PAGE 57-58

41 9 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AUSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK1:CHAPTER 57&58

__________________________Kaman yanda Mama tace haka ya kasance.

Da misalin karfe biyu wakilan Sani su kazo inda suka bada komai na na gani ina so sannan aka saka rana nan da wata biyar masu zuwa.

Bayan sallan magarib Hauwa ta dawo Mama ta sanar mata da duk yanda su kayi har kudin da aka kawo da ranar da aka saka.

Hauwa na gama jin abinda Mami ta fada taji zuciyar ta yayi wani irin bugun da har sai da ta dafe kirjin ta ta naimi wuri ta zauna.

Dafa ta Mama tayi tace mai ya faru,mai ke damun ki,ulcer ki ne ya tashi.

Dagawa Mama kai tayi tace"ehhh! Mama".

Kwalawa Ummi kira Mama tayi tace"ta dauko mata maganin Kuluwa a daki".

Ba jimawa Ummi ta dauko maganin ta kawo hadi da ruwa.

Balla maganin Mama tayi ta bawa Kuluwa sannan ta bata ruwa ta sha.

Bayan ta gama sha ta kwantar da ita ta lullube ta,da yake tasan bata sallah hakan yasa bata takura mata ba.

Wani irin zazzabi ne ya kama Hauwa a daran wanda hakan ya hana ta zuwa aiki washe gari.

Sossai hankalin Jalal ya tashi washe gari da baiga jiddan shi ba,ya fi awa uku a zaune yana jiran zuwar ta amman bata zo ba,ya kalli wayar shi ya fi a kirga,yayi kokarin kiran ta sai ya tuna baida number ta.

Daya tabbatar baza ta zo ba sai ya tashi ya koma parlor,yana shiga ya ga dayar mai aikin na girki,hakan ya tabbatar mishi da baza tazo ba,kuma ga dukkan alamu Mami tasan baza tazo ba.

Sai Hauwa tayi kwana biyu kafin ta dawo aiki.

Sossai Jalal ya ji jiki a yan kwanakin nan,har wani dan rama yayi wanda yasa har Mami ta so ta harbo jirgin shi.

Tunda Hauwa ta dawo aiki ta daina kula Jalal,gaisuwa kawai ke hada su,daya amsa gaisuwan ta zai jata da hira sai ya ga ta wuce shi,hakan ko ba karamin taba mishi zuciya yake ba.

Shi da yake tunanin cikin satin nan zai bayyana mata abinda ke zuciyar shi sai kuma ya ga ta sauya mishi,toh mai ya same ta,mai ke damun ta,mai aka mata,ko dai an bata mata rai ne daga gida,haka dai yayi ta zancen zuci...........

Hauwa na gama break ta daura da girkin bakuwar Mami,bayan ta kammala ta gyara ko ina ta wuce dakin da yake mallakin nata ta watsa ruwa ta sauya kaya.

Bayan ta gama shiri ta nufi dakin Mami ta sanar mata.

Godiya sossai Mami tayi mata tare da yi mata sannu da aiki.

Mikewa tayi za ta fita taji Mami tace"zo nan ina za ki".

Juyowa tayi ta kalli Mami fuskar ta ba yabo ba fallasa tace"babu komi Mami kawai dai kai na ke dan min ciwo".

Mikewa Mami tayi da sauri ta tare ta tace"ayyyah daughter na sannu kin ji,kin sha magani?"

Girgiza kai Hauwa tayi tace"a'a Mami".

Zaunar da ita Mami tayi a gefen gado ta bude drawer dressing mirror ta dau paracetamol da goran ruwa,maganin ta balla ta bata sannan ta bata ruwa,bayan ta gama sha Mami ta kwantar da ita ta lullube ta da bargo tace kiyi barci kinji daughter Allah ya kara sauki,ta fada tana shafa gashin ta da ta cire mata dankwalin wai yana kara mata ciwon kai.

Bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita.

Da misalin daya da minti ashirin ta farka bakin ta dauke da Addu'an tashi daga barci"yana da matukar mahimmanci,dan Allah yan uwa musulmai ku kula ku rinka karantawa bayan kun tashi daga barci" ga Addu'an kamar haka"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaihin nushur,la'ila ha illalla wahdahu la shari kala lahul mulku wa lahul hamd wa huwa ala kulli shai'in kadir".

Tana duba agogon dakin taga lokacin sallah yayi har ya wuce,i da sauri ta sauka ta shige bayi ta dauro Alwala ta fito,dakin ta ta koma ta saka hijab sannan ta shinfida darduma ta tayar da sallah.

