PAGE 49-50

49 12 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 49&50

___________________________Da sallamar ta ta shiga cikin gida,a tsakar gida ta iske Mama da Asiya suna hira.

Tana zuwa ta fada kan Mama ta rungume ta tace"washhhh! Mamana na gaji".

Murmushi Mama tayi tace"ayyyahh Mamana sannu kinji,tashi ki je kiyi wanka zaki dan ji dama".

Hada mata ruwa Ummi na.

Mikewa Ummi tayi ta nufi wurin murhu ta hada mata ruwan wanka ta kai bayi.

Daki Hauwa ta shiga ta tube ta fito daure da towel iya gwiwa kanta rufe da dankwali ta shige bayi.

Da misalin karfe takwas da ashirin Sani yazo zance gun Hauwa.

Wani yaro ya aika ya kira mashi Hauwa.

Kimtsawa tayi ta dau soson powder tana gyara fuskar ta bayan ta gama ta dau tulare ta fesa.

Tsayawa tayi tana kallan kanta a madubi.

Mama dake zaune a gefen gado tana nade kaya tace"wai kwalliyar bai isa ba,haba kina batawa bayon Allah lokaci".

Murmushi Hauwa tayi tace"toh na tafi Mama".

"Yauwa ki kula,ki rike mutuncin kanki,in kina tunanin ba mai ganin ki toh akwai Allah".

"Insha Allah Mama",ta fada tare da ficewa.

Bayan ta fita ta iske shi jingine da bango ya harde hannayen shi a kirji

Sallama Hauwa ta mai muryar ta a sanyaye.

Juyowa yayi ya amsa sallamar ta fuskan shi dauke da farin cikin ganin ta,dan raban shi da ita sati daya kenan.

Murmushi Hauwa tayi tace"sannu da zuwa ya hanya?".

Murmushin daya bayyanar da fararan hakoran shi yayi yace"Alhmd masha Allah,munje kuma mun dawo lafiya".

"Toh Alhmd haka ake so,ya su Mama da kowa da kowa".

"Lafiyan su lau suna gaida ki".

Daga haka hira ya barke a tsakanin su,suna cikin hira Sani yace"yauwa Queen ina son na turo magabata na domin tsaida magana".

Sossai Hauwa taji gaban ta ya fadi wanda bata san dalilin haka ba,baza ta ce ba ta ji dadin abin da yace ba,ta ji dadi sossai amman a wani bangare na zuciyar ta tana jin kaman ta rasa wani abu wanda ta kasa tantance ko mai ne ne.

Ajiyar zuciya Hauwa ta sauke tace"toh shikenan insha Allah idan na shiga gida zan sanarwa Mama sai ta sanarwa Kawu,duk yanda ake ciki zaka ji insha Allah".

"Toh shikenan Baby na Allah yasa naji alkhairi ga wannan" ya fada tare da mika mata wani laida.

"Ameeeeeeen".

Kin amsan laidan Hauwa tayi tace"ta gode".

Hada rai Sani yayi yace"ban gane kin gode ba,tun muna mu biyu ki amsa ko kuma na kai ciki da kaina".

Shiru Hauwa tayi dan tasan sarai zai iya,hakan yasa ta amshi laidan dake hannun shi tace nagode Allah ya kara budi ya saka da Alkhaini.

"Ameeen".

Bai jima ba ya tafi.

Hauwa na shiga gida ta sanarwa Mama abin da Sani yace sannan ta bata laidan daya ba ta.

Shiru Mama tayi tace"anya bai yi sauri ba kuwa naga kwata-kwata watan ku uku da haduwa",hmmmmmm! shikenan Allah yayi mana zabi mafificin Akhairi.

Toh wannan kuma meh a ciki?.

Hannu Hauwa ta bude alamun ohooo! bata sani ba.

Bude laidan Mama tayi taga waya ne da tulare sai kayan zaki,sai wani dan paper da aka makala akan kwalin wayar.

