PAGE 105-106

45 11 2
                                    

🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
               (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

BOOK 1: CHAPTER 105-106

__________________________Sannan yace"kizo da abinda na bukata washe gari,shida tai miki a nannnnn!,in kika wuce wannan lokacin kumaaaaa!.......tohhhhhhh!..........ki kuka da kanki,Hmmmm!..........",ya fada yana furzar da iska.

Lubna ta tsorata ba kadan ba,sam bata yarda ta bar kauyen ba sabida kar ta makara gobe.

Washe gari biyar da hamsin yayi mata a bukkar boka,amman bata shiga ba sai da lokaci ya cika.

Mika mishi abinda ya buka ta tayi,nan ya fara aiki.

Bayan minti talatin boka ya sallame ta tare da gindaya mata sharuddai.

************************************

Shiru Hauwa tayi ta naimi wuri ta zauna idan ta na tsiyayar da ruwan hawaye,ta fi tsawon minti goma a haka tana tunanin abinda zata gaya mata wanda zai wanke ta ba tare data gaya mata ainahin zance ba.

Dan murmushi tayi tace"dazun ne na fadi a ties da zan shiga kitchen shi neee"..........

Shiiiiiiiiiiii!,kar ma ki karasa zancan ki dan na san karya kike,Hauwa'u yaushe kika fara karya?".

Shiru Hauwa tayi jikin ta yayi mugun sanyi,tunda take da ita bata taba kiran ta da sunan ta ba sai yau.

Fashewa tayi da kuka harda shasheka tace"nayi kokarin rike sirri na iya ni kadai har zuwa lokacin da Allah zai kawo min mafita,amman girman ki da darajar ki da yardar dana baki yasa zan fada miki gaskiyar zance wanda ko iyaye na ban gayawa ba",ta fada tana share hawayen idan ta.

Dukar da kai Maman Fauzan tayi idan ta cike da hawaye.

Ajiyar zuciya Hauwa tayi tana share hawayen idan ta ta fara bata labari tun daga farko har kan marin ta daya yi,ba abinda ta boye mata.

Ameen ne yasa hannu yana share mata hawayen dake zuba daga idan ta.

Rungume shi tayi ta cigaba da kukan ta.

Maman Fauzan ce tayi kokarin shanye nata kukan ta lallashe ta tare da bata shawarwari.

Sun jima suna tattaunawa kafin Maman Fauzan tayi haramar tafiya,har kofar gida Hauwa ta rakata,da zasu rabu Hauwa tace"Dan Allah ki rike min amana ke kadai na gayawa sabida na yarda da ke".

Murmushi Maman Fauzan tayi tace"ba kida matsala dani sai dai naso ace gida sun san da zanchan,amman tunda haka kike bukata babu komai zan rike miki sirrin ki insha Allah babu wanda zai ji".

"Murmushi Hauwa tayi bayan Maman Fauzan ta tafi,ji tayi kashi saba'in na damuwar da take ciki ya kau,haka kawai take jin farin ciki mara misaltuwa,hakika Maman Fauzan ta zama wata bangare a rayuwar ta,tana jin ta kamar yar uwar ta ta jini".

Bayan sallan isha'i Sani ya shigo gidan ko sallama babu,direct dakin shi ya nufa ba tare daya ce mata ci kanki ba.

Ajiyar zuciya mai karfi Hauwa ta sauke jin ya murza makulli a kofar dakin shi,mugun shakkar shi da tsoron shi take,a hankali ta mike ta rufe kofar gida ta dawo ta rufe kofar parlor ta kashe kayan kallo ta dauki yaron ta suka shige daki ta murza makulli tana Addu'ar kar ya naime ta,dan ba karamin tsorata tayi da ganin fuskar shi ba.

Washe gari bayan tayi sallah ta hada breakfast ta gyara kitchen da parlor taiwa Ameen wanka ta shirya shi cikin kayan islamiya,hijabi ta saka ta rike mai hannu,har ta kai bakin kofa taji ance,"ina za kiiiiiii!?".

