🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
BOOK 1:CHAPTER 63&64
*****TUSHEN LABARI*****
_______________________Alhaji Sa'id Abdul-Razak haifaffan dan garin Zariya ne kuma dan kasuwa,ya kasance yana siyar da atanfa kuma yana da shagon siyar da mai irin su manja da man gyada,yana da mata biyu da yara takwas.
Ya hadu da matar shi ta farko mai suna Hauwa'u a Kano ya je siyo kaya.
Hauwa'u Abdullahi asalin yar kano ce haihuwar kano kuma girman kano,masifaffiya ce na kin karawa,ta san sirrin masifa ciki da waje.
Bayan wata tara da haduwar su ya biya komai aka daura musu Aure ya dauko matar shi suka dawo Zaria.
Bayan wata tara da Aure Hajiya Hauwa ta haihu santalelen dan ta kyakyawa,ran suna aka sha suna kowa ya watse,yaro yaci suna Mu'az,haka dai rayuwa ya cigaba da tafiya.
Bayan haihuwar ta da wata biyar.
A wata ranar Alhamis Abban Mu'az ya dawo daga kasuwa da tsakar rana da misalin karfe daya da minti arba'in da biyar ya iske gidan a wargaze kamar anyi danbe a gidan,ga yaro a tsakar gida tsirara sai kuka yake kaman wanda yayi kwanaki bai ci abinci ba,dai-dai nan Hajiya Hauwa ta shigo gyale rataye a wiyar ta,turus ta ja ta tsaya a yayin da zuciyar ta ya bada wani kara dumm!.
Juyowa yayi a fusace ya daka mata tsawa,nan ya fara mata fada akan abin da ta yi,iko bata yi wata-wata ba ta mayar mai da martani,ta inda take fita ba ta nan take shiga ba,shiru Abba yayi yana bin ta da kallan mamaki,daga karshe kada kai yayi ya shiga daki ya dau abin da yake so ya fice daga gidan a mugun fusace,tun daga ranar aka fara samun matsala a wannan gidan,ba a sati ba'a samu matsala ba,a haka rayuwar ya cigaba da tafiya.
Bayan shekara biyu da haihuwar Mu'az Hijiya Hauwa wacce ake kira da Inna ta haifi santalelen danta mai kyau,ran suna yaro yaci suna Abdullahi amman ana kiran shi da Lado.
Bayan shekara bakwai cir da Auren su rayuwar taki dadi domin inna ta dagulawa Abba lissafi ta fi karfin shi,idan ta yi abu yayi mata magana sai ta hau shi da fada,ana haka wani abokin shi ya ba shi shawaran kara Aure,iko Abba ya amince,bayan wata daya da maganar Abba ya hadu da wata matashiyar budurwa mai kimanin shekara ashirin da uku a duniya,wasa-wasa soyyaya mai karfi ya kullu a tsakanin su,duk abin nan da ake inna bata sani ba,dan data sani baza ta bari ba,bayan wata hudu aka daura aure amarya ta tare a gidan ta da mijin ta ya kama mata.
A ranar ba karamin tashin hanlali aka yi ba domin har yan unguwar sai da ta jirkita su,Abba ko sai da yayi sati bai leko ba domin yasan bala'in da zai tarar,washe garin ranan ya zo gidan i ko ya tarar da bala'in da yake gudu dan goshin shi a fashe ya bar gidan,iko tun ranan bai koma ba sai dai yayi aike.
Da dai ta ga kwabar ta naso yayi ruwa sai ta sauko ta naimi mijin ta suka shirya amman halin na nan sai dai ta rage.
Sossai kishiyar ta ta sha rashin mutunci da cin kashi kala-kala,amman ko da wasa bata taba fada wa mijin su ba.
A wata ranan juma'a bayan anyi sallah Inna ta zo gidan Amaryar Abba mai suna zaituna.
Zaune zaituna take a kan kujerar tsugunno tana gyara waken daza ta yi alale,kwasam sai taga mutun ya dirgo ba sallama,batayi wata-wata ba ta wanka mata mari tasa kafa zata bige cikin ta.
Abba dake kwace a kan doguwar kujera yana latsa waya ya mike ya fito tun lokacin data shigo gidan,yana ganin abin da take kokarin yi ya afko wurin kaman kiftawar ido da bismillah bai yi wata-wata ba ya dibe ta da mari hagu da daman daya dauke mata jin ta da ganin ta,hannun ta ya kama ya kaita har bakin kofar gidan ya cillar.
Bayan sallan magariba ya zo mata da tsarabar saki ya kwashe yaran shi zai fita,kukan kura ta yi tai wani super ta dira ta rike kafar shi tana kuka da majina tana rokon shi,shiru Abba yayi ya kulle idan shi zuciyar shi na tafarfasa,da dai ya ga baza ta sake shi ba sai yayi fatali da ita ya fice daga gidan ba tare da ya duba in da ta bugu ba..............................
Ku yi hakuri da wannan banda charge,nagode da kaunar da kuke nuna min da novel dina.
By GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Historical Fiction"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...