ta zauna ta buga uban tagumi.
Duk abin nan da ake Jameela bata ma sani ba tana kwance a daki tana sharara barci abun ta.
Wasa-wasa an kasa samun jituwa tsakanin Jalal da Hauwa,sam Hauwa ta ki ba shi fuska,sossai ko abin ke damun Jalal dan har wani dan rama yayi.
Kullun sai Mami ta tanbaye shi damuwar shi amman amsar daya ce babu komi Mami.
*****BAYAN WAYA UKU*****
Abubuwa da dama sun faru a cikin wata ukun nan,ciki ko harda barin da Jamela tayi,a ranar ko ta ci kuka dan kwana tayi tana kuka da surutai.
Jalal ko ko a jikin shi dan damuwar dake kan shi ma ya ishe shi.
Mami ko tayi lallashi har ta gaji ta kyale ta.
A cikin wata ukun nan aka kawo lefen Hauwa set daya mai akwati shida,akwatin yayi kyau masha Allah,ya zuba kaya masu kyau da tsada dai-dai karfin shi.
Mami ta zo ta ga laife ta sa Albarka,daza ta tafi ta ba Mama kyautar kudi naira dubu dari biyar wau ra kara a siyan kayan daki.
Da kyar Mama ta amsa shima sai da Mami ta nuna bacin ranta.
Bayan an kawo laife da sati biyu shagon Sani ya kone kurmus ko tsinke ba'a cire a shagon ba.
A ranar hauka ne kawai Sani bai yi ba,daga karshe dai ya fauwala wa Allah komai.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda saura wata biyu bikin Hauwa.
Ana haka ciwon Baban Sani ya tashi,gashi ba kudi,Sani ya buga ya buga amman bai samu ba,duk inda ya san zai sami kudin sai da ya je amman abin ya gagara.
Bayan sallan isha'i Sani ya je zance,suna cikin hira Hauwa taga yayi shiru,tana ta magana amman shi ba amsa,dan yatsar ta tasa ta dungure mishi kai.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke ya jingina da jikin ginin gidan ya lumshe ido.
Kallan shi tayi tace"Habibi mai ke damun ka,mai ya faru,ya na ganka haka".
Ajiyar zuciya ya sauke yace"babu komi ki bari kawai".
Hade rai Hauwa tayi tace"ya zaka ce min babu komai bayan ga damuwa ina gani tattare da kai,dama damuwar ka ba damuwa ta bace,dama baka dauke ni da mahimmanci ba,dama"................
Daura yatsar shi yayi a bakin ta yace"shiiiiiiiiiii! yi shiru dan Allah kiyi hakuri ba haka bane,nan ya labarta mata komai".
Tagumi tayi idan ta cike taf da hawaye tace"Allah sarki Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne,kamar nawa ake bukata na komai da komai".
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke yace"kamar dubu saba'in".
Hannu tasa a cikin Aljihun dogon rigar dake jikin ta ta ciro wayar ta ta amsa account number shi ta mai transfer dubu dari nan take,tana gama transfer nan take alert ya shigo wayat shi,duba wayar yayi ya ga kudi kimanin dubu dari,kallan wayar yayi ya kalle ta,yayi haka ya fi sau uku,sam yaki yarda da abin da idan shi ya gane mishi.
Sharce hawayen dake idan ta tayi tace"gasu kayi managing din su,Allah ya kara mai lafiya yasa kaffara ne Ameeeeen",yanzu ka tafi kayi duk wani abin da ake bukata.
Dukawa Sani zai yi ya saka gwiwowin shi a kasa Hauwa tayi saurin taran shi tace"babu godiya a tsakanin mu,shima Baba ne a gare ni,kayi maza kaje kayi duk wani abu da ake bukata",sai mun yi waya,ta fada tana daga mishi hannu ta shige ciki.
Sani ya shafe minti 10 a tsaye kafin ya iya daga kafar shi ya bar wurin.
Satin Baban Sani uku a Asibiti Allah ya dauki ran shi.
Sossai Sani yayi kuka kaman wani karamin yaro.
Bayan an gama sadakan bakwai kowa ya watse ya rage daga sani sai mahaifiyar shi da kanwar shi.
*****WASA FARIN GIRKI*****
Masu karatu mu hadu da ku a next page dan ganin yanda za'a kaya
COMMENT
VOTE
SHARE
BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
أدب تاريخي"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...