🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1:CHAPTER 85-86
__________________________A kwana a tashi ba wiya.
Kwance take akan gado sai juyi take tana salati kasa-kasa,tun sha biyu ta farka amman ta kasa komawa barci sabida tsananin azaba da bayan ta ke mata,ga wani irin ciwo da marar ta ke mata kamar an sukin ta da mashi mai kaifi.
Runtse idanta ta yi ta dafa marar ta tana salati kasa-kasa,zufa sai keto mata yake ta ko ina,ta yada uban gumi kaman an kunna wuta a karkashin ta.
Ta dau tsawon lokaci a haka kafin ta samu ciwon ya lafa.
Tashi tayi ta dafa bango tana cije lebe,bayan kamar minti biyu ta fara takawa a hankali kamar wata mai koyon tafiya,haka ta daddafa har ta samu ta shiga bayi.
Sai data dan huta kafin ta samu ta tsugunna,tana tsugunnawa ciwo yace dawa Allah ya hada ni,nan wani sabon ciwon da ya fi na dazu ya taso,hannu biyu tasa ta rike drum din dake bayi tana salati,idan ta yayi zuru-zuru kamar mayunwaciya.
Kuka ta fashe da shi ganin ciwon ba na karewa bane.
Da sauri Mama ta farka sakamakon kukan mutun data ji.
Ganin wuta a kunne yasa ta duba bangaran da Hauwa ta kwanta amman bata ganta ba,alamun motsi data ki a bayi ne yasa ta mikewa da sauri ta nufi bayin tana gyara zanin ta tace"wannan wani irin barci ne ya kwashe ni haka,ya Allah ka sassauta mata kasa ta haihu cikin aminci Ameeeen".
Tana tura kofar bayi kukan baby yayi mata sallama.
Da sauri Mama ta shiga cikin bayin ta nufi inda Hauwa ke duke sai nishin azaba take,kunce zanin dake daure a jikinta ta yi ta nannade jinjirin a ciki sannan ta fice da hanzari ta nufi daki ta dauko kayan da aka hada na haihuwa, sabon reza ta dauka ta yanke cibiya ta kara kulle bby ta kai daki.
Maman ta fara gyarawa sannan ta dawo ta yiwa bby wanka ta shirya shi cikin rigar sanyi ta kwantar da shi.
Ruwan zafi ta tsiyaya a cup ta hada mata tea mai kauri ta bata sai data tabbatar ta shanye shi kafin Mama ta amshi kofin.
Tana ajiye kofin yaran ya tsala kuka.
Dariya Mama tayi tace"ka ji shi dama jira kake ta gama Sha kaima ka sha kohhh!".
Murmushi Hauwa tayi tana kallan yaran.
Daukar shi Mama tayi ta daura shi a kan cinyar Mama ta gwada mata yanda zata rike yaran sannan ta sa ta bashi abinci.
Rintse idanta ta yi lokacin da yaran ya kama tsotsa,wani irin zafi taji ya ratsa tun daga kanta har dan yatsar ta na kafa.
Murmushi Mama tayi tace"ki jure kin ji yi hakuri,haka ko wace uwa ta fara".
Fita Mama tayi daga dakin ta nufi dakin Ummi ta taso ta,tuni idan Ummi ya washe jin ta zama uwa.
Da gudun ta ta shiga dakin,tana zuwa bata yi wata-wata ba ta rungume Hauwa tace"wai kinji jiki,sannu kinji,Allah ya raya mana baby ya baki lafiyar shayarwa Ameeen.
Wai-wai-wai amman babyn nan ya hadu,ni na kasa tantance da wa yake kama.............
Toh uwar dumi sarauniyar surutu,bakin ki bai ciwo ne, dare ne dai kibi a hankali kar ki tashi jama'a atoh.
Rike bakin ta tayi da hannu biyu tace"na yi shiru Mama,wlh dadi nake ji kamar an jefa ni a aljanna na makale..................
Washe gari bakwai tayiwa su Mama a Asibiti daki aka shiga da Hauwa,bayan an gama duba ta aka gano ta karu amman karin ba sai anyi dinki ba ruwan zafi ma kawai ya isa.