Bin kayan Mama tayi da kallo,kafin tasa hannu ta cire paper ta fara karanta abinda ke ciki kamar haka

"Assalamu alaikum,ina wuni Mama,ya gida da ayyyuka,Mama na rubuta wannan sakon ne sabida nasan za kice ta miyar min da kaya na,ni kuma na bata shi ne kyauta da zuciya daya kuma a matsayin tsarabar da na kawo mata,dayan laidan dake ciki kuma na antin mu ne da naki,nagode Mama fatana shine ki fahimce ni".

Shiru Mama tayi tana bin paper da kallo ta kasa magana.

Mikewa Hauwa tayi tace"Mama ni kam barci nake ji bari naje na kwanta".

Hararan ta Mama tayi tace"gidan ku,kayan kuma sai ayi yaya da su tunda kin amso,ba na hana ki amsan komai daga hannun shi baaaaa!".

Turo baki Hauwa tayi tace"Mama wlh naki amasa amman yace zai kawo da kan shi idan ban amsa ba,shi yasa kawai na amsa amman insha Allah bazan sake ba".ta fada tare da mikewa tsaye".

Kallan ta Mama tayi tace"ina kuma zaki?".

Zama Hauwa tayi tana sosa kai,mika mata laidan Mama tayi tace"gashi ki duba".

Amsan laidan Hauwa tayi ta fara duba kayan,chan kuma ta ciro kwalin wayar daga laidan da yake,zaro ido tayi tace"whatttttttttt! IPhone".

Kallan ta Mama tayi da sauri dan taga ko lafiya,sabida sossai tayi ihun.

Dariya Hauwa tayi tace"wlh Mama iPhone ce,wow wayar ta hadu wlh,iPhone 8+".

Kwalawa Asiya kira tayi,ba bata lokaci ta antayo,dan ta san kiran nan ba banza ba.

Tana shiga idan ta yayi arba da iPhone,har kusan faduwa tayi garin sauri tazo ta dauki wayar.

Daukan wayar Asiya tayi tana juya shi tace"wai dan Allah da gaske wayar ce? ".

Dariya Hauwa tayi tace"a'a toy ce".

Bude dayan laidan tayi wanda taji Mama ta ce na ita da Asiya ne.

Wani dan laida ta gani ta bude,zaro ido tayi tace"wayaaaaaaa!".

Daga Mama har Ummi kallan ta su kayi,ganin da gaske wayar ne a hannun ta yasa duk su kayi shiru.

Chan kuma Mama tace"ina kika ga wannan kuma".

Nuna mata laidan da aka ce nasu tayi tace"a nan Mama".

Tagumi Mama ta buga tace"aje wayoyin,dole na gan shi gobe".

Ajiyewa Hauwa tayi ta amshi na hannun Ummi ta ajiye.

Tabe fuska Ummi tayi tace"ayyyahhhh Mama kar ki maida kin jiiiiii!".

Wani irin mugun kallo Mama ta aika mata da shi tace"gidan ku,gidan ku nace,maza je ki naimi wuri ki kwanta tun kafin ranki ya baci yan zunnan,uwar azarbabi kawai,Allah dai ya shirye ki ba dan halin ki ba".

Shiru Ummi tayi ta fice daga dakin.

Zaune Hauwa take a parlor tana kallo,bata jima da zama ba Mami ta sauko,sai uwar son miji.

Bayan sun gama break Mami tace"taje ta shirya za su fita yanzu".

Tabe baki Jameela tayi tace"karere kawai an samu gindin zama".

Ko kallan bangaran ta Hauwa bata yi ba balle tayi tunanin samun amsa.

Shiru Mami tayi ta kasa magana sossai abin ya bata mata rai,bata san dalilin da yasa takewa Hauwa haka ba,na daya ba su ma cika haduwa da shi ba,kuma in sun hadun ma da fada ake karewa,na uku ba miji daya suka hada ba balle ta ce tana kishi,ta rasa gane wannan kiyayyar daga ina ya samo asali.

Murmushin yake Hauwa tayi tana kwantarwa Mami hankali.

Goma da rabi dai-dai suka bar gidan direct wani babban shagon saloon suka nufa

Bayan kamar awa daya da rabi aka gama komi............................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now