🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
Ina godiya sossai da comment dinku,ina muku fatan alkhari.
BOOK 1:CHAPTER 43&44
_________________________Haka Jameela tayi ta tunani,wani tayi ta ja tsaki wani kuma ta zuburo baki,wani kuma tayi tace"Allah ya isa Allah ya kiyaye",daga karshe dai kuka ta fashe da shi ta fada kan gado,a haka barci ya dauke ta.
Zaune Jalal yake a Office abun duniya ya ishe shi,hannu biyu yasa ya tallafa kuncin shi da shi,aiki yake son yi amman ya kasa,daya fara zai ajiye,wayar shi ya ciro ya dan yi latse-latse.
Gyara zama yayi ya tasa wayar a gaba yana kallo,shi bai danna wayar ba kuma bai ajiye ba illa idan daya zuba mai.
"Matsowa nayi dan naga mai yake kallo,ina lekawa na zaro ido waje,wazan gani........Hauwa ce a jikin wayar da alama bata masan ya dauka ba".
Murmushi Jalal yayi a fili ya furta"sanyin idanuwa na,farin ciki naaaa!".
Haka Jalal yayi wasting wannan ranar ya kasa yin komi,daga karshe dai gida ya nufa dan zaman Office din ya gagare shi.
Biyu da minti talatin Jalal ya shigo gida bai iske kowa a parlor ba sai Tv da aka bari yana aiki,karasawa yayi ya kashe shi.
Tsayawa yayi ya kalli hanyar kitchen ko zai ji mostin ta amman shiru,har tsawon minti biyu.
Dakin su ya shiga ya iske Jameela kwance a kan gado tayi ruf da ciki tana barci ko takalmin kafar ta bata cire ba,tabe baki yayi yace"inda tafi auki kenan barci,dan gajeran tsaki yaja ya kulle kofar".
Ajiye jakar laptop din shi yayi a bed side drawer,dressing mirror ya nufa ya cire agogon hannun shi da zoben dake yatsar shi,hannu yasa ya ciro wayar shi daga aljihu ya ajiye.
Cire kayan dake jikin shi yayi ya saka a hanga ya saura daga shi sai singlet da boxers,toilet ya shiga yayi wanka bayan kaman minti shida ya fito daure da towel a kwankwason shi hannun shi rike da karamin towel yana share kan shi da shi,bayan ya gama ya dau hand dryer ya busar,cream ya shafa ya feshe jikin shi da tulare,drawer ya nufa ya dau wani farin riga mai gajeren hannu da wani farin three quarter ya wuce gwiwar shi da kadan,shiryawa yayi bayan ya saka singlet da boxers,feshe jikin shi ya kara yi da tulare ya dau wayar shi ya fice daga dakin.
Dakin Mami ya nufa yana tafiyar kasaita kan shi a kasa.
Sallama yayi a bakin kofar dakin Mami amman shiru ba'a amsa ba,jin shirun yayi yawa yasa shi yin sallama ya shiga.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke ya karasa cikin dakin,ganin babu Mami a dakin yasa shi zama gefen kujeran bed side drawer,tagumi yayi ya zuba mata ido tun daga kanta da hular ta ya fita ribon din data daure gashin ta da shi shima yayi gefe gashin kanta ya barbaje akan gado.
Yatsar hannun shi yasa ya gyara mata gashin dake kokarin rufe mata fuska,zubawa fuskar ta ido yayi yana kallon ta,kamar an tsikare shi ya dau wayar shi ya fara daukar ta hoto har da video,jin alamun bude kofa yasa shi barin abinda yake ya matsa daga wurin gadon ya rike wayar kaman wani mai yin abin kirki.
Mami ce ta fito daga bayi daure da towel,tana shiga daki idan ta ya kaiga bed side inda Jalal ke zaune.
Kallan shi tayi da alamun mamaki tace"kai kuma mai ya dawo da kai yau da wuri".
Shagwabe fuska yayi yace"Mami kai na ke ciwo shi yasa na dawo".
Kallan shi Mami tayi da alamun tausayi tace"ayyyah Son dina sannu kaji,ka sha magani,ta fafa da alamun tausayi".
Girgiza mata kai yayi yace"a'a Mami na ban sha ba".
Drawer dake wurin dressing mirror Mami ta bude ta dau paracetamol kafin ta nufi fridge ta dauko ruwa ta kawo mai,mika mishi ruwan tayi ta balle maganin ta bashi.
Amsar maganin Jalal yayi yana tabe baki yace"Mami na warke fahh! ba sai na sha magani ba",ya karasa maganar shi yana shagwabe fuska.
Hada rai Mami tayi tace"wlh ko ka amsa ka sha da kanka ko nayi maka dure".
Turo baki Jalal yayi ya amsa maganin ya bude ruwa ya sha sannan ya saka maganin,yaje hadiye maganin ya shanye ruwa ya bar maganin a baki,da sauri ya dau roban ruwan ya fara kwankwada har sai da ya tabbatar maganin ya wuce, yana gama sha ya dau hanki yana share bakin shi da shi.
Dariya sossai Mami tayi tace"gantalallan yaro kawai,har yanzu dai baka bar halin ba",bari naje na shafa mai duk jiki na ya bushe,kaje ka kwanta ko ciwon zai sauka kafin lokacin sallah.
Mami na zaune kan dressing mirror tana shafa mai ta hango Jalal yana kokarin kwantawa a kan gadon ta,da sauri Mami ta juyo tace"mai zan gani,kai meh haka,baka ga daughter a kwance ba".
Hada rai Jalal yayi yace"toh i Mami a nan ni zan kwanta,ita kuma tana chan kinga akwai space tsakanin mu"
Kallan sama da kasa Mami ta mai tace"gode-gode da kai zaka kwanta gado daya da mace baliga,wait naji akwai space a tsakanin ku,inta mulmulo fah sai kayi yaya?".
Shiru Jalal yayi yana kallan Mami,chan kuma yace"toh Mami zan saka pillows a tsakiya".
"Wlh Jalal ka kiyaye ni,zan maka rashin mutunci,kai ba kada daki ne,ko dai wani salon mugunta ka shiya,yi maza ka wuce dakin ka kar na bata ma rai oyaaaa!". ta fada tana nuna mai hanyar fita.
Sossai ran Jalal ya baci,ya rasa dalilin da yasa Mami ke mai haka,da ada ne da wlh a jikin ta zai rama amman yanzu sam baze iya ba,maimakon yaji haushin ta sai ma wani son ta dake kara linkuwa a cikin zuciyar shi.
Juyawa yayi yana kallan ta.Binshi da kallo Mami tayi tace"kai meh haka,bangane maka ba,wlh ko da wasa ka taba min yarinya sai na saba maka".
Murmushi Jalal yayi yana sosa keya ya fice daga dakin.
Binshi da kallo Mami tayi fuskar ta dauke da mamaki...................................
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficción histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...