Bayan an gama duba Hauwa aka duba yaran ta inda aka tabbatar bai da wani abnormalities, immunization room aka nufa da shi aka mishi alluran daya kamata.
Bayan sun kammala komai suka fito daga Asibiti dai-dai nan Sani ya karaso,ba kunya ya nufi matar shi ya rungume ta tare da babyn ya mana mata peck a goshi yace"a gaishe ki Hajiyar mata sannu da aiki Ubangiji Allah yayi miki albarka ya raya mana babyn mu Ameeeen".
Daukar yaran yayi yana kallan shi bakin shi har kunne,nan ya radawa yaran suna.
Tuni su Mama suka bar wurin,sai da ya dan dawo natsuwar shi sannan yace"ina Mama take".
Da sauri Hauwa ta dubi gefen ta amman wayam babu kowa,da mamaki ta fara bin haraban wurin da kallo chan idan ta ya kai kansu,ajiyar zuciya ta sauke tace"gasu chan Abban baby,mai sunan yaran ba'a gaya min ba".
Murmushi Sani yayi yace"za ki sani amman ba yanzu ba".
Girgiza kai kawai ta yi ta nufi inda su Mama suke.
Bayan sun koma gida Mama ta kira Mami ta gaya mata,bata ko kai karshe ba Mami ta kashe wayar,bata fi minti goma ba ta karaso gidan da murnar ta.
Ran suna aka yankawa yaro ragon suna biyu,daya wanda Mami ta kawo daya na Angon karni.
Jameela ta zo mata barka kuma ta kawo mata kayan baby har kala biyar da atanfa uku sannan ta bata kudi ta ce in ji Mijin ta.
Godiya sossai Hauwa tayi mata tare da mata fatan sauka lafiya sannan tace"taiwa mijin ta godiya".
Ranaku na tafiya inda lokacin mu ke karewa.
Kwanci tashi asaran mai rai.
Zaune Jameela take a parlor da misalin karfe goma Sha daya na safe tana kallan Tv hannun ta rike da Apple tana ci ba dan tana jin dadin shi ba,tun data tashi barci take jin babu dadi a jikin ta amman haka tayi ta daddafawa.
Gyara zaman ta tayi ta jingina da kujera,ji tayi kaman an taikare ta,nan kuma bayan ta ya amsa.
Mami dake saukowa tace"ya dai jikin ne?".
Girgiza kai Jameela tayi tana murmushi tace"ba komai Mami",bata ida rufe bakin ta ba taji kaman an tokare cikin ta ta ciki,ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe ido tana cije lebe,tuni ta hada uban gumi sai kace wacce aka saka a cikin oven.
Tun tana iya jurewa har ta kasa ta kira Mami.
Dama Mami ta san abin ne yazo dan har ta gama shirya komai ta kai mota,hijabi kawai tasa mata ta taimaka mata har wurin mota suka shiga driver ya ja suka nufi Asibiti.
Tun kafin su isa Mami kira Dr ta sanar mai.
Ko daidaita parking driver bai yi ba Mami ta balle motar ta fito aka dauki Jameela aka daura ta akan gadon aka nufi cikin Asibitin da ita.
An shafe awa uku ana abu daya amman ya gagara,yanke shawaran cs kawai aka yi sai ga yaro ya turo kai,nan aka fara kokarin taimaka mata,anyi anyi tayi nishi amman ta kasa sabida karfin ta ya kare,karshe dai wata Nurse ce ta haura saman ta ta danna cikin ta aka samu babyn ya fito.
Shirya babyn aka yi sannan aka dawo kan uwar,bayan sun kammala Dr ya fito yana sharce zufa.
Da sauri Mami da Jalal suka nufi Dr,murya na rawa Jalal yace"Dr matata fa".
Dafa kafadar shi likita yayi yace"kayi hakuri mun..................................
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.
![](https://img.wattpad.com/cover/316204785-288-k292975.jpg)
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Historical Fiction"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...