Bayan ta idar tayi Adduo'in da Manzon Allah S. A. W ya koya mana,tana gamawa ta shafa ta mike ta cire hijabin jikin ta ta linke sannan ta linke darduman ta ajiye.

Gaban madubi ta nufa tana kallan kanta,kasan dankwalin ta tasa ta share kwallin daya dan zazzago mata,bayan ta gama ta gyara daurin dankwalin ta ta feshe jikin ta da wani daddadan tulare mai tsanya natsuwa.

Down stairs ta nufa bayan ta gama karewa kanta kallo a madubi,dukawa tayi har kasa ta gaida Mami tare da bakuwar ta.

Murmushi bakuwar tayi tace"fine girl ykk ta fada tare da jan kunatun Hauwa sannan ta zaunar da ita a gefen ta tayi mata side hug".

Murmushi kawai Hauwa tayi tana sunne kai kasa.

"Mamin Abdul ina kika sami fine girl haka,ko dai mata Abdul ya kara ban sani ba kuma ba nida labari",ta karasa maganar ta hannun ta rike da habar ta fuskar ta dauke da mamaki.

Dariya Mami tayi tace"ke dai ba'a raba ki da kayan ban dariya,duk kin bi kin rude daga ganin ta".

"Ummmmm! baza ki gane ba,yarinya ta shiga raina sossai wlh,ya sunan ki fine girl?".

Murmushi Hauwa tayi ta kara sunnar da kanta kasa tana murza yatsar hannun ta tace"Hauwa".

"Ahhhh! kice sunar tsohuwa gare ki,sunar Hajiya ta kenan,Allah ya miki Albarka kinji ya tsare ki a duk inda kike Ameeeen".

Da Ameeen Ameeeen Mami ta amsa haka zalika Hauwa amman ita a ciki ta amsa.

Bayan tafiyar Hauwa matar mai suna Hajiya Ramlat tace"gaki da diya mai kyau ga natsuwa,tarbiya,kunya da sauran su,ke da zakiwa dan ki hanya u
Ya aure ta shine kika tsaya wasa".

Dariya Mami ta fashe da shi har da tafi tace"kai Mummyn Hydar ke kohhh! abin dariyar ki baya karewa,haka kawai zan chusa mishi yarinya azo ayi rashin sa'a baya son ta na shiga uku,kema dai kin san Jalal da bakin hali,in baya san abu baka isa kasa shi san wannan abun ba har sai shi yayi ra'ayi hakan da kan shi,ta ina ma zan fara,mutumin da a haduwar su ta farko aka fara da kiyayyah,yanzu ma naga abin ya danyi sauki dan har hira ma naga yana shiga tsakanin su,amman da ko ga macici basa yi,keh in na gaya miki surutun da nayi a kan Jalal za ki tausaya min wlh". 

Dariya Maman Hydar tayi tace"kai-kai ke da wannan yaran naki kohh!,ni dai abin da na karanta a cikin dan labarin nan da kika bani shine akwai alamun soyayyah a tattare da shi,tsabar jin kan shi da wannan mugun miskilanci ne ya hana shi bayyanawa ko nace ya kasa ganowa,in ba haka ba taya daga haduwar farko sai kiyayyah,i da alamun tanbaya a wannan al'amarin,ke dai bari za kice na gaya miki za ki gani".


Sun sha hira sossai da Mami,sai wuraran biyar ta wuce bayan ta yiwa Hauwa kyautar kudi masu yawa,da kyar Hauwa ta amsa shima sai da Mami ta sa baki.

Tana amsa ta bar wurin.

Dai-dai nan Jalal ya turo kofar parlor bakin shi dauke da sallama,da Hauwa ya fara cin karo da yake ita ke kusa da kofa Mami da Mummy na tsakar parlor a tsaye.

Kura mata ido Jalal yayi murya a tsanyaye yace"mai ke damun ki,y are u behaving like this?".

Juyawa Hauwa tayi ta bar wurin ba tare da ta amsa mai ko da tanbaya daya ba.

Bige kafadar Mami Mummy tayi tace"kinga abin da nake gaya miki kohh!".ta fada tana murmushi.

Zama kawai Mami tayi a kujera ba tare da tace komai ba,sam bata yarda ba sabida yanda taga fuskar Jalal,babu alamun murmushi,fuska a hade kaman an mai albishir da sakon mutuwa.

Zaune Mama take a tsakar gida tana gyara shinkafar two,kofar da taji an banko ne yasa ta mikewa tsaye ta dafa kirjin ta tana salati sakamakon wacce ta gani.................

Mu hadu a next page ..............

Ina kaunar ku fanz❤

Idan kuncinka wacece mu hadu da ku a comment box.................


By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now