A tsorace ta juyo jikin ta na rawa tace"za.....zan kai shi islamiya ne".

Uffan bai ce ba ya karaso ya rike hannun shi suka fice daga gidan.

Bin shi da kallo Hauwa tayi baki bude,ta fara tunanin Aljanu sun shige shi,in ba aikin aljanu baaaa! mutun zai ta yin abu kaman an.................

Tsit tayi sakamakon turo kofar da aka yi tana rarraba idanu,kai tsaye yace"miko min pose dina a kan dressing mirror".

Da sauri ta juya kamar zata kifa ta nufi dakin shi,tana tafiya tana waige har ta isa ta dauko,bayan ta mika mishi cikin sanyin murya tace"an gama breakfast".

Girgiza kai yayi yace"bari naje na dawo".

Bin bayan shi tayi da kallo,a fili tace"ba shakkah Aljanu sun shafi mijina,dole na tsaya tsayin daka wurin yi mishi Addu'a".

Bayan ya dawo yayi breakfast suka yi sallama lami lafiya.

**********************************

Ummi tayi nisa a karatu dan har ta gama aji biyu suna shirin shiga na uku.

A duk sanda su kayi waya sai Mama ta mata zanchan Hauwa'u,tun abin bai damun ta har ya fara damun ta,hakan yasa ta dau alwashin kai mata ziyarar bazata in ta samu sarari.

Zaune Sani yake a shago ya kishingida da jikin kujera,haka kawai yake jin wani abu na mai yawo a kai, hannun biyu yasa ya rike kan yana salati,dai-dai nan Lubna ta shigo ba tare da sallama ba,dagowa Sani yayi dan ganin wanda ya shigo,yana hada ido da ita kan shi yai wani irin  sarawa,rintse ido yayi da mugun karfi yana sauke ajiyar zuciya kaman mai asthma.

Murmushin mugunta Lubna tayi ta ja kujera ta zauna a gaban shi, drink din data shigo da shi ta bude ta tsiyaya mishi a cup ta mika mishi,ba musu ya amsa ya shanye,yana ajiye copin Lubna ta dube shi tace"Habibi,so nake ka turo magabatan ka su naima maka aure na".

Jiki na bari yace"toh shikenan masoyiya,yanzun ma zan kira Baffah yazo muje sai a daura kawai".

Zuru Lubna tayi da ido tace"ba yanzu za'a daura ba sai nan da wata daya".

Shiru yayi chan kuma yace"yayi nisa,ni naso ace yau aka daura".

Dariya Lubna tayi tace"kace haka kake bukata ta Habibi?".

Girgiza kai yayi yana ta murmushi.

Hira suka dinga yi har yamma,sallah kawai ke daga shi,ko abinci bai fita ya siyo ba dan tazo da nata special girki.

Da yamma bayan ya tashi aiki ya nufi gida,bayan ya gaishe da Ammi yace"Mama Aure zan kara".

Faduwa kwanon dake hannun ta yayi ba tare data shirya ba,murya na rawa Ammi tace"ban ji mai kace ba,anya lafiyar ka kalau kuwa?,kasan abinda kake fada kuwa?,kana cikin hayyacin ka?".

Girgiza kai yayi yace"lafiya ta lau,ni Aure kawai nake so nayi,idan ban aure ta ba wallahi zan iya mutuwa".

Salati Ammi tayi ta kai zaune tana sallallami.

Tausayin Hauwa ce ya tsarga mata a zuciya,ta tabbata ba lafiya ba,amman babu komai Allah baya barci,koma mainene Allah zai warware shi insha Allah.

Lallaba shi Ammi tayi ya bar gidan sabida birkice mata daya yi,a ranar kasa barci Ammin tayi tsabar firgici da zullumin.........................................

COMMENT
VOTE
SHARE

BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now